Page 16

58 4 2
                                    

Page 16

Isar su shukra dakin ajiyar gawar dukkansu suka shiga tare da tsayawa a gaban gadon da aka ajiye gawar,IG ne ya kafa mata ido tare da cewa
"Fada min wace iriyar hujja kike tunanin zaki iya samu?"
Shiru tayi tana rarraba ido,lieutenant ya kalli IG tare da cewa
"Yallabai yarinyar nan kawai ka kulle ta ,bata da gaskiya". Hannu IG ya daga masa alamar ya dakata da magana,har yanzu idon shi yana kan shukra da ta kasa cewa komai,cikin sanyin murya yace
"Ki yadda dani,zan fahimci duk abinda kike son fada,ki fada min me kika zo nema a nan"
Bayyanannuyar ajiyar zuciya shukra ta sauke ba tare da tace komai ba ta ajiye ta fara kwance kayan da suke hannunta,kwalba guda daya ta dauko ta nuna wa IG tare da cewa
"Yallabai wannan vinegar ce,nayi amfani da ita ne na shafa a hannun gawar nan domin akwai wani reaction da pinellia da vinegar suke bayarwa,yau tsawon kwana uku da mutuwar sa,amma indai ya taɓa pinellia to vinegar nan zata nuna mana" cike da mamaki yake kallonta tare da jinjina kai yace
"Amma ta yaya vinegar zata nuna ko ya taɓa pinellia?"
Cikin qarfin gwiwa shukra ta cigaba da bayani
"Idan aka shafa vinegar a hannun,za'a bashi ɗan mintuna sai a saka farin qyalle a goge,idan ya taɓa pinellia to farin qyallen zai fito da kalar pink,idan kuma bai taɓa ba,ba zai bada wani colour ba" cikin matuqar burgewa IG yake kallon shukra,Jinjina kai sukai gaba dayansu cike da gamsuwa,IG ne yace
"Zamu kawo pinellia sai mu gwada domin tabbatar mana da hujjar da kika zo da ita"
Rusunar da kanta tayi a gabanshi ba tare da tace komai ba,
Hannu ya miqa mata tare da cewa
"Bani vinegar,yanzu zanje na samu mai martaba " kwalba daya shukra ta miqa masa a cikin kwalabe uku,ya kalli lieutenant yace
"Kayi maza ka aika jami'ai a samo pinellia domin akwai amfanin da zamuyi da ita idan na dawo daga wajen mai marataba,rusunar da kanshi yayi a gaban IG tare da cewa
"Yehhh" (yes sir in korean)cikin sautin amsar umarni.

Bayan tafiyar IG da minti 10 shukra tace wa lieutenant
"Yallaɓai ko yaushe IG zai dawo?" Kallonta yayi cike da birgewa yace
"Ai ki koma bureu of music kawai,duk yadda ake ciki bayan ya dawo zamu sanar dake" jinjina kai tayi alamar gamsuwa,ta juya zata tafi ta jiyo muryar shi yana cewa
"Dare yayi ko na sa guards su raka ki?"
Dan rusunar da kanta tayi tace
"A ah ba komai zan iya komawa,ai na saba fita a iron wannan lokacin" ta qarasa tana murmushi,shima murmushin yayi mata tare da cewa
"Toh shikenan sai kin ji mu" qara rusunar da kanta tayi sannan ta juya ta tafi.

