Page 37

63 6 0
                                    

Page 37

Washegari da safe shukra tana jin labarin ai an samu hujjojin da suke tabbatar da cewar queen haneefah tana da alaqa da doctor Nuh,da gudu ta fito ta taho police bureu,IG yana tsaye suna magana da wani dan sanda ta fara qwala masa
"Yallabai! Yallabai!!" Juyowa yayi,ta fara yi masa magana tana haki
"Yallabai ta yaya za'ayi ace haka? Ni na tabbatar her majesty bata da laifi! Ina da tabbacin haka!" Cikin dakewa ya ke kallonta,amon muryarsa da karaya da kuma kausasawa yace mata
"A yadda abubuwa suka juye yanzu,zaki iya karbar mummunan hukunci idan kika ce zaki kare her majesty! Saboda haka kiyi shiru da wannan maganar,ki cire hannunki a ciki,kada ki aikata komai"

Mai martaba a zaune a quaters din queen haneefah,rasit din na yang miliyan dari ya miqa mata tare da cewa
"Ki yi min bayanin menene wannan?" Dubawa tayi ta dago kai ta kalle shi
"Ban san ko menene ba your majesty!" Jinjina kai yayi
"A baya da na tambayeki ko akwai wani abu da ya rage da baki fada min ba,ko kuma wanda zaki kare kanki dashi,kin ce min babu" daga kai tayi,alamar "Ehh" amma bata yi magana ba,ya cigaba
"Ina son na tambayeki,shin kinyi wannan maganar da wani daga cikin ahalin gidanku?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta qasa,yace
"Ina tambayarki!" Dagowa tayi amma bata yadda sun hada ido ba tace
"Ehh nayi maganar dasu,domij abin yayi girman da ba zan iya riqeshi ni kadai ba,kuma ban taba sanin cewar doctor Nuh yana da alaqa da ahalina ba" yanayin fuskarshi ne ya canja gaba daya zuwa bacin rai yace
"Da kenan boye min kika so kiyi?" Durqusar da kanta tayi kamar bai bada haquri tace
"Ba haka bane your majesty! Ban yi tunanin in fada maka har cewar nayi magana da 'yan uwana ba,domin ban san hakan zai iya zama matsala ba" shiru kawai yayi bai qara cewa komai ba,kafin daga bisani ya tashi ya fita,aikawa yayi a kirawo masa chief secretary kafin ya qarasa grand palace.
Yana shiga ya zauna chief secretary ya qaraso,shigowa yayi ya rusuna ya gaishe da mai martaba,bai amsa masa ba kuma hakan ba wani abu bane a wajensu,chief secretary da ya lura da yanayin mai martaba yace masa
"Your majesty! Yanzu yaya zakayi kenan?" Juyowa yayi sosai ya kalleshi
"Ka miqa alhakin binciken zuwa ga tribunal"
"Yea cho-na" chief secretary ya fada tare da fita daga wajen.

Chief maid din queen haneefa ce ta ahigo cikin hanzari,tare ta samesu da minister of state affairs,durqusawa tayi tace
"Your majesty,mai martaba ya miqawa tribunal alhakin bincike!" Idanuwa queen haneefah ta zaro waje
"Me kikace?" Jinjina kai chief maid tayi,ta cigaba da magana
"In dai hakan ta faru,da ni da sauran duk yaran da muke anan quaters dinki za'a kama mu a tafi damu domin tambayoyi,amma kada ki karaya,ina son ki qarfafa zuciyar ki,kada ki nuna musu karayarki" sai yanzu minister of state affairs yayi magana
"Gaskiyane your majesty! Dukkanmu hakiman arewa zamu goyi bayanki,ya kamata ki qarfafa zuciyar ki,kada ki nuna karaya!" Ita dai queen haneefah bata ce musu komai ba,sai hawaye da yake qoqarin zubowa daga idonta,chief maid dinta tace
"Kiyi haquri,ko da an kasa samo hujjar da zata wanke ki,toh lallai mu zamu jarbi hukuncin a maimakon ke,zamu fadi cewar mu mukayi komai ba tare da saninki ba,amma tabbas zamuyi duk yadda zamuyi muga mun tseratar da ke your majesty!" Da qyar ta iya bude bakinta
"Lady Han!" Ta kira chief maid da sunanta,kafin ta qara cewa komai suka jiyo dirowar 'yan sandan tribunal cikin quaters din,da sauri suka fito don ganin me yake faruwa,ladies in waiting dinta ne 'yan sandan suke fuzgo su da qarfin tsiya,cikin sigar tozarci da wulaqanci,yayinda jameel da wasu 'yan sandan guda hudu a bayansa suke nufo inda take,tsawa ta daka musu
"Me kuke yi haka!?" Jameel dai dai lokacin da ya qaraso gabanta ya rusunar da kanshi
"Ki gafarce ni your majesty! Muna aiki ne bisa umarni mai martaba,zamu tafi da dukkan ma'aikata da maids din quatera dinnan domin yi musu tambayoyi"
Daga murya yayi,tare da cewa sauran 'yan sandan da suka dakata tunda sukaji muryar queen,yace musu
"Ku hanzarta!"
"Yes sir" suka amsa sannan suka ci gaba da fuzgo dukkan ma'aikatan wajen,minister of state affairs yana ta ihun su dakata,amma ina! Ba sa jii ko kadan,sai da suka kwashe kowa,sai queen haneefah ita kadai a tsaye tare da minister,numfarfashi take yi kamar mai cutar asma,hawaye ya gangaro kan fuskar ta,me yake faruwa da ita haka? Ko kuma me yake shirin faruwa da ita?

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now