Page 54

96 4 0
                                    

Page 54

Sun shirya tsaf,duka su ukun suka baro gidan saukar baqin,sukayiwa qawar sulhee sallama sannan suka dauko hanyar da zata kaisu qofar shiga cikin birni.

A qofar shigowa cikin birnin JOSHUN da take zagaye da ganuwa,dogon layi ne na 'yan kasuwa da sauran mutane da suke shigowa daga qauyuka zuwa cikin birni domin hada-hadar yau da kullun,sai guards da suke tsaye a bakin qofa da suke tantance duk wani mai shiga,su duba name tag (kamar Id card ne amma na katako ne ake zana sunan mutane a jiki) sannan su duba fuskar mutum don tabbatar da cewar shukra bata wuce ta kowace qofa ba a cikin qofofi guda hudu da akeda su na shiga cikin birnin,Sulhee ce akan layin dubawa,sai masinjan ta a bayanta sai shukra da akayi mata shigar kayan maza,an saka mata kayan tsummokara da kuma tilin kayansu sulhee a goye a bayanta,kasancewar da sulhee ta kasance 'yar rawar masarauta yasa mutane da dama suka santa a garin,haka ma guard din da yake dubasu caraf ya kira sunanta,sai da suka gaisa sannan ta miqa hannu ta karbo name tag din masinjan ta dana shukra wanda tuni aka samo mata mai sunan namiji,guard dinne ya tambaye ta
"Su kuma fa?" Murmushi tayi
"Masinja na ne,da kuma slave (bawa) na" duba nametag din yayi duka ukun sannna ya miqa mata yace
"Ku wuce" sun wuce amma basu kai ga fita daga qofar ba wani guard ya tsayar dasu
"ku dakata!" Guard din da ya duba su ne ya tambayeshi
"Me yasa zaka tsayar dasu?" Ya bashi amsa da
"Wancan yaron ne naga kamar yayi yanayi da yarinyar da muke nema" dukkansu sai da zuciyarsu tayi wani irin bugawa,sulhee cikin murya qasa qasa tace
"Shukra! Ki gudu"
"A'ah ku kuma fah? Idan na gudu ku zasu kama tunda tare suka ganmu" an kawo hoton daidai inda shukra take tsaye kenan suka jiyo muryar jameel
"Me yake faruwa anan ne?" Dukkan guards din suka rusuna domin gaishe dashi,bai bi ta kansu ba saboda mamakin shekarun da ya dauka bai ganta ba
"Sulhee? Ko ba ke bace?" Murmushin da ta san yana narkar da zuciyarsa tayi masa
"My lord!" Ta fada tare da rusunar da kanta,guards din ya kalla
"Ya akayi naga kun tsare su?" Cikin rawar jiki guard din yace
"Ba wani abu bane,kawai sabanin fahimta ne,zasu iya tafiya" jinjina kai jameel yayi sannan ya juyo ya qara kallonta yace
"Zaku iya tafiya" rusunawa tayi cikin murmushi tace
"Thank you my lord!" Girgiza kai yayi
"Babu komai! Nine da godiya da idona ya qara ganinki a wannan lokacin,yanzu akwai abinda zanje yi na gaggawa,amma kizo gida ki ganni tunda kin dawo cikin garin"
"Yes my lord" tace ,wucewa yayi shida mutanen sa,itama suka wuce suna sauke ajiyar zuciya.

Yaune liyafar sericulture da queen jaleela ta hada a cikin garin joshun,kafin tafiyarsu wajen ne da safe ta kira chief maid dinta domin bata wani umarnin sirri,cikin tsoro da tsananin kaduwa chief maid tace
"Your majesty! Ba zan iya ba,ba zan iya abinda kika sani ba! Ta yaya ma kike tunanin zan iya haka?" Fuskar jaleela a daure babu alamun wasa tace
"Ai ba ra'ayinki na tambaya ba! Umarni na baki,kuma kinsan me bijirewa umarni na yake nufi ko?" Runtse ido chief maid tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace
"Amma your majesty..."
"Rufe min baki,kawai ki tabbatar baki yi kuskure ba a cikin abinda na saka ki!"
Takadda ta rubuta ta miqa mata
"Wannan! Ki aika a kaiwa superintendent of police (jaleel) cikin sirri,ke kuma ki shirya mu tafi,bayan ta aika an tafi kaiwa jaleel wasiqar daga bisani suka shirya suka bar cikin palace din domin gabatar da liyafar.

