Page 32

75 4 0
                                    

(A cikin masarautar JOSHUN dukkan wasu mata da suke cikin inner court sunan su PLACE MAIDS,amma suna da rabe rabe,da kuma matsayi matsayi,akwai kitchen maids wato masu girki,akwai ladies in waiting wato wanda suke a bangaren masu gidan,su suke kusu dukkan hidima,guda shida daga cikinsu kuma suna binsu zuwa duk inda zasu je,a cikinsu ne ake da chief maid,kowa yana da chief maid dinshi,wacce itace shugabar ladies in waiting din bangaren,akwai ladies investigators suma suna cikin palace maids,amma su sunada aiki na musamman,kuma ana daukan masu ilimi ne kuma daga dangi mafi nasaba a qasar tunda su ba aikin wahala suke ba,sannan akwai court ladies wanda sune muqarraban sarauniya,kuma sune kamar qwarqwarorin sarki,duk wacce sarki ya nuna ra'ayi a kanta a cikin palace maids,to za'a qara mata girma zuwa court lady,idan kuma ta kai ga sun hada shimfida da sarki,toh za'a qara mata matsayi ta zama consort,a halin yanzu ana qoqarin qarawa jaleela matsayine daga special court lady zuwa consort,ina fatan kuna fahimta sosai)

Page 32

Shukrah cikin shirin uniform dinta ta fito daga daki,a farfajiyar office dinsu ta tarar da sameerah,Aliyah,ruqayya da Afrah suna tsaye suna magana,zuwa tayi cikin yanayin da ya riga ya zama jikinta,ta dan rusuna tare da cewa
"Ni zan tafi" dukkansu banza sukai mata,sai Afrah ce cikin murmushi tace
"A dawo lapia shukra" murmushi tayi kafin ta wuce ta bar wajen,dukkansu suka bi bayanta da kallo,sameerah ce ta kwabe fuska
"Shekarata goma a cikin masarautar nan,amma ban taba ganin mutum irin ta ba" harara aliya ta rafkawa sameera tare da ce mata
"Duk dai wanda akeyi wa hassada,toh haqiqa yafi qarfinka ne" hakan yasa babu wanda ya qara tofa komai har ta bace musu suka cigaba da maganar da sukeyi.

Da sauri chief maid ta shigo cikin sitting room din lady jaleela,da hanzari take magana
"My lady,ga mai martaba nan yana tahowa" ba tare da ta amsa mata ba ta tashi da sauri ta fito,har ya qaraso farfajiyar quaters dinta,zuwa tayi har gabanshi tare da rusunawa tace
"Your majesty" murmushi yayi mata yace
"Kina lapia?"
"Lapia qalau your majesty,mu ahiga ciki ko?" Ta bashi amsa cike da murnar ganinshi,shima cikin yanayin farin ciki ya girgiza mata kai
"A'ah akwai dai inda nake son na kaiki" ba tare da ta ce komai ba ya miqa mata hannu,hannun ta itama ta saqala a cikin nashi,ya jata suka bar wajen,lambun da ya zamana wajen shan iskar sa suka nufa,daidai inda suka fara hango inda aka qawata da ado domin yin liyafar ya dakata,kidan algaita da ta fara jiyowa ya kalleta tare da cewa
"Menene wannan nake ji haka?" Cikin sigar zolaya,hakan yasa ta fara kalle kalle a wajen,har idonta ya fada inda mutane suke zazzaune,wajen yasha ado na musamman,bude baki tayi cike da mamaki tana kallon ami martaba,kafin tace komai ya daga mata kai  alamar tabbatarwa sannan yace mata
"Wannan itace kyautata a gareki" cikin tsananin farin ciki ta bude baki,ya qara dakatar da ita
"Kiyi shiru domin wannan bai cika abin mamaki ba,sauran yana gaba,mu qarasa" ya qarasa yana qara miqa mata hannun da ta saki cikin mamaki,cike da doki ta miqa masa hannu suka qarasa,suna zuwa wajen kowa ya dakata da abin da yake yi,masu busa algaita suka daina,kowa ya ranqwafar da kanshi qasa har suka isa wajen zamansu,kan dragon throne da take wajen mai martaba ya zauna,ita kuma da kujerar ta a gefen tashi bakinta yaqi rufuwa.

Sameer da manager da suke ranqwafe amma zuciyar su na dukan shida-shida suka runtse ido a tare cike da zullumin abinda mai martaba zaiyi musu a wannan taro na musamman.

