Page 28

72 5 0
                                    

Page 28

Jaleel ne tsugunne a gaban tribunal minister,a daya gefen kuma jameel ne da yake jefa wa jaleel harara
"Yanzu wannan makaman da aka kama,idan wajen bincike sunan Abbana ya fito fah?" Ya jefowa jaleel tambayar,wata dariya jaleel yayi yana nuna jameel din cikin nishadi tare da cewa
"Nace ka qyaleni zanji da hakan,babu wani abu da zai faru" shi dai minister bai ce komai ba,shiru kawai yayi yana sauraronsu,amma cike yake da tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo,sallama jaleel yayi musu ya fita,yana fita jameel ya matso kusa yana fuskantar mahaifinsa
"Yanzu Abba haka zaka bari wannan shashashan yaji da matsalar nan? Bayan duk shi ya samu a cikinta? Yanzu idan aka samu labarin abinda kuka qulla kai da Kim Young Dal fa? Me kake tunanin zai iya faruwa?" Gyaran murya minister yayi
"Jameel ka kwantar da hankalinka,kuma idan ban bawa jaleel damar ya gyara abinda ya lalata ba yaya kake so muyi? Dole mu zuba masa ido muga abinda zaiyi,domin shi ba shashasha bane kamar yadda kake zaton shi" duk da dai jameel bai gamsu da hakan ba amma haka ya haqura,yayiwa mahaifinshi sallama ya tashi ya fita.

Mai martaba yana zaune duk hankalinshi ba a kwance ba,yana ta tunanin me zai ce wa shukra,shi kadai yake magana da kanshi
"ko dai ce mata zanyi banyi niyyar nayi mata qarya ba? Ba da gangan nayi ba,a'ah a'ah ba haka ba,ce mata zanyi...." Maganar chief eunuch ce ta katse shi
"Your majesty ta qaraso,a ina kake buqatar ganinta?"
Dan zabura yayi daga inda yake zaune,kafin yace
"Ka kaita dakin da nake ganin baqi na musamman" dago kai chief eunuch yayi cike mamakin abinda yaji,abinda bai saba yi ba,da ido mai martaba ya bashi tabbacin haka yake nufi,hakan yasa ya juya domin kai shukra inda ya kamata.

