Page 26

59 3 0
                                    

Page 26

Afrah ce tsaye itada shukra a bayan dakin baqin,cikin qaramar murya afrah ta miqowa shukra wata takadda
"Karbi wannan shukra,maganganunsu ne kiyi maza ki kaiwa lady nadeeya,ko za'a samu wani abu mai muhimmanci a ciki" karbar takaddar shukra tayi z
"Amma afrah kina jin yaren chineese ne har kika iya fahimtar maganganun su?" Murmushi tayi mata tare da cewa
"Ina ji kadan kadan" sallama sukayi,shukra ta tafi office of investigation kai saqon takaddar.

Washegari da safe dukkan baqin da akayi suka tafi gaisawa da mai martaba domin cin abinci na musamman,hakan ne ya bawa su shukra damar bincike a cikin dakunan da aka sauke baqin,babu wanda ya samo komai,sai shukra da ta samu wani rubutun kalmomin chineese a wata siririyar takadda kuma anyi rubutun ne a tsaye,yayinda fadin taddar zai iya daukan kalma daya ne kawai tak,Zuwa tayi ta nuna wa afrah,afrah ta karanta da yake tana fahimtar yaren chineese amma babu ma'ana,kawai wani surkullen rubutu ne mara ma'ana,hakan yasa sukayi shawara da shukra akan ta mayar da takaddar domin bata da amfani,hakan kuwa akayi ta mayar ta ajiye a inda ta dauko.

A ranar bayan baqi sun dawo daga wajen mai martaba ne kawai suka tara 'yan matan tare da bincike quaters dinsu tas,mudubi suka samu 'yan qanana a cikin kayan kowaccen su,hakan ya tabbatar musu da cewar investigators ne,nan da nan labari ya cika masarautar cewar an aikawa baqin sarkin china investigators saboda ba'a yadda dasu ba,kuma matuqar maganar taje kunnen sarkin china toh qasar JOSHUN zata ahiga cikin tashin hankali,domin qasar tana qarqashin mulkin mallakar china ne,abubuwa da dama basa yiwuwa sai da sahalewar
Masarautar china,haka kuma suna da damar sauke ko dora wanda suka ga dama akan mulki,hakan yasa ake yi musu biyayya sosai.

Da labari yaje wajen IG da hanzari ya taho zuwa quaters din masaukin baqi,jameel ya tarar a wajen wanda shine director na tribunal,cikin tashin hankali yake tambayar jameel
"Ya akayi suka gane yaran nan? Kuma wane hali yaran suke ciki?" Jameel cikin halin ko in kula yace
"A halin yanzu bamu da tabbacin komai" takowa IG ya fara yi domin shiga wajen,jameel ya tare shi
"Kasan idan wakilin sarkin china ya san cewar ana binciken nan ne tare da police bureu da kuma tribunal to tashin hankalin da qasar nan zata shiga sai yafi na yanzu,domin yanzu Office of investigation kawai aka sani a cikin lamarin nan,to shigar mu ba zai haifar da da mai ido ba" lura da cewar maganar jameel gaskiya ce,yasa IG dakatawa daga shiga wajen,juyawa yayi domin zuwa wajen mai martaba,wata qila su samu mafita.

Washegari da safe,su nadeeya suna office suna alhini tare da tunanin halin da yaransu suke ciki,suka ga shigowar su shukra,su 8 reras 'yan china sun sako su,domin a cewar su ba zasu hukunta yaran ba,kawai dai zasu koma garinsu ne a ranar ba tare da sun gama abinda ya kawo su ba,domin dama a qa'ida duk shekara suke zuwa masarautun da suke qarqashin ikonsu domin qarfafa alaqa da kuma tattauna cigaba,hakan ne ya tayar wa mai martaba hankali matuqa domin hakan zai bada matsala a tattalin arziqin qasar,hakan yasa ya shirya tsaf domin zuwa har inda suke a quaters dinsu ya samesu,ya amsa laifin da sukayi kuma ya basu haquri,tare da umartar 'yan bureu of music da su shirya domin zuwa nishadantar da baqin tare da mai martaba.

