Page 41

68 4 0
                                    

Page 41

Ladies investigators kyawawan 'yan mata cikin shigar cikakken uniform dinsu,suna tsaye a farfajiyar Office of investigation fuskokinsu kowanne da annurin farin ciki,'yan matan biyar suna tsaye waje daya kasancewar kusancin da yake tsakaninsu
Rukayya,sameerah,Afrah,Aliya da kuma shukra,Aliya da ta kasance mara nutsuwa a cikinsu ce da qarfinta take cewa
"Yanzu dai yau kowa za'a fada masa inda zai tafi aiki!" Rukayya da sameerah da tasu tafi zuwa daya suna fuskantar junansu suke magana,ruqayya ce tace
"Ni dai zanso a kaini inda ake yin ROYAL ATTIRE,zanji dadi sosai" (inda ake dinkin kayan sarauta) sameerah itama cikin murmushi tace
"Ni kuwa nafi son ROYAL KITCHEN don ance suna baka abincin da dangin sarauta suke ci saboda in suna ganin girmanka,kuma zaka rufa musu asiri" Aliya da suke tsaye a gefe ita da Afrah da shukra suna jiyo me su ruqayya suke cewa,Aliya tace musu
"Lallai ku inda kuke so kenan? Ni kam zanso a kaini office of PALACE MANAGEMENT" shukra ta kalleta
"Meyasa kike son can?" Murmushi aliya tayi ta sunkuyar da kai
"Saboda ma'aikatan da suke wajen sun yi sosai" cikin rashin fahimta shukra tace mata "sun yi kamar ya kenan?" Afrah da take gefe tace
"Muna jin labarin cewar samarin da suke aiki a wajen kyawawa ne kuma majiya qarfi" ruqayya da take gefe tacewa Aliya
"Kinga ki kiyayi kanki! Kada kisa kanki cikin matsala" harara ta aika mata
"Meye laifi aciki don ina son aiki a cikin kyawawan samari?" Shukra ta tabe baki
"Rabu da ita,babu laifi,nima inason aiki da kyawawan tare da ke" harara aliya ta aikawa shukra
"A'ah kada ma ki fara,bana so" dariya ta bawa shukra sosai,tace mata
"Me yasa?" Aliya har yanzu hararar ta take
"Saboda su din nawane mana,kada ki kuskura ki mayo tunanin zuwa kusa dasu" dariya duk suka fara yiwa Aliya,ita kuma ta dake irin ita da gaske take dinnan.

Daidaita tsayuwar su sukayi dukkansu jin tahowar madams investigators din,a gabansu suka tsaya gaba dayansu,sumayya da take tsakiya ce ta fara magana
"Da fatan kun shirya domin zuwa inda zaku aiwatar da ayyukan ku,za'a raba ku tsakanin ofisoshin da suke cikin inner court,zakuyi aiki kuma ku dinga kawo mana report" rusunawa sukai dukkansu a tare
"Yes  My lady!" Takadda ta karba a hannun ta kusa da ita ta bude tare da fara kiran sunayensu kamar haka
"Afrah da Rukayya- Grand palace"
"Sameerah- palace kitchen"
"Aliya-office of palace cleaning 🧼 🧹"
"Shukra-Royal treasury"
Haka akayi ta kiran sunayen su kaf,tun da aka kira sunan Aliya taji an kaita wajen masu share-share da goge-goge ta cika tayi fam,bare ma da taga an kai shukra ROYAL TREASURY inda nan ne duk wata dukiya da duk wani abu mai daraja na qasar yake,kuma eunuchs sune suke kula da komai a wajen,babu wanda yake shiga lamarinsu domin sune masu cikakken iko a wajen,idon kowa akan shukra da mamaki bayan an fadi inda aka kaita domin sun san yadda take da karambani to lallai zata samu matsala a royal treasury,kuma kamar ita kadai aka kai wajen,shukra ko kadan bata fahimci irin kallon da suke mata ba sam,bayan sun watse ta shiga office dinsu nadeeyah domin ta fada musu inda aka kaita,nadeeyah da basma shiru sukayi da suka ji abinda tace,zare ido shukra tayi
"Me yasa naji duk kunyi sanyi haka? Akwai wata matsala ne my lady?" Basma ce ta bata fuska
"Kawai dai zaki sha wahala ne,ina tunanin ma da gangan sumayya ta tura ki can!" Murmushi tayi
"Haba menene abin wahala? Ni ce fa shukra,duk abinda na riqe ai sai naga qarshen shi nake sakin shi" girgiza kai nadeeyah tayi cike da takaicin sakarcin shukra
"Ai wannan dalilin ne zaisa ki sha wahala a can din shukra"

"An kai shukra Royal treasury?" Jaleela tayi tambayar,sumayya da take zaune tana fuskantarta ta rusunar da kanta
"Yes your highness! Kamar yadda kikayi umarni,na duba hanyar da zai fi mana sauqin fitar da ita daga cikin masarautar nan,kuma karambanin ta ne kawai zai zamar mata matsala a royal treasury domin zata yi qoqarin ganin ta qure eunuchs din da suke wajen,su kuma ba zasu qyale ta ba" da murmushi jaleelah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dago idonta cikin na sumayya tace
"Na so ace na san cewar zaki yi min amfani tun tuni,da na taimaka miki kin samu babban matsayi" rusunar da kai sumayya tayi
"A'ah your highness,ina godiya ma da kika zabi ki yafe laifukan da nayi miki a baya"
Jaleela murmushi tayi
"A'ah,a yadda kike dinnan zakiyi kyau a matsayin director din office of investigation,ba ma chief madam ba wanda kika riqe a baya" dago kai tayi cike da murna da murmushi tace
"Your highness! Zan biki,zan yi miki biyayya ko da kuwa zan fansar da rayuwata ne"

ROYAL CONSORTWo Geschichten leben. Entdecke jetzt