Page 57

100 6 0
                                    

Page 57

Tun ranar da aka dauke su nadeeyah,Hankalinsu basma da Aliya bai kwanta ba har sai da suka ji chief Suh ya dawo kuma mai martaba yayi umarnin a qara wani binciken,hakan yasa suma suka cire uniform dinsu suka tafi gidan queen haneefah,a tsorace suke dukkansu suna tafiya suna boye fuska,Aliya ce ta kalli basma
"My lady ni dai duk a tsorace nake! Idan muma aka ganmu a gidan aka kama mu kamar su Afrah fa?" Harararta basma tayi
"In komawa zakiyi kawai ki koma" girgiza kai Aliya tayi
"A'ah tunda nazo nan ai ba zan koma ba"
Qarasawa sukai har gidan queen haneefah,maids dinta ne kawai a tsakar gida,su basma suka gaishe su,cikin mamakin ganinsu suka amsa musu tare da yi musu iso wajen queen haneefah,bayan sun shiga sun gaisa suke sanar da ita mai martaba ya bada umarnin a qara bincike game da case dinta,cikin farin ciki da mamaki take cewa
"Da gaske mai martaba yasa a qara sabon bincike? Amma meyasa haka bagatatan? Don ko zuwa jiya ai babu wani labari kamar wannan" Da sauri basma tace
"Shukra ce your majesty!" Murmushi mai sauti queen haneefah tayi cikin tsananin farin ciki tace
"Shukra?" Basma ta jinjina kai
"Ehh shukra ta dawo,kuma dawowarta ne ya janyo duk wani sabon sauyi"
"Amma naji dadi sosai! Dama shukra tana raye bata mutu ba? Naji dadi sosai" Queen haneefah ta fada har zuciyarta take jin dadin kasancewar shukra tana raye.

Shima Abdullahi bayan gari ya waye,yaje gida yayi wanka ya canja kayanshi zuwa uniform din aiki sannan ya dawo ya fara aikin rarraba private guards na musamman da mai martaba ya aiko domin su taya shi tsaron shukra,rarraba su yayi duk suka zagaye gidan yadda babu wani abu da zai iya shiga ba tare da sun ganshi ba,bayan ya gama nuna musu ne ya shiga gidan,royal doctor da nurses hudu ya gani a farfajiyar gidan,da sauri ya qarasa wajen likitan
"Me yake faruwa ne?" Likitan ne ya girgiza kansa
"Jikin lady shukra ne babu dadi,shi ne nake son a dafo mata magani a kawo" da sauri abdullahi ya nufi dakin da shukra take,tana kwance tana ta rawar sanyi goshinta yana ta tsatstsafo da gumi,hannu yasa ya tallafo kanta yana kiran sunanta,da qyar ta bude baki tace
"Orabeuni!"
"Shukra! Tun yaushe kika fara jin rashin lafiyar Baki fada min ba?" Idonta a rufe tace
"Orabeuni! Kada ka sanar da mai martaba,zai shiga damuwa sosai,kada ka fada masa" zubewa tayi a hannunsa sumammiya,jijjigata ya fara yi daga bisani ya fara qwalawa likita kira.

Nadeeyah,Afrah da minister of state affairs sun galabaita saboda dauresu da akayi a kurkukun tribunal,chief Suh ne ya bada umarnin a kawo su zaiyi magana dasu tunda yanzu binciken yana hannunsa,kwantar musu da hankali yayi tare da tabbatar musu su dan qara haquri na dan lokaci kadan ne,domin kuwa gaskiya zatayi halinta.

Ministocin kudu gaba daya sun taru a gidan ministan tribunal domin tattauna yadda zasu hadu gaba daya qarfinsu suyi jayayya da mai martaba akan dawo da chief Suh tare da bashi babban matsayi,don basu da masaniyar dawowar shukra,shiyasa tsoron da suke ji kada chief Suh ya tono wani abin da zai sa gwamnatin su ta bare,don a halin yanzu sune ke da qarfin juya gwamnatin garin kasancewar sune mafi jinjaye kuma sarauniyar garin 'yar bangaren su ce.

Chief secretary ne ya shigo da takadda ya miqawa mai martaba,tare da yi masa bayani kamar haka
"Wannan takaddar tabbacin filin da aka bawa doctor Nuh ne,kuma anje a bincika an tabbatar da cewar a halin yanzu iyalansa ne suke da mallakin wannan filin,wannan duk binciken royal guards ne bisa jagorancin chief suh" jinjina kai mai martaba yayi yana duba takaddar,chief secretary ne ya qara rusunar da kanshi yace
"Amma your majesty kana ganin wannan ya isa hujjar da za'a qara bude sabon bincike? Ka san hakiman kudu sune suke da qarfin juya gwamnati a halin yanzu,na tabbata ba zasu zauna su zuba ido suna kallo ba alhalin suna da qarfin da zasu ja dakai"
jinjina kai mai martaba yayi
"Abinda ka fada hakane! Suna da ikon da zasuyi jayayya dani! Amma ni kuma da wannan ikon nasu zanyi amfani naci galaba akansu" cikin rashin fahimta chief secretary yace
"Zakai amfani da ikonsu domin cin galaba a kansu?" Kafin mai martaba ya kai ga bashi amsa suka jiyo muryar chief eunuch daga bakin qofa
"Your majesty! Eunuch Han ne"
"Shigo" mai martaba ya fada,shigowa chief eunuch yayi fuskar shi babu walwala ya rusuna yace
"Cheo-na! Yanzunnan na samu labari mara dadi"
"Menene?" Mai martaba ya tambaya yana mai dawo da hankalinsa kan chief eunuch,chief eunuch ya qara yamutsa fuska yace
"Lady shukra! Tana cikin mawuyacin hali,bata da lapia kuma rashin lafiyar ta tsananta sosai" zumbur mai martaba ya miqe daga kujerar da yake zaune yayi hanyar fita,da sauri chief eunuch ya bi bayanshi suka bar chief secretary a tsaye a nan,don ina ganin mai martaba ya ma manta da wanzuwar shi a wajen.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now