A yayinda a office of investigation kowa yake alhinin abinda ya faru dasu,domin binciken ya lalace kenan,kuma ba za'a samu abinda ake so ba tunda an riga an gano su,shukra kuwa babu abinda yake ranta sai wannan takardar da ta gani,ita dai zuciyarta tana ta bata cewar akwai wani abu mai muhimmanci ga bincikensu a cikin takaddar,amma kuma rubutun sam bashi da ma'ana,tana zaune ita kadai tana tunani,kawai wani tunanin ya fado mata,da gudu ta tashi ta nufi police bureu wajen abdullahi,tana shiga da gudu taci sa'a kuwa dab da yana fitowa daga office din lieutenant,hakan ya sa ya jawo ta zuwa office din da suke zama,cikin nutsuwa shukra tayi masa bayanin abinda ta gani,sai da ta gama bayaninta tsaf,sannan yace mata
"Tsaya mu gani" tashi yayi yaje ya dauko takadda,ya yanka ta a tsaye sannan ya dauko wani dogon katako mulmulalle ya nade takaddar a jiki,iya inda ya nado ta gabanshi ya dauko brush din rubutu tare da fara rubutu daki daki,daga sama zuwa qasa,duk layi daya kalma daya,sai da ya gama tsaf sannan ya warware,sai ya kasance rubutun akwai space sosai tsakanin kalma da kalma,sai kawai ya cike space din da duk kalmar da tazo masa kansa,sai da ya hama tsaf ya daga takaddar ya nunawa shukra
"Kamar haka takaddar take?" Saurin daga kai shukra tayi
"Sak kuwa yayana,sak haka take,shin me hakan yake nufi?"
Mulmulallen katakon ya dauko,ya qara nade takaddar a jiki tare da cewa
"Kina ganin wannan katakon ko? To dashi kadai ake iya karanta irin wannan wasiqar sirrin,kinga idan kika nada gaba,kika nadoshi ta baya,tunda takaddar siririya ce,zata nannade gaba daya a jikin katakon ne,to idan kika gama,zaki ga kalmomin da suka bayyana a gaba,ki bar na bayan katakon,idan kika karanta zakiga sun bada ma'ana" ai shukra sosai ta fahimta,ba tare da ta tsaya yi masa bayani ba ta fita da gudu,direct ta wuce bureu of music,manager ta samu tare da roqonshi ya barta taje tare da su,tunda mai martaba ya gayyacesu,zatayi shiga kamar yadda take baiwa a da,domin akwai abinda ya kamata tayi,kuma babu hanyar da zata iya shiga wajen sai da taimakon shi
"Abin da kamar wuya shukra,me zai hana kije ki sanar da manyanki a office of investigation?" Manager ya tambayeta
"Haba manager,masifar da suke ciki ma,da muka zama silar lalacewar binciken nan ai ta isa haka,babu wanda zai qara kasada da rayuwarsa da matsayinsa akan abinda bani da tabbas akai,nu dai ka taimaka min ka shiga dani" shukra tayi masa bayani game da qara roqonsa,
da qyar ta samu ya yadda zai tafi da ita amma sai tayi taka tsan tsan,don yasan ko bai barta ta bishi ba sai ta samo wata hanyar da zata shiga,don yasan irin karambanin ta kuma idan ta sa abu a gaba to tabbas sai taga qarshen shi.

Shukra ta shiga masaukin baqi tare da su manager da sameer da sauran mawaqa na bureu of music cikin shiga irin ta bayi wacce ta saba yi a da kafin ta zama palace maid,kuma har ta samu nasarar shiga dakin da ta dauki takaddar wancan karon,wani mai kida ne na bureu of music da yaga lokacin da suka wuce shi kuma yana tsaye,yake cewa na kusa dashi
"Kalli waccar yarinyar kamar shukra fah"
Juyawa dayan yayi
"Ya za'ayi kaga shukra anan? Bayan yanzu investigator ce?" Dayan ya bashi amsa
Kallon bayanta suke sosai da yake sun riga sun danyi nisa,wanda ya fara ganin nata yace
"Ka san ni na dade ina son yarinyar nan,ba yadda za'ayi na kasa ganeta ko da kuwa wane irin kaya tasa,kuma ka duba ka gani ai babu mace ko daya a servants din bureu if music sai ita kadai" jinjina kai dayan yayi tare da cewa
"Gaskiyane,ai itace ma,toh amma me zai kawo ta nan bayan ita lady investigator ce? Kuma cikin kayan bayi?" Wani dan china da ya kasance a cikin baqin da ya dade a bayansu yana jin abinda suke fada ya matso gabansu tare da cewa
"Kuka ce kunga lady investigator a cikin kayan bayi ta shigo nan?" Diriricewa sukayi,suka tambayeshi a tare
"Shin kana jin yaren korea ne? Har kaji me muke fada?" Bai amsa musu ba yayi maza ya hada kan sojojin su ya basu umarnin su shiga bangaren dakin baccinsu su kamo yarinyar da take ciki,kasancewar wakilin sarkin china da sukayiwa rakiya yana tare da mai martaba acan dakin ganawa da baqi na cikin quaters din,shukra tana can tana ta bincike bincike bata san me yake faruwa ba,littafin elementary learning da ta samu takkadar a ciki ne a hannunta ta jiyo daga waje ana cewa
"Ku shiga ku bincika ko ina ku kamo yarinyar nan" jin haka ta hanzarta ta bubbude littafin tare da daukar takaddar,ta nannade skirt dinta ta fara gudu,hangota sukayi tana gudu nan da nan suka bita a baya,gudu take tayi daga gani ta qware a gudun,ta shiga can ta fita can ba tare da tasan inda take shiga ba,suna ta binta a baya har ta bullo wani fili,royal guards ne gaba daya birjik a wajen,sun jeru a qame kamar basu taba motsi ba,yayinda mai martaba yake fitowa daga dakin ganawa da baqin tare da wakilin sarkin china ya rako shi,shukra tana shigowa ta tsaya qarewa wajen kallo domin ganin sojojin mai martaba ta tabbatar sarki yana wajen nan,idonta ne ya sauka akan mai martaba,ai da sauri ta qarasa wajenshi ta tsaya a gabanshi tare da cewa
"Yallabai me kake anan wajen? Gara da na ganka,ka taimaka min wasu mutane ne suka biyo ni" ganin baice mata komai ba,kuma ya dake ganin jama'ar da suke wajen,wani royal guard ne ya yanquro zai kama shukra,chief eunuch ya dakatar dashi kasancewar ya san wacece shukra,mai martaba ma yayi masa alama da hannu akan kada ya taba ta,matsawa yayi tare da rusunar da kanshi yace
"Yea your majesty " jin abinda ya fada yasa shukra a gigice ta kalli mai martaba tare da cewa
"Me yasa ya kiraka Your majesty?" Matsawa tayi da sauri daga gabanshi ta qare masa kallo tas,sai lokacin ta lura da dragon 🐉 robe din da yake jikinsa,a ranta tace
"Lallai sarki ne kawai yake sa dragon robe kuma kalar maroon" kafin ta gama tunani sojojin china suka shigo wajen

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now