Page 20

63 6 0
                                    

Page 20

Page 20



A office of investigation chief sumayya ce da dukkan ladies investigators da kuka sani a bayanta suka taho a sukwane cikin tashin hankali suka nufo inda director take tsaye bayan ta rako tawagar 'yan office of properties wanda daga wajenta suka wuce bureu of music wajen shukra,sumayya cike da damuwa tace

"My lady ki taimakemu ki janye amincewarki akan wannan lamarin,wannan abu ne da bai taba faruwa ba a cikin qasar nan,tozarcin da zamu ji a ranmu har sai yafi na abinda shukran tayi mana,mutuncin office dinmu zai zube" ta qarasa cike da matsananciyar damuwa,director da ta kasa hada ido da kowannen su,itama fuskarta da damuwa sosai tace

"Bamu da abinda zamu iya yi,domin anyi hakan ne da izini da kuma sa hannun queen haneefah,kuma a matsayinta na shugabar inner court ba zamu taba tsallake unarnin ta ba,amma nima ina tunanin mu gwada zuwa wajen ta din ko za'a dace"

tana gama fadar haka tayi gaba ita da wanda suke binta a baya suka bar wajen.

Chief sumayya,nadeeya,basma,afrah,aliya,da sameerah sukai tsaye duk jikinsu a sanyaye,haqiqa lady jalila ta shammace su akan shukrah don sunsan wannan shine kawai abinda zatayi ta hukunta su cikin ruwan sanyi,chief sumayya ce tayi qwafa ba tare da kowa ya san abinda take tunani a cikin ranta ba tayi gaba sameerah ta bita,yayinda sauran suka tsaya suna jajantawa juna.



A bureu of music dukkan ma'aikatan wajen sun matsu suga saqon menene aka zowa da shukra haka,yayinda itama take tsugunne akan pillow da carpet din da aka shinfida a kasa,tana fuskantar 'yan office of properties,hannu shugabansu ya miqa aka miqo masa takadda da take ajiye akan tray a hannun wata mata da suka zo tare,hannu ya saka ya bude ya fara karantawa kamar haka

Slave shukra Anas Malak zatayi biyayya ga unarnin office of properties.

A yau 11 march na shekarar 1432.

Baiwa shukra zata shiga cikin inner court.

Zata shiga cikin office of investigation a matsayin lady investigator.

Ya zama dole kiyi riqo da biyayya ga dokoki da kuma cika haqqin aikin ki ga wannan qasa tamu da kuma a matsayinki na lady investigator.

You will hear and obey.



Wato tun daga kan manager,sameer,da kuma dukkan ma'aikatan kallon kallo suka shiga,domin ko a tarihi basu taba jin yadda baiwa ta shiga inner court cikin office of investigation ba,abin mamaki ya zama har shukra ta kasa cewa komai sai kawai nuna kanta take tana cewa

"Ni? Ni? Ni din? Lady investigator? Office of investigation? Gaba daya ta rude,ta rasa me zatayi,wanda ya gama karanto mata takardar ne yace

"Slave shukra,hear and obey" da sauri ta nutsu na miqa hannunta biyu biyu ta karbi takardar tare da cewa

"I hear and obey my lord" nan take wajen ya cika da shewa ta ko ina,ma'aikatan bureu of music ba komai ne yake basu mamaki ba illa yadda akayi wannan abu ya faru,sun san ba saboda dalilin abinda tayi ne kadai ba,domin idan ana son bata tukwuici kudi ya kamata a bata da abubuwan alfarma amma tunda aka ɗaga darajar ta lallai akwai sa hannun wani babba( ni dai maryam nace baku san qawar mai martaba bace kenan ko? 😂😂 toh aikin sa ne)

Kafin ki ce me labari ya karaɗe ko ina ai slave girl shukra yanzu ta zama court lady investigator,ana ta taya ta murna a cikin bureu of music kowa da abinda yake faɗa na alkhairi,wasu suce dama bata dace ta zama slave ba,wasu suce yau sunga ikon Allah a tsarin rayuwar su indai aka haifeka a talaka mara galihu to a haka zaka qare rayuwarka sai gashi shukra ta samu ɗaukaka.

A office if investigation director ta kira meeting din kowa da kowa,ta kalli basma da nadeeya tace

"Ku zaku kai takaddar da na rubuta na cewar ba zamu karbi shukra ba zuwa office of properties,ni kuma ni da sumayya zamuje mu samu queen haneefa don its kaɗai take da damar dakatar da faruwar hakan"

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now