Page 4

92 6 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤

                  ROYAL CONSORT
Korean inspired novel

         ©️ marriam mayshanu.... ✍️

Page 4

Washegari tun da sassafe chief eunuch ya turo mutane bureau of music domin a nemowa mai martaba gwanin busa algaita,yayin da shukrah tana can ta dauki hanyar shiga cikin gida domin zuwa taya bayin ciki aiki,hankali a tashe manager yake nemanta,hanyar fita daga wajen ya nufa,nan take ya hango bayanta tana tafiya hanyar shiga cikin gida,da sassarfa ya qarasa wajenta,yayi qasa da murya yace
"Ina kika shiga tun dazu ina nemanki? " zaro ido tayi tana kallonshi don yanayin da yayi magana ya tabbatar mata ba lapiya ba,tace
"Ranka ya dade lapiya kuwa? Dama da ina fitowa naga dogarai suna shiga cikin ma'aikatar mu,Allah yasa ba wani laifin mukayi ba"
Kallonta yayi cikin damuwa yace
"Ai ke suka zo nema,mai martaba yaji busa algaitar ki jiya da dare,shine ya turosu su nemo wanda yayi busar" ya dan nisa sannan ya cigaba "Ban san ya zanyi ba idan suka san servant girl ce take amfani da kayan kidan masarauta,kashi na ya bushe" ya fada cikin damuwa,sameer ne ya qaraso wajen da qullin kaya a hannun sa,manager ya juya kalleshi tare da cewa
"Yauwa sameer kawo kayan nan" ya fada yana karbar kayan daga hannun sameer,tare da miqawa shukra yace
"Ga kaya nan,ki tafi can maqera da take wajen masarautar nan,suna buqatar mai taimaka musu da aiki kafin a gama nemanki sai ki dawo" rau rau tayi ido kamar zatayi kuka tare da cewa
"Amma ranka ya dade yanzu fa cikin gida zan shiga in taya su aiki,ai babu wanda zai gane ni"
"Kiyi maza ki fice daga nan ki tafi inda nace miki yanzunnan kafin ranki ya baci,ni zaki janyo wa masifa ace ina barin servants suna amfani da kayan masarauta? Maza ki wuce" ya fada mata a fadace tare da nuna mata hanya,sameer ne yace mata
"Kiyi haquri wani lokacin sai kije ki taya su aikin,amma yanzun tafiyar ki ita tafi muhimmanci saboda kada dogaran sarki su gane ki" gyada kai tayi fuskarta abin tausayi tare da juyawa ta bar wajen.

A cikin fada kuwa ana ta shirye shiryen dawowar jalila cikin masarautar,musamman uban gayyan mai martaba,yana zaune cheif eunuch ya shigo ya gaishe da mai martaba tare da cewa "Ranka ya dade ba'a samu mai kidan algatar ba,mun tambayi kowa amma basu gane waye yayi kidan jiya ba" cikin mamaki mai martaba yace
"Ikon Allah,amma kaima kaji kidan jiya ko? Da ni kadai naji sai nace gizo kunnuwa na suke yi min" murmushi chief eunuch yayi,mai martaba ya qara da cewa
"Dama ina son ko waye yazo yayi wa jalila ranar da zata shigo,domin tana son kidan algaita,kuma ina shirin tana shigowa zan bata matsayin CONSORT domin hakan zai qara qarfafa hakiman kudu sosai,domin ita din daya ce daga cikin ahalinsu" shi dai chief eunuch murmushi kawai yake yi,domin ya dade bai ga mai martaba a cikin farin ciki irin wannan ba.

A bangaren jalilah itama nata shirye shiryen yayi nisa,tana kuma cikin matuqar farin cikin komawa cikin fada domin tasan hakan yana nufin aure tsakanin ta da mai martaba abin qaunar ta,amma akwai abinda ko yaushe ta tuna sai hankalinta yayi matuqar tashi,wani bawan Allah da bata san waye shi ba tun shekaru bakwai da suka wuce ya fada mata abinda ko da yaushe idan ta tuna annurin fuskarta yake daukewa ta shiga cikin damuwa da rudewa,amma duk wannan ba zai mata magani ba,dole ta jira rayuwa ta gasgata ko kuma ta qaryata mata abinda mutumin nan ya sanar da ita.
Miqewa tayi ta dauko wani dan qaramin akwati,bashi da fadi sosai sai tsayi,budewa tayi nan take keyholder ya bayyana,irin wanda shukra take da zanen shi a hannunta,daukowa tayi ta riqeshi a hannunta tana dubawa a hankali tace
"Wannan abin shine mafi soyuwar kyauta a gareni,shine shaidar soyayya ta da maimartaba,ko da yaushe ririta shi nakeyi ina kaffa kaffa dashi amma gashi ya fara tsufa" ita kadai take fadawa kanta hakan,daga bisani ta miqe,ta dauki wata alkyabba plain ta saka a jikinta ta fito,kai tsaye maqera ta tafi da keyholdern ta a hannunta.

