Page 19

64 6 0
                                    

Page 19

Manager ne da sameer suna zaune suna ta shashanci,wai suna jiran suga wannan karon wane irin tukwuici za'a bawa shukra,sameer ya kalli manager

"Yallabai ina jin wannan karon ma za'a kawo mana abinci na alfarma irin wancan" manager ya kwabe fuska tare da cewa sameer

"Gaskiyarka fa,ni tun yanzu ma ba zan qara cin komai ba,sai kayan alfarma sun iso"

Da sauri sameer ya cafe

"Ai nima dani za'a yi yajin aikin cin abincin,don cikinmu ya shirya karbar kayan dadi" dukkansu suka tuntsure da dariya,shukra suka hango tana shigowa da wani qullin kaya mai girma a hannunta,da gudu suka nufi inda take shigowa sameer yana cewa

"Yauwa shukra kin dawo daga wajen lady jalila,bari muga me aka baki?"

Manager ya dora "Ehh bamu mu gani,silk ne ko keychains din 'ya'yan sarauta?" Tana qoqarin yi musu magana amma basu bata dama ba,saurin karbar kayan suka yi yayinda duk sauran ma'aikatan suka yo cincirindo zuwa wajen domin suga me ta kawo,suna bude qullin suka ci karo da kayan takalman su da ta dauko domin ta wanke,kallon kallo suka fara yi,manager ya kalle ta yace

"Wai bata baki komai ba?"

Kafin ta bashi amsa sameer yace

"Kai dai mu cigaba da yajin aikin cin abincin,kasan dafa irin wannan abincin yana daukan lokaci watakila sai gobe " jinjina kai manager yayi cikin gamsuwa da maganar sameer yace

"Haka ne kam,ke kuma ki ajiye takalman nan kije ki huta don zirga zirgar da kika je jiya" ya qarasa maganar shi yana kallon shukra,murmushi kawai tayi ta kwashi kayan ta bar wajen.



Da daddare,Mai martaba shi da lady jalila a tsaye a wani hawan bene inda mai martaba yake hutawa,duk masarautar babu bene mai tsayin shi,hakan yasa idan ya hau barandar wajen yana iya hango ko'ina na cikin masarautar,shiru sukayi babu me cewa komai suna kallon taurari a sararin samaniya,kowa da tunanin da yake ran shi,yayinda maids dinsu suna can baya baya yanda ba zasu iya jin me suke fada ba sai dai in sun daga murya,mai martaba ne ya katse shirun da cewa

"Lady jalila kina fushi da ni ne?"

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ba tare da ta kalleshi ba tace

"A'ah ko kadan bana fushi da kai,kamar dai yadda na fada maka ne,zuwan da kayi ka ganni ma kawai ya wadatar" ta qarasa har yanzu fuskar ta da murmushi,juyowa yayi ya fuskance ta sosai

"Gaskiya yarinyar nan shukra tayi qoqari,domin duk saboda itane komai ya zo cikin sauqi,hakan abin birgewa ne sosai"

Itama juyowa tayi ta kalleshi

"Gaskiyane your majesty,shiyasa nake ganin zamanta a matsayin slave girl kamar zai zama asarar qwaqwalwarta da basirar ta" shiru ta danyi,shima mai martaba bai ce komai ba ta cigaba

"You majesty ina da wata alfarma da nake son na roqe ka"

"Alfarma wace iri? Game da shukra?" Cewar mai martaba,jinjina kai tayi ba tare da ta ce komai ba,ya cigaba

"Ki fadi duk abinda kike so ayi mata,za'a yi mata my lady" ya fada cike da barkwanci,murmushi hakan ya bata ganin yanayin da yayi maganar.



Shukra a bureu of music ma'aikatan suna cin abincin dare,ita kuma sai kai kawo take tana harhada kayan da sukai amfani dasu,wani cikin ma'aikatan ya kalleta

"Yanzu duk irin qwaqwalwa basirar yarinyar nan,haka zata qare tana kai kawo na share share da goge goge"

Wanda yake maganar dashi ne yace

"Gaskiyar ka fah,domin a qasar mu matuqar dai aka haifeka a matsayin lowborn(talaka) toh baka da wata nasara a rayuwa" haka suka cigaba da tattaunawar su game da shukra.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now