Jalila a office of investigation a zaune tayi zurfi cikin tunani amma a nutse take,kamar babu wani abu da yake damunta amma kuma cikin zuciyarta wani tarnaqin baqin ciki ne da tashin hankali na yadda yau ita ce aka wulaqanta aka ciwa mutunci har ladies investigators ma su samu damar fada mata abinda suka ga dama,tunanin ta ne ya katse daidai lokacin da chief sumayya ta shigo,daga idonta tare da binta da kallo har ta zauna tana fuskantar ta,cikin gadara da rashin ladabi chief sumayya tace
"Mai martaba yayi umarnin a miqawa tribunal alhakin binciken laifin da kika aikata" jalila bata ce komai ba,ganin haka ta cigaba
"Ke kuwa me ya kaiki kika aikata irin wannan laifin? A matsayin mu na wanda muke kula da case dinnan muna ganin hakan abin kunya ne" Ran jalila idan yayi dubu ya baci,cikin tsanaki take kallon sumayya,tace
"Ni kike fadawa irin wannan magnaganun? Ehh na yadda abin kunya ne amma a gareku,a sanina office of investigation suna daukar matan da suka fi kaifin basira da ilimi ne,amma yau na fahimci cewa hakan bashi da amfani,ba shi kuma da tabbas,ina tunanin yadda zaku jagiranci inner court nan gaba a rayuwa"
Murmushi sumayya tayi tare da cewa
"Kinyi matuqar birgeni da a cikin wannan yanayin ma kina tunanin me zai faru da inner court,amma a halin yanzu abinda ya kamace ki shine ki kula da halin da zaki shiga ba rashin tabbas din office of investigation ba"
Jinjina kai jalila tayi tare da cewa
"Ba zan manta da kalaman ki ba chief madam inspector" ta qarasa cikin tsuke fuska,chief sumayya ta kalli ladies investiga din da suke tsaye su biyu tace
"Ku kula da ita sosai kafin gobe da safe tribunal su aiko masu rakata can" rusunar da kansu sukayi tare da cewa
"Yehh ma-ma-neem" (yes my lady in korea- zamu dan fara sirkawa da words dinsu domin jin dadin masu karatu) sannan ta fita daga office din ta bar jalila a zaune cikin takaici.

Shukra tana cikin tafiya take jin kamar ana binta,juyawa tayi da sauri taga ba kowa,ta cigaba da tafiya amma har yanzu taji kamar alamar ana binta,juyawa ta qara yi taga ba kowa,ga wajen babu mutane,rungume kwalaben da suke hannunta tayi ta fara gudu,sai ga wanda yake binta shima ya biyo ta gudu,tana shan wata kwana taga wasu sun biyo ta gaban ta,ta juya zata canja hanya amma wasu ma suka tare mata hanya,a tsorace tace
"Me nayi muku? Su waye ku? "
Babu wanda ya kula ta a cikinsu,sai daya daga cikinsu ne da babbar murya yace
"Ku damqe ta mu tafi" jikin shukra ne ya fara rawa,mutum biyu suka zo suka rirrriqe mata hannaye,tana ta qoqarin qwacewa amma dai qarfin ba daya bane,hakan yasa ta fara kuka,kamar daga sama suka ji mutane sun diro da qarfi,kowa hankalinsa ya koma wajen,mai martaba ne ya ɓullo daga kwanar da shukra ta biyo nan da nan guards dinnan suka bawa wanda suka riqe shukra umarni
"Ku sake ta matuqar kuna son ku tsira da rayuwar ku " ogansu ne ya kalli guards din cikin rashin fahimta tare da cewa
"Ba zamu saketa ba,ku din suwaye? Kuyi abinda zakuyi"
Mai martaba ne yayi gyaran murya,cikin kaushin murya yace
"Ku sake ta aka ce ko? " ganin an tsaya taqaddama ogan ya kama shukra ya sa mata wuqa a wuya,cikin dabarun guards din mai martaba suka karbo shukra suka kame 'yan iskan da suka kamata,daddaure musu hannaye suka yi suka gurfanar da su a gaban mai martaba,a dai dai lokacin da hankali tashe yake kallon shukra
"Babu abinda ya same ki ko? Basu yi miki komai ba ko?" Girgiza kai shukra tayi tare da cewa
"Ehh lapiyata qalau,babu abinda sukai min"
Daya daga cikin guarda din sarki ne yace
"ya za'ayi dasu?" Mai martaba ya kallesu yace
"Yan iskan hanya ne,ku kaisu police bureu a hukunta su" tisa qeyarsu akayi shi kuma mai martaba suka tafi tare da shukra.

IG yana isa grand palace chief eunuch ya tabbatar masa mai martaba baya nan,domin ya tafi police bureu domin ya gana da shi,hakan yasa ya juyo domin dawowa police bureu.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now