Page 33

88 9 0
                                    

Page 33

Zazzaune suke a cikin office din da ya kasance nasu,kayan duk da suka kwaso ne daga quaters din ladies in waiting a kan tebur,ruqayya tana qirga su,yayinda afrah take riqe da littafi da brush din rubutu,sameerah ce cikin damuwa take ce musu
"Yanzu duk satin nan kawai aikin binciken cikin masarautar nan zamuyi,gaskiya sai mun kusa mutuwa kafin mu iya bincika ko ina da ina a cikin masarautar nan" babu wanda ya kulata,sai shukra ce tace
"Ban sani ba ko a cikin ku akwai wacce taga wani keychain na butterfly?" Afrah ce ta ajiye rubutun da takeyi ta dago idonta ta kalli shukra
"Ni dai ban gani ba,amma tunda muka fara binciken nan sai kin tambaya,me yasa kike neman shi?" Girgiza kai shukra tayi cikin sanyin murya ta e
"A'ah ba komai,kawai dai na taba ganinshi can da dadewa"  sulalewa tayi ta fita ta bar su suna aikin.

Tana tafiyarta a hankali har ta isa gidan sameer,inda ta tarar da abdullahi a zaune,ganinta yasa ya miqe tsaye da murmushi a fuskar sa,gaisawa sukai cikin kulawa yace mata
"Kin ce min kuna ta aikin cikin satin nan,fita zatayi miki wahala" murmushi ta mayar masa,tare da amsa
"Ehh aike ne akayi min wajen masarauta,shine na biyo na ganka" cikin nutsuwa yake kallon yanayinta kafin daga bisani ya tambayeta
"Na ga yanayinki wani iri,wani abu yana damunki ne?" Shiru tayi ta sunkuyar da kai,yace
"Mu shiga ciki" dakin shi suka shiga,suka zauna sannan ta fara fada masa damuwarta,sai da ta gama tsaf yace mata
"Wato har yanzu kina nan kina neman wannan keychain din? Me yasa ba zaki haqura ba? Ki barni zan ji da komai" girgiza kai tayi
"A 'ah Yaya,ina burin in samo wanda sukai sanadin mutuwar babana da yayana akan laifin da ba nasu ba,har yanzu ina kallonsu a idona,lokacin da aka dinga zagaya gari dasu kowa yana kallonsu a matsayin 'yan ta'adda" ta qarasa qwalla tana cika mata ido,cikin sigar rarrashi yace mata
"Kiyi haquri,amma hakan yana da hatsari a gareki tunda kina cikin masarauta,idan har aka gane ke 'yar chief ce da suka dade suna nema,kuma sukai zaton kin mutu,akwai matsala" girgiza kai tayi
"A'ah Yaya ba zasu gane ba,wannan shine dalilin da yasa na shiga masarauta tun ina qarama,shine dalilin da yasa na koma shukra a maimakon shukriyya da ake kirana da shi,shin kasan yadda na rayu a tsawon shekaru shida kafin ka dawo gareni? Har yanzu ina mafarkin tsaunin da jinin mahaifina,da yayana,da sauran abokanka yake kwaranyowa akai,duk tsawon shekarun nan ban taba mantawa da su ba ko daidai da rana daya" Abdullahi baice mata komai ba,sai kallon tausayi da ya bita dashi,ajiyar zuciya ta sauke,ta canza yanayi daga karaya zuwa dakewa tace
"Ni yanzu lady investigator ce! Zan iya yin hakan,ka taimaka ka daina cemin in dakata ko kuma ba zan iya ba"

Royal noble Consort jaleelah da a yanzu an canja mata quaters tunda aka bata matsayin consort lokacin da take da ciki,bayan haihuwar danta kuma aka qara mata matsayi zuwa ROYAL NOBLE CONSORT,yanzu ta qara kusanci da cikin gida,aka bata quaters daga cikin wanda suke da kusanci da na queen haneefa,tana zaune riqe da dan jariri cikin shigarta ta royal noble consorts,alkyabbar ta mai zanen ado ce a wuya,sabanin da wacce take sawa da take plain,sai 'yan fulawoyi a saman kafadar da wasu a qasan skirt dinta wanda lokacin da take consort babu su,hakanan head band dinta da hairpin dinta duk an sauya mata su zuwa wanda suka fi wancan wanda take sawa ado da tsaruwa,yayinda chief maid dinta take zaune a gefen ta,jaleel ya shigo,cikin farin ciki take jijjiga yaron tare da yiwa yayanta sannu da zuwa,qoqarin zama yake ya amsa mata da
"Greetings,Your highness" cikin murmushi take ce masa
"Barka da zuwa yaya,congratulations naji labarin an qara maka matsayi zuwa Left Chief of police" cikin murmushi ya kalli yaron da yake hannunta
"Nagode sosai your highness,ai godiyar tawa zuwa ga prince ne,domin dalilinsa ne darajar mu ta dagu a qasar nan" cikin murmushi tace
"Bari in miqo maka shi ko?" Hannunsa ya miqa ya dan bude shawul din da yaron yake ya kalli fuskar sa
"lafiyayyen nephew dina,kuma da na fari a wajen mai martaba sarki ya'aqub Naoufal,lallai ya cancanta da zama yarima mai jiran gado" rarraba ido jaleela tayi tana nuna masa chief maid dinta da take zaune tare da cewa
"Yaya!!!" Cikin shagwababbiyar murya,murmushi yayi
"Ai ko chief maid ma ta yadda da abinda na fada,ko ba haka ba?" Murmushi tayi itama ta sunkuyar da kanta qasa
"Ehh haka ne,yallabai" jaleela ce ta kalleta tace
"Bamu waje ko?" Cikin ladabi ta tashi tare da miqa hannu ta karbi yaron a hannun jaleela ta fita,hankalinta gaba daya ta mayar kan jaleel tare da tambayar sa
"Shin kaje wajen tribunal minister kuwa kun tattauna?" Jinjina kai yayi
"Ehh naje your highness,dukkan hakiman kudu sun shirya tsaf suna ingiza mai martaba akan ya nada yarima mai jiran gado,amma queen dowager taqi amincewa,kuma hakiman arewa suna bayanta akan hakan" yanayin fuskar jaleela ne ya canja,cikin dakewa tace
"Ai dama na san zata bamu matsala,amma ai ba zata ja da dokar qasa ba,domin a doka ai babban da shi yake gadon sarauta" jinjina kai jaleel yayi
"Hakane,kin san tsohuwar guzumar nan tana amfani da rashin lafiyar tane tana juya mai martaba,shiyasa ya kasa yin komai har yanzu,tunda kika haihu yayi miki nadin sarautar ki ta ROYAL NOBLE CONSORT amma yayi biris da nada CROWN PRINCE" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da tambayar sa
"Yanzu yaya jikin queen dowager din?"
"Bana tunanin zata mutu nan kusa,kada kiyi tunanin nasarar ki tana kusa,amma idan mai martaba ya nada wata consort din kamar yadda ta buqata (wato ya qara aure) toh lallai zamu shiga mawuyacin hali" jaleel ya bata amsa
Ajiyar zuciya kawai take saukewa domin ita dai bata gano mafita ba a wannan halin da suke ciki,tashi yayi ya fita ya barta zaune tana tunani,yana fita waje ya tsaya a gaban maids din da suke tsaye,bayan chief maid,akwai lady in waiting din jaleela ta yadda da ita sosai,kuma tafi kusanci da ita sunanta Nusaiba kallon kallo suke ita da jaleel,wata alama yayi mata da ido,itama ta amsa masa,sannan ya wuce ya bar wajen.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now