Page 25

66 2 0
                                    

Page 25

Har dare sameer da manager suna nemanta amma basu ganta ba,hakan yasa sameer dawowa gida kuma har lokacin abdullahi bai dawo ba,yana tsaye yana ta kai-kawo a tsakar gidan yaji shigowar abdullahi,turus yayi ganin sameer a gidan,sameer ne yace masa
"Yau baka dawo da wuri ba,lapia kuwa?"
"Lafiya qalau,na biya wani waje ne" abdullahi ya bashi amsa
"Toh sai ka shiga ka kwanta"
"Toh yallabai" abdullahi ya fada tare da shiga dakinsa,yana shiga ya fara bin dakin da kallo ya san an taba masa kaya,hakan yasa ya duba abinda yake tunanin shi za'a dauka kuwa yaga baya nan,fitowa yayi ya murde hannun sameer ta baya tare da cewa
"Ina headband dina? Me kayi dashi?" Cikin jin zafin yadda abdullahi ya murde masa hannu ta baya yace
"Kayi haquri dauka nayi na bawa wata lady investigator saboda ban yadda da logo din da yake jiki ba" da sauri abdullahi yace
"Lady investigator kuma?"
"Ehh kamar qanwa take a wajena,amma ina bata ta gane LOGO din da yake jiki ta fella da gudu ta tafi nemanka kuma har yanzu ban ganta ba" jin haka da sauri ya saki hannun sameer ya juyo daidai fuskarsa tare da cewa
"Kace ta gane LOGO din da yake jiki?" Gyada kai sameer yayi
"Ehh shukra ta gane logo din" jikin abdullahi ne gaba daya yayi sanyi,da qyar yace wa sameer
"Kace sunanta shukra?"
Gyada kai sameer ya qara yi
"Ehh sunanta kenan,shukra Anas malak"
Qwalla ce kawai ta cicciko a idon abdullahi,yacewa sameer
"Taho muje ka kaini cikin palace din,ni zan nemo ta"

Suna zuwa cikin palace,bureu of music suka fara zuwa,manager ya shaida musu yanzu shukra ta bar nan kuma ta tafi gidansu ne nemanshi,hakan yasa suka qara juyowa suka dawo.
Da zuwanta ta tarar babu kowa a gidan,tana ta bude bude,ta shiga nan ta shiga can,tsayawa tayi tana tunani
*FLASHBACK*
tana yarinya qarama suna tsaye da abdullahi a tashar jirgin ruwa da je garin,irin headband din da sameer ya samo a dakin abdullahi ne a hannunsa yana nunawa shukra
"Shukriyya,kada ki manta da wannan zanen (logo) domin matuqar dai kina tare da wannan abin to komai dadewa zan dawo gareki" gyada kai tayi tare da cewa
"Ba zan manta da hakan ba,amma kwana nawa zakayi ka dawo?" Murmushin jin tausayinta abdullahi yayi tare da cewa
"Duk dadewar da zanyi,nayi miki alqawarin zan dawo gareki,ki kula da kanki"
Motsin da taji ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi,juyowar da zata yi suka hada ido da abdullahi,hannunta ne ya saki kamar babu jini a jikinta ta daskare a tsaye a wajen,matsowa yake yi kusa da ita yana cewa
"Shukriyya,Ke ce? Shukriyya" hawayen farin ciki ne kawai ya lullube fuskar ta,sheshsheqar kuka ta fara,hakan yasa yayi saurin qarasowa gareta tare da rungumeta sosai a jikinsa,a hankali ta bude bakinta tare da cewa
"Orabeuni" (Babban yaya in korean)
Dagota yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta tare da cewa
"Qara fada shukra,ni ne" hawayen bai daina zuba a idonta ba tace
"Dama kana raye? Zaka dawo gareni Yaya Abdallah?"
"Ina nan Shukriyya,dama na fada miki duk dadewar da zanyi nayi miki alqawarin zan dawo gareki"
Tuni suka manta da sameer a wajen,hakan yasa shima ya basu waje,nan gaba ya nemi qarin bayanin alaqar da ke tsakaninsu,waje suka samu suka zauna,shukra da har yanzu da hawaye a fuskarta tace
"Yaya duk lokacin da zanyi wa su Abbana addu'ah ina hadawa hadda kai domin ban taba tunanin kana nan a raye ba,na zata ni kadai ce na rage bani da sauran dangi a duniya" murmushi yayi mata shima da hawaye a fuskarshi tare da cewa
"Na dade ina nemanki shukra,amma ban sameki ba,duk cikin garin nan babu inda ban zagaya ba amma ban sameki ba"
Shiru shukra tayi ba tare da tace komai ba,abdullahi yana mata kallon tsanaki ganin yadda ta girma,tare kuma da farin cikin qara ganin qanwar tasa,jan hanci tayi da ya taru da majina
"Yaya kullun ina tunaninku,da Abba da yaya Abdulshakur,ina ma ace zan qara jin muryoyinsu suna kirana shukriyya?" Tausayinta ne ya lullube shi,dafa kafadarta yayi
"Shukriyya Abba zai yi matuqar farin ciki a duk inda yake domin kema kina cikin farin ciki,kuma nayi masa alqawarin zan kula dake,zan zame miki garkuwa" haka suka yini tare,da yake tunda zata shigo cikin gari ta cire uniform dinta ta skaa normal kaya,hakan yasa babu mai ganeta suka cigaba da zama a cikin gidan tare da hirar yaushe gamo har dare,a nan ta kwana sai da asuba ta koma office of investigation.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now