Page 27

57 4 0
                                    

Tsayawa tayi tana qara bin ko ina da kallo,a hankali hankalinta ya dawo kan royal guards da suke tsaye a wajen,wannan ma wani qarin tabbacin ne,royal guard din da yake kusa da maimartaba ne ya bawa sauran umarni
"Ku kama wannan yarinyar,zata iya cutar da mai martaba"
"Yea " sauran suka amsa a tare da tahowa don tafiya da shukra,mai martaba ne ya daga hannu,da qarfi yace
"Ku dakata,na santa" jin hakan yasa suka rusuna tare da cewa
"Yhea your majesty" sannan suka koma inda suke a tsaye suka qame,duk abinda akeyi shukra kawai ido take binsu dashi domin tana ganin kamar a mafarki duk abubuwan suke faruwa,sojojin china da suka biyota ne suka taho daidai gaban mai martaba suka rusuna,babban su wanda shine yake gaba,sauran sun tsaya a bayanshi ne yace
"Mai martaba ka gafarceni,zan tafi da wannan palace maid din,domin lady investigator ce ta shigo quaters dinmu domin wani dalili nata" yana gama fadar haka,ya bada umarnin a kama ta a tafi da ita
"Ku dakata nace" mai martaba ya fada cikin tsawa,har sai da shukra ta daga ido ta kalle shi,royal guard din da yake kusa dashi shi kuma ya daka mata tsawa
"How dare you? Kike kallon mai martaba ido cikin ido" da sauri tayi qasa da kanta,tare da ranqwafar da wuyanta,chief eunuch da yake tsaye duk yaji babu dadi domin ya san mai martaba ma don babu yadda zaiyi ne,gyaran murya mai martaba yayi
"Yanzu a gabana ina tsaye zakuyi arresting palace maid dina? Tunda palace maid din masarautar mu ce,ku barmu domin muyi binciken abinda ya kaita wajen,kuma zamu hukuntata yadda ya kamata idan mun kama ta da laifi" rusunar da kai sukayi tare da bashi haquri,alama yayiwa police officers din da suke tsaye a bayanshi,da hanzari suka matso kusa,yace
"Ku tafi da ita" shukra da har yanzu take jin kamar babu jini a jikinta ta fara tafiya,'yan sandan suka sata a gaba,suna tafiya tana waiwayen mai martaba har suka bar wajen.

Manager da yaji labarin sojojin china suna bin lady investigator da gudu ya rikice sosai ya shiga tashin hankali,sameer ne ya taho wajenshi da gudu,manager yacewa sameer
"Me ya sami shukra? Sun kama ta?" Cikin alhini sameer yace
"Basu kamata ba amma an tafi da ita police bureu" juyawar da sameer zaiyi ya hango mai martaba a tsaye a inda shukra ta barsu,nuna wajen sameer yayi tare da cewa manager
"Yallabai wancan kamar dan sandan sirrin nan ko? Ka ganshi" manager da ya juyo shima yana kallon mai martaba yace
"Kai ba shi bane,wannan mai martaba ne" sameer ya kalli manager
"Mai martaba kuma?"
"Ehh mai martaba ne,ba kaga alkyabbar sa ba,dragon robe ne a jikinshi " manager ya fada yana qara nunawa sameer inda mai martaba yake tsaye,daidai lokacin da ya juya baya ya bar wajen,jinjina kai sameer yayi
"Tabbas dragon robe ce a jikinshi,mai martaba ne,ka san ni ban taba ganin shi a kusa kusa haka ba,amma abin bai baka mamaki ba? Kamar su tayi yawa sosai" haka dai suka cigaba da alhinin tsananin kamar da mai martaba yakeyi da abokinsu dan sandan sirri.

Mai martaba suna fitowa daga wajen ya tsaya ya daina tafiya,ganin haka chief eunuch yace
"Your majesty ya za'a yi da shukra?" Mai martaba da damuwa ta cika fuskar shi ya ce
"A kirawo police IG,na tabbata tana da qwaqqwarar hujjar da yasa ta shigo wajen nan"
"Yea your majesty " chief eunuch ya bashi amsa,wucewa yayi domin komawa palace.

A office of investigation,'yan matan suna zaune gaba dayansu Aliya ta shigo da saurinta
"Wai da gaske ne abinda nake ji shukra ta samo hujja mai muhimmanci?" Rukayya ce ta bata amsa
"Ehh da gaske ne,an ce wasu kalmomi ne na china kuma ba kowa yake iya gane me suke nufi ba" Afrah da take zaune tace
"Lahh abinda shukra ta nuna min,nace ta mayar basu da amfani" sameerah ce ta kalli Afrah
"Lallai ta qara takar sa'a kenan" Afrah ta miqe tsaye
"Ta yaya zaki ce ta taki sa'a,taga abu mara ma'ana,ni banyi tunanin zai iya zama wani abu ba,amma ita ta dage har sai da ta fitar da abu mai ma'ana a ciki,kuma kice sa'a ce?" Shiru Sameerah tayi,Afrah ta cigaba
"Wannan halin naku shi zai kaiku ya baro,wai ta taki sa'a saboda kawai ba zaku iya yaba mata akan qoqarin da tayi ba" kowa tsit yayi a wajen don kuwa gaskiya Afrah ta fada,baqin ciki kawai sukeyi.

A office din director kuwa,lady sumayya ce cikin bacin rai take fadawa director
"Yarinyar nan fa yin kanta tayi ba tare da izinin kowa ba,ko da ta samu abu mai muhimmanci amma mu bai kamata ace mun zuba ido ba,ya kamata a hukunta ta domin tayi gaban kanta...." basma ce ta katseta
"Duk da gaban kanta tayi amma ta cece mu ne gaba dayanmu daga abinda zaije ya dawo idan labari ya jewa sarkin china cewar an tura ladies investigators a matsayin ladies-in-waiting domin suyi binciken qarqashin qasa,yanzu kuwa ana samun hujja a kan wanda ake tuhuma ai komai ya qare,kuma muma mun tsira daga mu har mai martaba"  harara sumayya ta aika mata,basma ta sunkuyar da kanta,director ce tace
"Yanzu ina yarinyar take"
"Naga kamar bata cikin nutsuwarta,shiyasa nace taje ta huta" nadeeya ta bata amsa.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now