Tana shigowa maqerar duk ma'aikacin da ya ganta a hanya sai ya tsaya ya dan risinar da kanshi alamar gaisuwa,sannan ya wuce,kai tsaye wajen shugaban maqeran ta tafi,kanta tsaye ta shiga cikin office dinshi yana zaune,dago kai yayi yaga lady jalila ce,da sauri ya tashi daga inda yake yazo gabanta ya rusunar da kanshi tare da cewa
"Barka da zuwa my lady" murmushi tayi ba tare da ta amsa ba,taje kan kujerar da ya tashi ta zauna,har yanzu yana tsaye kanshi a qasa,ya qara rusunawa yace
"Wane irin taimako zan miki my lady?" Cikin qasaita ta kalleshi tare da cewa "Abin muqulli na ne ya tsufa nazo a sabunta min shi" ta fada tana miqa masa keyholder dinta tare da ajiye shi kan tebur din dake gabanta,cikin rawar jiki ya dago kanshi ya dauki keyholder din tare da cewa "At your service My lady" sannan ya juya ya fita,dawowa yayi da takadda sai kuma brush (kamar brush din da masu kwalliya suke amfani dashi,domin a wancan zamanin babu biro,ink ne ake narkawa sai a sa brush ayi rubutu) yana shigowa kanshi a qasa yazo daidai tebur din da jalila take,ya qara rusunawa tare da cewa "With your permission my lady" wato yana son ya zauna ne,amma sai da izinin ta,ba tare da ta kalli inda yake ba ta bashi amsa "Zaka iya zama" dan qarasowa yayi yaja kujerar da take kallon tata,amma sai ya mayar da ita gefe kadan sannan ya zauna,a hankali ya fara zanen keyholdern da ta kawo,tana zaune tana kallon me yake yi har ya gama zanenshi tas,zanen ya fito sak iri daya da wanda shukra take dashi a hannunta,tashi yayi domin tafiya can bangaren masu aikin sassaqa katako ya kai musu domin su yanka irinshi kuma suyi masa paint kalar maroon kamar yadda ya zana.
Cikin abinda bai wuce minti talatin ba aka gama mata komai aka kawo mata sabon da tsohon keyholder dinta,ta tashi ta bar wajen.
Shukrah kuwa tana can tana ta aikin ta a wani waje da suke hada wani abu da farin dutse,farin dutse ne ake fasa shi sai ayi masa wani shape cikin gwanancewa domin yana da matuqar amfani wajen fitar da sautin kid'a,ji tayi an bude qofar wajen a hankali an shigo cikin sanda,dago kanta tayi don taga waye mai shigowar,wani ma'aikacin su ta gani,shi har yanzu bai kula da mutum a wajen ba,a hankali cikin sanda yake tafiya yana kalle kalle,sai da yazo dab da ita yana ta kallon baya,juyowar da zaiyi ya ganta sai ya zabura,zare ido yayi tare da cewa "kin tsorata ni sosai,me kike a nan" cikin sakarcin ta tace masa "aiki aka saka ni nayi polish din wadannan duwatsun" murmushi yayi yace mata "yi tafiyarki kawai zan qarasa" zaro ido tayi tace masa "an ce fa na gama kafin 5 na yamma" dan sassauta murya yayi yace mata "Ehh kiyi tafiyar ki,kinga tunda na fiki iyawa ma ai zan fiki saurin gamawa" tana jin haka cikin murna kuwa ta fito,fitowar ta kenan manager ya hango ta,da hannu yai mata alamar tazo,ta qaraso gabanshi ta rusunar da kanta qasa tare da cewa "barka da yamma my lord" murmushi yayi tare da cewa "kema sannunki,ga takaddun zanen aikin da akayi yau,ki dauka kije rijiyar da ake hada wuta ki zuba su a qona" qara rusunawa tayi tare da cewa "Yes my lord" sannan ta wuce da sauri ta shiga office din,takaddun ta gani a cikin wani bakitin qarfe,ta dauko ta nufi hanyar rijiyar dasu,zuwanta ke da wuya ta fara zazzage su tana kawar da fuskarta saboda hayaqi,sai da ta gama zazzage su tas sannan ta juya tana kallon yadda suke qonewa,wata takadda ta hango da maroon din kala,da sauri ta sa hannu ta zaro gefen da bai fara qonewa ba na takaddar,a qasa ta ajiye ta ta fara tattake inda wuta take ci,nan da nan wutar ta mutu ta qara daukowa tana kallo,sak irin zanen da yake hannunta,dan yatsan ta ta saka ta lakuto ink 🖋️ din da akayi zanen dashi,ta ga danyen ink ne ko gama bushewa baiyi ba,ai da gudu ta bar wajen zuwa inda kayanta suke,waccar takaddar ta hannuta ta dauko ta hada su taga babu bambanci,ta qara fitowa a gigice sai wajen masu sassaqa katako,nuna musu abin tayi wani ma'aikacin wajen yace mata "Wanda yayi aikin ya tafi garinsu yau,sai wani satin zai dawo aiki" fitowa tayi ta nufi office din manager,tana haki ta shiga tare da cewa "My lord Dn Allah wannan zanen na abin muqulli waye ya kawo shi" kallonta yake cike da mamakin dalilin da ya sata wannan gudun,kawai dai ya bata amsa "Na wata court lady ce ta kawo akayi mata sabo" runtse ido tayi gam cikin takaici,ya qara ce mata "me yasa kike tambaya?" juyawa kawai tayi ta bar office din ba tare da ta ce mai komai ba.
Dakin da aka bata ta koma ta zauna,da zanen duka guda biyun tana kallon su qwalla na cikowa a idonta,a zuciyarta take fadan
"Yanzu shekara bakwai kenan da rasuwar babana da yayana amma na kasa yin komai cikin tsawon shekarun,ga dama na gani yau amma ta kufce min,naso zuwa cikin fada na taya su aiki amma shima na kasa samun damar" ta sunkuyar da kanta haqaye na zuba a idonta ba tare da ta samu damar share su ba.

