Page 45

76 7 0
                                    

Page 45

Fitowarta da safiyar kai tsaye office din IG ta nufa,cikin kulawa yake ce mata
"Shin zaki iya shiga royal treasury kamar yadda kikayi niyya?"
"Ehh yallabai,kada ka damu,ina da hanyar da zan iya yin hakan" kallon tuhuma ya jefe ta dashi,fahimtar hakan yasa tace masa
"Zan fada maka idan kun dawo" jinjina kai yayi
"Ki bi a hankali,domin lafiyarki ta fi hujjar muhimmanci a wajen mu" har cikin ranta taji dadin kalamansa,dan rusunawa tayi tace
"Nagode sosai da kulawa" lieutenant da assistant ne suka shigo,cikin girmamawa lieutenant NAM yace
"Yallabai zasuyi mana nisa,dawakan suna waje cikin shiri" da yake dama a tsaye yake,kawai yace musu
"Toh muje kawai" fita sukayi dukkansu har shukra,sallama sukayi sannan suka wuce,abdullahi ne ya qaraso inda take tsaye shima sukayi sallama,yake fada mata zasu kwashe yinin yau ne a kan hanya shiyasa ba zasu dawo da wuri ba,murmushi tayi tace
"Hakane yaya! Ka kula da IG sosai kaji?" Murmushin shima yayi mata
"Kada ki damu da wannan! Duk zamuje mu dawo lapia,ni nafi damuwa da ke ma saboda bana jin dadin duk zamu tafi mu barki bayan mun san cewar zasu iya cutar dake" dariya tayi sosai
"A'ah kada ka damu! Wa ya isa ya taba ni a cikin palace? Babu abinda zai same ni" dan gyara tsayuwar sa yayi
"Amma..." katse shi tayi
"Kai dai kawai ka kula sosai,Allah ya dawo daku lapia" murmushi yayi mata,kawai gani yayi ta daga hannu tana qirge
"Kwana nawa zaka yi? Kwana daya? Ko Kwana biyu?" Dariya sosai yayi
"Kinga yarinyar nan! Baki manta ba kenan"
"Ya za'a yi na manta,bayan sai da na shafe shekaru bakwai kullum da daddare sai nayi tunanin hakan" miqa masa dan qaramin dan yatsanta tayi
"Yanzu mu qulla,kayi min alqawarin wannan karon zaka dawo da wuri" murmushi kawai yakeyi yana jinjina yarintar shukra,shima dan qaramin dan yatsan sa ya miqo tare da hadashi da nata suka qulla
"Naji! Nayi alqawari"
"Ka kula da kanka yaya! Ina nan ina jiranka"
"Kema ki kula da kanki! Sai na dawo" cikin farin ciki da walwala suka rabu
(Toh sai muce Allah ya qaddara saduwa 😝)

Da daddare bayan duhu ya shiga,lady investigators ne zaune a office dinsu,Aliya ce tace
"Yau palace din shiru saboda tafiyar mai martaba"
Sameerah ce ta kalleta
"Ehh ai ya zama dole kowa ya bishi domin addu'o'i da sauran abubuwan da akeyi a can na ahalin sarauta"
"Ji nake kamar fatalwa zasu iya diro mana cikin irin wannan lokacin" cewar ruqayya
"Dalla can! Banza matsoraciya" Aliya ta fada tare da banka mata harara,juyawa tayi ta kalli Afrah da tayi shiru kamar mai tunani
"Wai ina shukra ne?"
"Yanzu zaki ganta!" Afrah ta bata amsa
"Amma ai zata yi report,ya kamata ace tana nan" sameerah ta fada
"Zanyi mata nata report din,ba sai kun jira ta ba" tabe baki sameerah da ruqayya sukayi.

Ko ina a cikin masarautar shiru,kamar babu halittu a ciki,royal guards da 'yan sanda duk babu wasu jiga jigai sai 'yan kadan kuma masu qananan matsayi,wasu mutane ne suka fara dirgowa cikin office of investigation ta katanga,baqaqen kaya ne a jikinsu,sun rufe fuskar su da baqin qyalle kamar niqab,a hankali suke bin bango da sanda domin kada aji motsin su,bangaren dakin kwana suka nufa yayinda shukra take cikin daki tayi shigarta tsaf cikin uniform din ladies in waiting,irin uniform dinsu ne amma rigar fari da blue,wutar kendir din da take dakin ta kashe tare da nufar hanyar waje,kamar wacce ta tuna wani abu kuma sai ta tsaya,juyowa tayi zuwa inda take ajiye littattafan ta,bude wani littafi tayi tare da dauko shaidar da take ta ajiye da ita wato takaddar chek din kudin da jaleel yasa aka bawa doctor Nuh kuma kudin ne aka diba a Royal treasury,waje ta samar musu a cikin kayanta ta adana sosai sannan ta fito.

A daidai qofar dakinta suka tsaya tare da zaro sharbebiyar wuqar su,cikin sanda suka shigo dakin,ganin shimfidar da mutum akai yasa dayan kawai ya soka wuqar,ya daga ya sake sokawa,ganin kamar ba mutum yake suka ba yasa suka dage bargon,filo suka gani a jere babu kowa a wajen,da hanzari suka fito domin bin bayanta.

Tana tafe tana waiwaye don kada kowa ya ganta,daga bayanta taji muryar sumayya
"Ina zuwa?" A rude ta juyo ta kalleta sannan ta rusunar da kanta,sumayya ce ta qare mata kallo
"Uniform din jikin ki.." sosa kai shukra tayi
"Madam nadeeyah ce take son nayi mata wani aiki,shine zan shiga a matsayin knitting maid (masu dinki)" jinjina kai tayi tare da yi mata kallon gefen ido
"To shikenan,kafin ki tafi bari na aikeki office of palace cleaning" tsayawa shukra tayi har sumayya ta kawo aiken sannan ta fito daga office of investigation,tsayawa tayi tana kallon qullin kayan da sumayya ta bata,can qasan maqoshinta ta furta
"Yanzu ya zanyi? Ya kamata na qarasa wajen nan kafin qarfe taran daren nan! Amma dai bari na fara kai aiken nata tukunna"
A qofar office din da sumayya ta aikota ta tsaya,a hankali ta fara magana
"Akwai wani a nan wajen ne?" Jin shiru yasa bata qarasa ba,mutanen nan ne masu rufaffiyar fuska suka diro tare da soka mata wuqa a baya,a take ta zube a qasa,juyota sukayi domin ganin fuskarta dayan yace
"Ba ita bace!" Cike da mamaki suke kallon juna bayan sumayya ta tabbatar musu zasu sameta a nan.
(Abinda tayi shine,ta samu wata lady in waiting ne domin ta taimaka mata da aiken sumayya domin wancan abinda zataje yi yafi mata muhimmaci,kuma hakan ya faru ne saboda Allah yana son ya kareta don ita bata san tarko aka sa mata a wajen ba)

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now