Jikinshi tsuma ya farayi da ya gama karanta abinda yake cikin wasiqar,a sukwane ya taso ya taho cikin palace din,amma sai dai bai samesu ba don sun riga sun tafi.

(Toh fah 🤔 me kuma jaleela take shiryawa a wannan lokacin?)

Dukkan wasu wanda kuka sani a palace suna wajen cikin shigar uniform dinsu,maids dinta,office of investigation,bureu of music,matan hakimai da manyan masu kudin garin,kai kowa ma dai yana wajen kuma akwai rawar da zai taka,ta shirya cikin kayanta da take sawa idan ana wani shagali (ceremonial outfit) anyi mata gyaran gashi kamar rawani mai girma sosai,sai qatuwar alkyabba mai nauyin gaske wacce aka qawata ta da zanen dragon,chief maid dinta da chief sumayya wacce a yanzu itace chief madam ta office of investigation suma suna cikin ceremonial outfit dinne,sun dora alkyabba a kan uniform dinsu sannan kuma anyi musu gyaran gashi suma kamar rawani shigen dai na queen jaleela,tana tafe cikin nutsuwa zuwa wajen inda zata tsaya tayi sericulture din wasu maids dinta suna tattare mata alkyabbar ta baya,a zuciyar ta ta ke cewa
"Yaya Jaleel! Na san baka manta alqawarin da na daukarwa kaina ba ranar da na fara shigowa cikin masarauta,kuma na cika wannan alqawarin na zama sarauniya hakan yasa ba zan taba barin wani ya qwace min matsayin nan ba"
Kamar yadda qa'idar take,chief madam din office of investigation (sumayya) itace take bada duk umarnin abinda za'a gudanar a wajen,su kuma 'yan bureu of music suna bada kida daidai da abinda ake yi
"A fara" sumayya ta fada
Kida aka fara,yayinda jaleela taje tayi abinda ya kamata tayi cike da nishadi (ba sai munyi bayani ba) bayan ta gama sumayya ta bada unarnin an gama,dukkan mutanen da suke wajen suka hada baki tare da maimaita
"Your majesty! Muna miki fatan shekaru dari da daruruwan albarka akan mulkin ki" haka sukai ta maimaitawa amma a wajen Nadeeyah,Basma,Aliya,Afrah,Sameer da manager bai kai zuci ba fa addu'ar.
Yayinda duk mutanen wajen suke yi mata addu'a,ita kuwa a zuciyarta tana cewa
"Yaya! Zanyi duk iya abinda zan iya,ko da kuwa zan sa rayuwata akan layi ne saboda na tabbatar ban rasa wannan matsayin ba"
Bayan haka ne suka dunguma zuwa bangaren da aka ajiye kayan abinci,qaton tebur ne mai daukan mutum goma,suna zaune ita da haj jameela suna fuskantar juna,sai sauran matan hakimai da aka gayyata suma a sauran kujerun,sai dai kujerar jaleela ta fita daban domin kuwa dragon throne ce,kuma abincin ta ma sai da aka dora akan tray yayinda sauran farantai ne kawai akan tebur din,cikin murmushi da nishadi tace musu
"Zamu iya fara cin abincin" dukkansu kowa ya dauki shayi ya fara korawa,nata shayin ta dauko ta gama qare masa kallo sannan ta kai bakinta,chief maid dinta da nusaiba da suke taaye a gefenta suka runtse ido har ta shanye shi tas,ai kuwa bata kai ga ajiye kofin ba ta sume,haj jameela ce ta fara kiran
"Your majesty!" Cikin tashin hankali,haka duk manyan palace maids din suka zo aka fara jijjigata amma ina! Ta suma,kowa hankalinshi a tashe don zai iya shafar duk wanda yazo wajen,daukanta akayi aka mayar da ita palace dinta sannan aka kirawo royal doctor domin ya dubata.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now