Page 5

84 6 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤

                  ROYAL CONSORT
Korean inspired novel

         ©️ marriam mayshanu.... ✍️

Page 5

Ranar da ya kama jalila zata shigo masarauta,a cikin bureu of music su sameer ne suke taya manyan masu kiɗa da mawaqa zuwa wajen taron cikar ranar haihuwar young prince,wajen gaba ɗaya kowa yana ta hada - hada,muryoyinsu kawai kake ji yana tashi"shukra miqo min hula ta" wancan yace "shukra ina igiyar rigata?" ita kuma tana ta kai kawo a tsakanin su tana yi musu duk abinda ya kamata.

Daga ɓangaren jalila kuwa an aika dogarai majiya qarfi da palanquin (wani abu ne da akeyi da katako kamar ɗan ɗaki,idan mace mai matsayi ce bata tafiyar qafa sai ta hau abin,maza majiya qarfi su dauko ta a kaita inda zata je) Yayin da ta gama shirin ta tsaf,cikin riga da skirt na silk sai alkyabba plain mara ado wacce ita special court ladies suke sawa,takawa takeyi cike da qasaita tazo har inda palanquin ɗinta yake,tsayawa tayi yayinda da sauri ɗaya daga cikin dogaran ya sa hannu ya buɗe mata qofar ta shiga ta zauna,ɗaukan ta sukayi har cikin masarauta kuma cikin quaters ɗinta.
Qarasowarsu keda wuya ta tarar da maids dinta su shida a jere suna jiran qarasowarta,suna zuwa bakin quaters ɗin dogaran suka ajiye palanquin ɗin yayin da senoir maid ɗinta ta matso ta buɗe qofar,qafa ɗaya ta fara zirowa waje,kafin ta fito da ɗayar qafar sannan ta fito da jikinta gaba ɗaya duk maids din da suke wajen da dogarai a tare duk suka rusunar da kansu tare ɗan lanqwasa wuyansu qasa kaɗan domin nuna girmamawa da dawowar ta cikin masarautar.
Kallon maids ɗinta tayi da murmushi a fuskarta kafin tace komai suka haɗa baki tare da cewa"Barka da dawowa cikin masarauta my lady" murmushin fuskarta ta faɗaɗa tare da ce musu "yauwa sannunku,kwana da yawa,da fatan na same ku lapia"
"Lafiyarmu qalau my lady,amma munyi kewar ku sosai da sosai" chief maid ɗinta ta faɗa cikin tsananin farin ciki,murmushi kawai tayi tare da fara tafiya,suna nan a tsaye har sai da ta gota su sannan suka bi bayanta a jere,chief maid ce a gaba,sai sauran maids din sunyi jerin biyu biyu suka bita a baya sai eunuch (dogari) guda ɗaya wanda shine kamar guard kenan da zai dinga bata tsaro (wannan tsarin haka yake ga sarki,sarauniya,mahaifiyar sarki wato dowager queen,consorts da kuma special court ladies,dole akwai maids da suke take musu baya,doka bata yadda da fitarsu su kadai ba duk inda zasu akwai masu bin su a baya) haka suka tafi suna biye da ita yayinda tayi hanyar quaters ɗin sarauniya haneefa.
A can quaters ɗin sarauniya hannefa kuwa,fitowarta kenan domin zuwa wajen birthday ɗin young prince,yayinda maids ɗinta suke tsaye suna jiran fitowarta a bakin qofar quaters ɗin,a jere suke a tsaye amma duk kansu a qasa,sun dan lanqwasar da wuyansu qasa,fitowarta keda wuya ta fara taka steps din da suke bakin wajen tana saukowa,suka biyota a baya,dowager queen ce tare da maids ɗinta suna take mata baya ta qaraso,da sauri sarauniya haneefah ta qaraso gaban dowager queen ta tsaya tare da rusunar da kanta har wuyanta qasa tare da cewa "Barka da zuwa queen mother" murmushi dowager tayi tare da dafa kafaɗar queen tace "da alama kin gama shiryawa ma,zamu iya tafiya" jerowa sukayi tare yayinda maids ɗinsu suma suka jero suka biyo bayansu suka ɗauki hanyar fita daga quaters ɗin queen,yayinda jalila itama take takowa ta inda su suke fitowa,gaba da gaba sukayi yayinda jalilah da maids ɗinta suka rusunar da kansu domin gaishe da queen da kuma queen dowager,jalila ce kawai ta ɗago kanta yayinda maids ɗinta har yanzu kansu yake a qasa,da murmushi akan fuskarta ta kalle su a jere sannan tace "Barkanku your majesty,Shigowata kenan nazo nayi paying respect a gareki" ta fada tana kallon queen Haneefah,queen dowager ce ta banka mata harara yayinda haneefah murmushi tayi har cikin ranta tare da cewa "barka da shigowa lady jalilah,kamata yayi kije ki huta ai yanzu,zaki iya komawa quaters dinki yanzu"  jinjina kai tayi alamar gamsuwa tare da qara rusunar da kanta kafin ta juya,suma maids dinta suka juya suka bi bayanta suka bar wajen,kai tsaye quaters dinta ta koma.
Tana barin wajen dowager ta kalli queen haneefah tare da cewa "yarinyar nan tana wasa dani,don taga mai martaba yana kare ta,amma zanyi maganin ta,ke kuma harda wani sakar mata baki kina mata dariya" ta qarasa ranta a dan ɓace,murmushi haneefa tayi tare da cewa "Ni dawowarta bata dameni ba,domin nasan irin son da mai martaba yake yi mata ko ni baya min irin shi,bani da matsala matuqar dai zaman ta a nan zai bawa mai martaba farin ciki" ta qarasa fuskarta babu yabo babu fallasa,haka suka taho suna zantukansu har suka qaraso filin da ake birthday din,shigowarsu ke da wuya duk manyan baqin da aka tara a wajen,da sauran mutane da aka gayyato kowa ya miqe tsaye tare da rusunar da kansu qasa domin girmamawa a garesu,babban fili ne mai girman gaske,an qawata shi dogayen tebura ta kowanne ɓangare yayinda kujerun suke a jere,nan ne inda hakimai da ministoci da matansu da sauran manyan baqi suke zaune,yayinda aka shimfida wani carpet na alfarma a qasa shima gefe da gefe aka bar hanyar wucewa kawai,a kan carpet din wasu qananan pillows ne masu faɗi kuma basu da tudu sosai wanda a kansu ne ake zama,sai tebur dan qarami daidai yadda mutum zai iya cin abinci a inda yake zaune a qasa, can sama kuma matattakala ce sai qatuwar kujera mai kama da karagar mulkin qasar da adon dragon 🐉 a jikinta,hakan ya tabbatar min ta mai martaba ce ,inda nan na hango shi a zaune yana ta murmushi,queen ma tare da queen dowager nan suka hau yayinda queen ta zauna akan kujerar da mai martaba yake a kusa dashi,a gefen wannan kujerar tasu ne akwai kujeru a gefen dama da kuma hagu,ta hannun dama young prince da yau ake cika shekaru takwas a duniya a zaune cikin shiga ta alfarma,yayinda ta hagun queen dowager ta zauna,zamansu keda wuya duk sauran mutanen wajen suka zauna suma nan aka fara gudanar da taron.
Young prince ne ya taso daga kujerar da yake yazo gaban kujerar da mai martaba da queen haneefa suke ya rusunar da kanshi ya gaishesu,sannan sai ya yi qasa ya durqusa ya lanqwasa qafafuwansa ya zauna a kansu kamar dai zaman tsakanin sujjada biyu,nan ya sake yin qasa da kansa domin cika gaisuwar sa,mai martaba cikin murmushi ya fara da "ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka,Fatan albarka da alkhairi a cikin rayuwarka" haka nan ma sarauniya ta sa masa albarka sannan ya miqe tsaye ya qara rusunar da kanshi ya koma ya zauna a kujerar sa.nan take aka umarci masu kiɗa da su fara nishadantar da mutanen da suke wajen,Cikin qwarewa suka fara kidan a tare,sautin kidan ya fara fita amma ba yadda ya kamata ba,melody din kidan kwata kwata ya kasa fita yadda ya kamata,wanda keyi musu umarnin tsayawa ne ya tsayar dasu sannan ya qara yi musu umarnin su fara,hakan ce ta qara faruwa har sau biyar,daɗin sautin kiɗan yaqi fita gaba daya,firgici ne ya bayyana a fuskokin ministers da hakimai da suke zaune kamar dai akwai wani abu da ya tsorata su a dalilin rashin fitar salon kidan yadda ake so.