"Shukrah,Shukrah " taji ana qwala mata kira,
Muryar sameer ne,da sauri tasa hannu ta goge idonta,ta dan saisaita kanta,shigowa yayi ya tarar da ita zaune a qasa da takaddu biyu a hannunta,zama yayi shima tare da duba abinda ke hannunta,kallon yanayin ta yayi,yace "kinzo nan babu mai kula da ke kika shigo nan kina aikin kukan ko? To ki shirya mu tafi yanzu" wata qwallar ce ta zubo mata ba tare da ta sani ba,kafin tace komai sameer ya qara cewa "A ina kika samo irin wannan zanen da kike dashi kuma?" Share hawayen tayi
"A nan wata court lady tazo aka yi mata irin shi" ta fada a taqaice,cikin murmushi yace mata "kin hadu da ita kenan? Itace wacce kike nema ko? Kin samu abinda kike buqata a wajenta?" Duk ya jero mata tambayoyin,kwabe fuska tayi tace "Ni ban ganta ba,mai aikin sassaqa katakon kuma ya tafi,manager ne ya fada min na wata court lady ne" sameer yai saurin cewa "meyasa shi managern baki tambaye shi wacece ba? "
Tace "ba zai san wacece ba tunda bashi yake yi ba,wanda yakeyi din kuma lokacin da na ga abin ya riga ya tashi kuma sai wani satin zai dawo aiki,kaga kuwa ba zan samu sanin wacece ba" gyada kai sameer yayi sannan yace mata "kiyi haquri yanzu ki tashi mu tafi ko?" Ba tare da tace masa komai ba ta miqe ta hada sauran kayanta ta qulle a abinda tazo dashi ta fito suka tafi.

A bangaren jalila kuwa tana komawa gida (tana zaune ne a wajen mariqin ta,minister na tribunal) ta tarar dasu suna magana a farfajiyar gidan minister da babban danshi mai suna jameel kamar cikin rashin nutsuwa,qarasawa tayi kusa dasu tare da cewa "lafiya kuwa na ganku haka? Ko wani abin ne ya faru a gidan?"
Juyowa sukai a tare gaba dayansu suka kalleta,jameel ne ya ce mata "mun fahimci kamar dowager queen tana da wani qulli da ta shirya ranar da zaki shiga cikin masarauta" cikin rashin fahimta tace "me kake nufi da haka?"
"Ta shiryawa young prince(qaramin qanin mai martaba ne) taron murnar zagayowar haihuwar sa,kasancewar shi dan consort din da tafi tsana ne yasa bata taba bashi muhimmanci irin wannan ba,shiyasa muke tunanin akwai wani abu da take shiryawa,kuma ko menene yana da alaqa da ma'aikatar kida(bureu of music)"
Jinjina kai tayi cikin zurfin tunani ba tare da tace komai ba,jameel ya qara cewa " ko zaki canza ranar ki qara ko kwana biyu ne saboda mu kaucewa ko ma me suke qullawa" girgiza kai tayi tace "A'ah bana son na kaucewa ko me suke qullawa,domin idan na kauce dole zasu qara qulla wani,a zaman da nayi a baya a masarautar na san yadda komai yake gudana,idan baka iya siyasa ba,ba zaka iya rayuwa ba saboda haka daidai nake da ita"
Sai a lokacin hakimi ya ce "Wannan haka yake jalilah,shiyasa na san duk inda zaki shiga ba zaki bani kunya ba".

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now