Page 22

51 3 0
                                    

Page 22

Sameerah tare suka dawo da shukra wajen karatun,yayinda aka fara bitar karatu,kowa da littatttafan sa a gaba,a zaune suke a qasa,sai qaramin tebur daidai yadda hannunsu zai kai rubutu,sai tawada (ink) da abin rubutu (brush) wanda dashi suke amfani domin yin rubutun,littafin doctrine of the mean (kamar constitution na qasa) ake karanta musu suna cikin duddubawa,malamar tana karantowa suna duba littafin,chief sumayya ce tazo daidai inda shukra take ganin ta tasa pejin da ake karantawa,durqusawa tayi ta budo mata shafin sannan tace
"Nan ne inda ake karantawa" tare da nuna mata kan layin inda ake karantawa,kallon kallo suka fara yi a tsakanin su ganin wani sabon mutunci da lady sumayya take yiwa shukra.

Washegari da safe shukra a tsugunne a bakin rijiya tana wanki,slaves din da suke aiki a wajen ne suka zo da gudu
"My lady,bai kamata kina wankin nan ba,domin aikinmu ne" dago kanta tayi ta kallesu
"Na tashi ne kuma naga babu abinda zanyi shiyasa,ku barshi kawai na qarasa" shukra ta basu amsa
"A ah my lady,idan aka ganki kina wanki hakan zai iya zamar mana matsala" miqewa shukra tayi daga wajen,ta dauraye hannayenta,har zata tafi ta juyo fuskarta da murmushi ta e
"Tunda ku kuna min magana bari in tambayeku mana?" Daya daga cikin bayin ne tace
"My lady kiyi tambayar ki"
"Na san dai ladies investigators suna aiki sosai,amma meyasa tunda nazo banga kowa yana aiki ba,kuma da na tashi daga bacci ma banga kowa ba,duk ina suka tafi?" Murmushi baiwar tayi
"Ai my lady a wannan lokacin na kowace shekara ladies investigators suna jarrabawar qarshen shekara,shiyasa yanzu kowa yana shirin yin jarrabawar ne,domin gobe ne ma zasuyi ta"
Jinjina kai shukra tayi sannan tayi musu godiya ta bar wajen.

Chief sumayya ce a office din director,tare suke da nadeeya da basma,director ta gama jin abinda ya kawo ta tsaf
"Yanzu kina nufin kina son shukra tayi wannan jarrabawar?" Director ta tambaya
"Ehh my lady,tunda itama yanzu lady investigator ce,ya kamata ayi mata yadda akewa kowa domin haqqinta ne hakan" sumayya ta fada,murmushi director tayi tare da cewa
"Gaskiyarki,ni banyi wannan tunanin ba,duba da cewar jiya jiya tazo,amma ayi hakan kawai" sumayya cike da murmushi tace
"Nagode ranki ya dade,ni zan taimaka mata wajen karatun jarrbawar" jinjina kai director tayi,sumayya suka juya suka fita itada su basma,office dinta ta wice yayinda su basma suka tsaya domin tattaunawa.

Basma ce ta kalli nadeeyah cikin zare ido tace
"Me chief take nufi da tana son shukra ta yi jarrabawa? Ai baza ta iya yin ta ba"
Nadeeyah cikin jimami,domin ita hankalinta ya kwanta da shukra tace
"Wannan wani abu ne kawai da chief take shiryawa domin korar shukra daga office dinnan,zatayi hakan ne ta koreta salin alin ba tare da wani ya zarge ta ba"
Basma ce ta kalleta cikin rashin fahimta
"Ban gane tana son ta koreta ba" nadeeya ta kalleta
"Haba basma,kin manta dokar jarrabawar ne? Ana bada maki ne kamar haka PASS,CREDIT da kuma DISTINCTION kuma kinsan mutum idan bai samu credit ba to shikenan ya rasa matsayinsa na lady investigator kenan" basma cikin damuwa tace
"Na kuwa tabbata yarinyar nan ba zata samu ko PASS din bane,shiyasa sukayi hakan domin su koreta"

Shukra tana tsaye a gaban sumayya a office dinta,domin ta aika a kirawo ta domin yi mata bayanin zata dauki jarrabawa gobe tare da kowa,cike da damuwa shukra ta kalleta
"Amma my lady ni da ban san komai ba,ya zanyi?" Murmushi sumayya tayi
"Kada ki damu shukra,kawai ki rubuta iya abinda kika sani,kada ki takurawa kanki kinji?" Jinjina kai shukra tayi,tayi wa sumayya sallama ta tafi.

Ranar har dare ya ratsa tana zaune a wajen karatu tana karanta wani littafi,ana jin muryar ta tana haddar "yawan palace maids din da suke cikin masarautar nan

14 attendants
20 sewing
23 embroidery
2 academy
2 treasurers
13 kitchen
11 beverages
12 laundry

Tana ta karantowa ba tare da ta duba littafi ba,daga baya ta duba taga akwai inda tayi kuskure,haka dai ta cigaba da karatunta a cikin daren,domin shiryawa wannan jarrabawa.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now