A can bureu of music kuwa,su sameer basa cikin wanda suka zo wajen bikin birthday din,suna zaune wasu daga cikin fadawan sarki suka shigo tare da bada umarnin sarki na suje ayiwa jalilah kidan barka da shigowa,hakan yasa su sameer suka shirya suka tafi zuwa quaters din jalila,tana zaune a sitting room dinta chief maid dinta ta shigo da sauri tare da ce mata "My lady,masu kida ne daga mai martaba ya aiko ayi miki na barka da zuwa" farin ciki ne mara misaltuwa ya lulluɓe ta tare da tashi da sauri ta fito bakin qofar quaters dinta,nan ta hango su suna shirin zama tare da shirya kayan kidansu,kujera aka kawo aka ajiye mata a nan ta zauna har suka gama shirinsu tsaf suka fara kidan,sai dai irin matsalar da aka samu a can ita aka sake samu a nan,domin salon kidan baya fita kwata kwata,haka sukai ta gwadawa amma abin ya gagara,firgici ne sosai akan fuskokin maids dinta game da abin da suka gani yayinda ita bacin ranta kawai bata samu damar jin sauti mai dadi ba domin shauqin soyayyarta da mai martaba.
Da alama dai jalila bata san dalilin da ya sa sautin kidan yaqi fita a ranar da ta shigo cikin masarautar ba,amma na tabbata hakimai da kuma maids dinta sun sani domin yadda fuskokin su suka nuna kadai ya isa shaidar hakan,to ko me yake faruwa kuma?
Nima maryam na tambaya amma basu bani amsa ba.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now