Suna tsaye a waje,cikin rakiyar ladies in waiting da suka rakota,ga jerin royal guards da suke gadin grand palace,tana tsaye ta rusunar da kanta,ita kadai take magana da kanta
"Ce masa zanyi KING a'ah your majesty ya kamata nace,ko kuma royal highness,ko dai imperial majesty?" Cikin rikita ta rasa inda zata sa kanta,taji muryar chief eunuch,zuwa yayi gabansu ya tsaya tare da cewa
"Ki biyo ni" bin bayanshi tayi har dakin da mai martaba yake ganin baqi na musamman,kalle kalle take tayi yadda aka tsara dakin gwanin sha'awa,akwai wajen zama na mai martaba sai dan qaramin pillow a qasa wajen zaman baqo,ta can gefe taje ta tsaya,jiyo muryarsa tayi
"Tana ciki?" Chief eunuch ya amsa masa da
"Ehh tana ciki your majesty" hakan yasa ta rusunar da kanta sosai,ta ranqwafa kamar zatayi ruku'i amma bata kai qasa sosai ba,yayinda ya sa hannyenta biyu akan cikinta,leqowa mai martaba ya fara yi,ganin yadda tayi yasa shi saurin qarasowa ya zauna a mazaunin sa,kallonta yayi da ko motsawa batayi ba yace
"Zo ki zauna" sai a lokacin ta dago kanta,amma ta kasa hada ido dashi kuma bata motsa daga inda take tsaye ba,cikin taushin murya ya qara ce mata
"Zo ki zauna nace" a hankali ta fara daga qafarta tazo dai dai inda yake tana fuskantar shi,tsugunnawa tayi da sauri akan gwiwoyinta  tare da rusunar da kanta tace
"Royal Majesty!!!!" Da qarfi,ta cigaba "ka yafe min ban san kai sarki bane,tunani na bai taba bani hakan ba,na san na cancanci mutuwa akan abubuwan da na aikata maka,amma ka taimaka ka ceci rayuwata a karo na farko ba zan qara ba" da qarfinta take maganar kuma cike da tsoro,sai da ta gama tsaf sannan mai martaba ya tuntsire da dariya har da hantsilawa gefe,sai da ya daidaita kansa sannan yace mata
"Ke dalla can,tashi ki zauna sosai,dama halinki ne bani dariya,ina ta tunanin me zan fada miki kika zo kika wani ce ROYAL MAJESTY" ya qarasa yana qara tuntsire mata da dariya,mamaki sosai hakan ya bata,ta dago kanta ta kalleshi,suna hada ido nan da nan ta sauke kanta qasa tana rufe idon,shi ya cigaba da magana
"Ai ni ya kamata na baki haquri,ke kuma kinzo kina sani jin kunya"
Qara rusunawa tayi hannayenta a qasa tace
"Dama ba kirana kayi ka hukunta ni ba?" Da mamaki yake kallonta
"Hukuntaki kuma? Meyasa zanyi haka? Ai nine nayi miki qarya nace miki ni dan sandan sirri ne,naso fada miki gaskiya amma sai nake jin dadin yadda kike mu'amala dani kuma har ta kawo mu ga haka,saboda haka kada kiyi fushi dani,ba da niyya nayi hakan ba" a firgice ta dago kanta
"Mai martaba ka daina fada min haka,ni wacece da na isa nayi fushi da kai?" Leqa fuskarta yayi
"Da gaske? Ina ta tunanin zaki ɗaka min duka ne saboda nayi miki qarya?" Da sauri tace
"Duka...duka mai martaba,don Allah ka daina fadar haka,idan royal guards suka ji yanka ni zasu yi" dariya ya sheqe da ita
"Ba zaki iya dukana ba? Amma ai kin taka  gadon bayana kin hau katanga" ai kamar ya tunzura ta da sauri ta dago kai ta kalleshi,fuskarta har yanzu cike da tsoro tace
"Your majesty,a wancan lokacin ban san kai sarki bane,ka gafarce ni"
"Yauwa,yanzun ma zaki iya yin kamar har yanzu baki san ni sarki bane? Ki dinga magana dani yadda kikeyi da,ki daina wannan durqusawar ki dauka kawai ni dan sandan sirri ne a wajenki ba sarki ba" kallonshi take da mamaki
"Your majesty" yana kallon yadda takeyi hakan yana burge shi yace
"Kinsan meyasa ban fada miki gaskiya tun da wuri ba? Saboda ina tunanin zaki yi abinda kike yi yanzun,ina tunanin zaki daina sakewa a kusa dani kamar yadda kike yi yanzu,na san abin ba mai sauqi bane a gareki tunda kin riga kinsan ni sarki ne,amma saboda wani dalili nawa ina buqatar ki cigaba da kallona kamar da,mutum ne kamar kowa ba sarki ba a duk lokacin da kike tare da ni"
Hankalinta ne ya dan kwanta,tsoron da take ji ya fara raguwa,a hankali tace
"Amma your majesty,ban isa nayi maka yadda kake so ba,domin dokar qasar nan...." Kafin ta qarasa cikin dakakkiyar murya yace
"Kin isa kiyi hakan,ke qarewarta ma umarni na baki,it's an imperial order kuma ki karya imperial order kin san mai zai biyo baya,kin ji me nace? "
Idonta ta dago ta kalleshi ido cikin ido,kwarjini yayi mata a cikin dragon robe da yau ne ganinta na biyu dashi a haka,hakan yasa ta qara sunkuyar da kanta,leqa fuskarta ya fara yi yace
"Dago dai" ta dan dago kadan,ya qara cewa
"Dago dai" ta qara dagowa kadan,haka har ta dago fusukarta sosai ta kalleshi,yana ta mata dariya,amma ita ta kasa sakewa,har yanzu mamaki bai bar ta ba,haka ya cigaba da surutun sa amma taqi sakewa har ya sallameta ta fito,a hankali tana ta qarewa wajen kallo har ta fita daga grand palace,a inda ta fita ta barshi a zaune murmushi ne akan fuskar shi yana tuna yadda ta dinga yi mai yace
"Ina fatan tayi saurin komawa yadda take da,ta dauke ni mutum kamar kowa"

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now