Part 3: The lady investigator

66 4 0
                                    

Page 21
❤️  Part 3:The  lady investigator

A bureu of music shukra ta kasa tsaye ta kasa zaune domin tana tsoron kada zuwa wajen queen haneefa yasa ta yadda da buqatar 'yan office of investigation na qin karɓarta,har sai da manager yazo yace mata ai basuyi nasara ba kuma queen haneefa ta bayar da cikakkiyar amincewarta,sai sannan ta saki jiki sosai su sameer suna ta tsokanarta suna ce mata "Maa-Maa-nemm! (My lady)" tana cewa su daina fada,sameer ne yace

"Chab rufa mana asiri mu ai yanzu bamu isa mu kira ki da shukra ba,bari ma ki gani" nan da nan yaja baya ya hada hannayensa a kan cikinsa,ya rusunar da kanshi qasa tare da cewa

"Maa-maa-neem!" haka duk sauran mutanen da suke wajen suma sukayi,dariya ya bawa shukra,haka ma sauran mutanen wajen kowa yana cikin farin ciki.

A halin yanzu matsayin shukra ya zarce kowa a bureu of music har manager,saboda haka yanzu babu wanda zai qara kiranta da sunanta,sai sun girmamata da my lady.

Manager ne yake tahowa inda suke da wasu ma'aikata a bayanshi dauke da tebur din abinci masu yawa,haka suka zo suna ta jerawa,shukra tace

"Yallabai wannan na menene?" Kafin manager ya bata amsa sameer yace

"haba shukra,ba kya gani walima zamuyi" da sauri ya rufe bakinsa, "ina nufin my lady" juyawa tai ta kalli manager hawaye ya cika a idonta,jinjina mata kai yayi cike da farin ciki shima idonshi ya cika da ruwa,wataqila wannan shine zamansu na qarshe don zata bar wajen kenan har abada,haka suka zazzauna kowa ya fara cin abinci,kowa cikin farin ciki gwanin sha'awa.

A police bureu suma IG ne sai lieutenant da assistant suke hirar shukra,a lokacin ne ake hirar yadda aka kai mata official decree of appointment harda cikakken sunanta Shukra Anas malak,jin haka yasa IG fadawa tunani shekaru takwas da suka wuce,kamar yasan wata qaramar yarinya mai irin wannan sunan,amma ita waccan SHUKRIYYA ANAS MALEEK ne sunanta,ya kwashe shekaru kusan hudu yana nemanta daga baya ya haqura,amma ya za'a yi ta kasance a cikin masarauta,kuma baiwa? maganar assistant lieutenant ce ta katse masa tunaninsa

"Yallabai,kana da baqo a waje,wani shashashan yaro yazo nemanka"

Tashi IG yayi tare da fitowa waje domin ganin me neman shi,tsayawa yayi yana kallon yadda jaleel yake shashanci da masu gadin wajen cikin uniform dinshi na 'yan sanda,da rank din lieutenant,har bai ma kula da isowarshi wajen ba,cikin rashin daraja suka gaisa,IG ya bashi warning akan cewar idan yana da hankali da iya aiki zasu zauna lapia domin an kawo shi ne ba akan qa'ida ba,alfarmar minister of tribunal ne,kuma matsayin lieutenant aka bashi daga sama,IG ne ya kalli assistant lieutenant yace

"Ya fika matsayi a rank amma ka fishi matsayi a sanin makamar aiki,saboda haka ka kula da training dinshi" yana gama fadar haka yayi gaba ya barsu,assistant lieutenant yana yiwa jaleel magana amma ko kula shi baiyi ba ya fara tafiya yana zagaye wajen,abdullahi ne ya bullo shi da wani dan sanda da littattafai a hannunsa,abdullahi cikin girmamawa yace

"Yallabai ko zaka bani litattafan sai naje na ajiyesu a inda ake ajiyewa" kallon abdullahi yayi yace

"Zaka iya jerasu kuwa?" Dariya yayyi

"Zan iya yallabai,duk da ban iya karatu ba amma zan iya gane harufan da zan jera" miqa masa littattafan yayi tare da cewa

"Ka taimakeni kuwa abdullahi domin ina da abubuwan yi da yawa" abdullahi juyawa yayi ya nufi inda suke ajiye litattafan su,da sauri ya ajiye wanda ya shigo dasu ya fara dudduba sauran wanda suke wajen cikin sauri domin kada wani ya shigo ya tarar da shi yana bincike,magana kawai yaji a kanshi

"Sannu da aiki ko?" A razane ya dago kanshi,jaleel yace

"A ah kada ka damu,cigaba da abinda kake yi,nima ai ka taimakeni a baya ko?"  hannu jaleel ya kai kan littafin da abdullahi ya bude,a fili ya karanta

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now