Lady jalila da suka fara magana qasa qasa da mai martaba,shigowar chief eunuch ta hango,a bayanshi kuma shukra ce cikin uniform dinta,nan take yanayinta ya sauya,amma da yake qwararriya ce wajen boye bacin rai,babu wanda zai fahimci haka,mai martaba da ya ga haka ya kalleta cikin kulawa yace
"Na gayyace ta ne domin ki yaba mata da kanki a bisa qoqarin da tayi a case din su wakilin china" murmushin yaqe tayi tace
"Yes your majesty" cikin girmamawa.
Daidai lokacin da shukra ta qaraso gabansu,ta rusuna ta gaishesu,da murmushi lady jaleela ta kalleta
"Kinyi matuqar qaqari,a matsayina na wacce nayi sanadin shigo dake Office of investigation,ina alfahari dake"
qara rusunawa shukra tayi tare da cewa
"Nagode my lady"
"Ki je ki zauna" lady jaleela tace mata,juyawa tayi zuwa inda jaleela ta nuna mata ta zauna cike da mamaki,domin wajen zaman manyan baqi ne,inda har mahaifiyar lady jaleela tana wajen,mai martaba ne ya daga murya tare da cewa
"A fara kidan" nan da nan makida suka fara shirin fara kida,hango sameer da manager yayi,da sauri yace
"Ku dakata,ashe kunzo" da qarfi sosai,jikinsu ne ya fara rawa sosai suka fara sunne kai qasa,cikin zolaya yace
"Yau nasa anyi abincin alfarma kawai saboda ku,domin ku rama kwana biyun da kukayi a wancan lokacin kuna jiran abincin mai martaba" juyawa yayi ya kalli wata kitchen maid
"Abincin ya kammala?"
Rusunawa tayi cikin girmamawa tace
"Ehh ya kammala your majesty,har da cow skin din" qyalqalewa yayi da dariya
"Hahahaa kunji hadda ganda aka hada muku" shukra hannu tasa a baki tana dariya saboda yadda yayi maganar,sameer kuwa nan da nan ya tuno yadda ya dinga ɗurawa mai martaba ganda a cikin kasuwa yana ce masa sai ya cinye,rusunawa yayi da sauri
"Your majesty,mun cancanci mutuwa akan abinda muka aikata maka" ganin haka shima manager ta fadi qasa tare da rusunawa,cikin dariya mai martaba yace musu
"Meyasa kuke fadan haka a rana ta farin ciki irin wannan? Ku tashi kuci ku qoshi har yanda yayi muku" shukra kuwa dariyarta take son ranta,yayinda su kuma suka sauke ajiyar zuciya,zamansu suka daidaita suna jiran izini,mai martaba ya juya ya kalli jaleela
"Kafin a fara kida zan baki kyautar da nace zanyi miki a yau" murmushi kawai tayi ya cigaba
"Ina son zanyi appointing dinki as Royal Consort!" Kasa magana tayi kawai ta saki baki tana kallonshi,maids dinta suka fara kallon kallo cike da farin ciki,haj jameela ce ta miqe zumbur daga inda take zaune da farin ciki a fuskarta ta rusuna sosai tace
"Kana da matuqar karamci your majesty! Godiya muke" sai yanzu lady jaleela ta hada kalaman bakinta tare da ce masa
"Your majesty!" Shukra ma cike da farin ciki take murmushi tana kallonsu abin sha'awa,hannu kawai ya daga musu,nan da nan masu kida suka fara,masu rawa ma suka fara,lady jaleela baki yaqi rufuwa tana ta kallon mai martaba tace
"Thank you Your majesty" cikin farin ciki ya amsa mata da
"Ai kin cancanta,kuma ma ai kin yi qoqarin jira har wannan lokacin" cikin farin ciki aka gama liyafar kowa ya tashi ya sn nayi,yayinda mai martaba tare suka koma quaters din lady jaleela,shayi aka kawo musu suka zauna suna zantawa,nan yake fada mata tunda ya dawo da ita cikin masarautar yaso a nadata sarautar,amma abubuwa suka hana,cike da kulawa yake kwantar mata da hankali
"Duk da nasan yanzun ma hakan ba zai zama sauqi a gareki ba,hakiman arewa zasuyi yaqi da nadin sarautar ki,haka nan ma queen dowager,saboda haka sai kin daure sosai kinyi haquri har zuwa lokacin da komai zai zo qarshe" cikin murmushi tace masa
"Kaima na san hakan ba zai zama sauqi a gareka ba,domin zaka sha wahala wajen jii dasu har su amince a kan hakan"
"Babu komai,ai sai da shirya sosai,saboda haka nasan yadda zanji dasu" kofin shayin daya shanye ya dauka tare da daga shi yace
"Zuba min shayin,wata qila shine shayi na qarshe da lady jaleela zata zuba min,domin ta kusa komawa her highness jaleela" dariya sukasa gaba dayansu,ta dauki butar shayin ta tsiyaya masa a kofin yake sha,sai da ta dan ja fasali sannan tace masa
"Your majesty kayi min albishir na ban mamaki,nima ina son na baka dan qaramin tukwici" nutsuwa shima yayi yana fuskantar ta yace
"Tukwuici? Ai kuwa zanso naji menene wannan tukwicin" bakinta yqqi rufuwa kuma ta kasa magana kawai
"Your majesty " take maimaitawa ta kasa cigaba,sai da ya sata ta nutsu sannan ta sanar dashi tana da juna biyu,murna biyu ce ta lullube shi,na farko zai ga gudan jininsa,na biyu kuma ya samu hujjar da zai bawa duk wanda yake jayayya da zamowarta royal consort.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now