Page 31

74 8 0
                                    

(A cikin labarin mu a baya,mun fadi cewar anyi auren sarki da lady jaleela,kuma har an bata matsayin consort,kuyi haquri domin na cire wannan bangaren,a halin yanzu ku dauka lady jaleela special court lady ce kawai,bata zama matar sarki ba,kuma dama a can baya sarki yayi qaryar tana da ciki ne domin a yadda ta zama consort,sai dai yanzu wasan zai fara yadda za'ayi auren mai martaba da lady jaleela kuma a bata matsayin consort yayin da soyayyar shukra take shimfiduwa a cikin zuciyar mai martaba,ku biyoni dai domin akwai dogon zango a gaba)


Page 31

Juyowar da shukra zatayi taga IG yana shigowa,da murmushi ya qaraso gabanta,cikin yanayin damuwar da take ciki tace masa
"Yallabai.." murmushin da taga yaqi barin fuskarsa ne ya hanata qarasa abinda zata fada,cikin farin ciki yana kallon fuskarta yace
"Shukra" ya juya ya kalli nadeeyah da Afrah a tsaye sannan ya qara cewa
"Ku biyoni muje office,nan take ya zayyana musu duk yadda akayi har zuwa yanda mai martaba ya miqa Kim hannun tribunal minister domin yayi binciken wanda suke da hannu a wannan tuggun.

Tribunal minister cikin tsananin tashin hankali yake cewa danshi jameel
"Yanzu jameel kana kallo mai martaba ni ya bawa alhakin bincike akan Kim,gaskiya ya kamata a rufe bakinsa domin kada ya ambaci sunayenmu" shima jameel din da tashin hankali ne kwance akan fuskarshi tun bayyanar Kim ya jinjina kai
"Tabbas kuwa Abbana,lallai yanzu Kim zaiyi mutuwar gaske" jinjina kai minister yayi domin tabbatarwa jamell cewar lallai kashe Kim shine mafita a garesu.

Bayan su shukra sun bar wajen IG suka koma office of investigation,daki shukra ta wuce ta watsa ruwa tare da sa uniform dinta ta fito,tana zuwa office ta tarar chuef eunuch yana jiranta domin amsa kiran mai martaba,hakan yasa ta bishi a baya suka tafi har lambun da mai martaba yake shan iska,chief eunuch yana gaba tana binshi a baya har inda mai martaba yaje a tsaye,sanye cikin alkyabbarsa ta dargon maroon colour,ya nade hannunsa a baya,ya juya baya fuskantar su,sai da chuef eunuch yazo daidai bayan mai martaba sannan ya tsaya tare da rusunar da kanshi yace
"Mun qaraso your majesty" ba tare da mai martaba ya juyo ba ya bashi amsa da
"Zaka iya tafiya" hakan yasa chief eunuch ya juya ya bar wajen,shiru ne ya ratsa tsakaninsu,cikin nutsuwa mai martaba ya juyo yana kallonta,da sauri ta rusunar da kanta sosai tare da cewa
"Your majesty" kallonta kawai yake fuskar nan a murtuke,ita dai tunda ta sunkuyar da kanta bata dago ba bare ta san me yake yi ma,cikin fada ya fara magana
"Yanzu abinda kika yi kin kyauta? Har yanzu idan na tuna tashin hankalin da kika sani a ciki zuciyata bugawa takeyi kamar dawakai suna tsere" a yadda take bata dago ba tace
"Ka yafe min your majesty" tsawa ya daka mata
"Ke wacece da kika isa tsallake royal order?" Da sauri ta dago kanta ta kalleshi,murmushi yayi mata ya kashe mata ido daya,idonta ta sauke qasa ba tare da ta rusuna ba,ya bata rai tare da cewa
"Haka nake son ki dinga yi,dago idonki ki kalleni" banza tayi masa,kamar ba magana yayi mata ba,ai kuw aya fara masifa
"Kina palace maid,a qarqashin iko na,kuma in baki umarni kiqi bi ko? Ina da tabbacin kinsan me hakan yake nufi,bijirewa royal order zai iya sawa ayi miki hukunci mai tsanani" cike da tsoro ta daga kanta sosai ta kalleshi,murmushi ya sakar mata kamar ba shi yaje fada ba
"Yauwa,haka zakiyi,shukra kin tayar min hankali sosai,meyasa baki fara zuwa wajena ba kika tafi wajen wakili? Da ace bai yadda da abinda kika fada ba fa?" Qara saukar da kanta tayi,cikin sanyin murya tace
"Ai kaga kai sarki ne,ta yaya zan dinga yi maka yadda nake maka lokacin da nake zaton kai dan sanda ne? Ai ba zan iya ba" murmushi yayi,
"Amma lokacin da wakili ya barki kika fito meyasa baki nemeni ba,sai kika tafi wajen IG?" Shiru tayi bata ce komai ba,ya tunzura ya daga murya tare da cewa
"Nace ki dago kanki ki kalleni ko? Ko ba haka nace ba?" Dan dagowa tayi kadan,yace
"Dago dai" ta qara dagowa
Ya qara cewa
"Dago dai" haka ya dinga yi mata har ta dago kanta sosai,a tare suka saki dariya,ya fara bata labarin yadda ya kasa bacci saboda tunanin halin da take ciki,da yadda dawakai suka dinga tsere a cikin zuciyarsa saboda fargaba 😂😂😂 suna ta qyaqyata dariyarsu cikin tsantsan farin ciki,lady jaleela ce ta taho ita da chief maid dinta domin zuwa shan iska tare da mai martaba,tun kafin ta qaraso take jin dariyarsu tana tashi,daidai lokacin da ta hangosu daga nesa,burki tayi ta tsaya cak tana qare musu kallo,tabbas ita tunda take bata taba ganinshi cikin farin ciki haka ba,a hankali ta furta
"Yayi mata kyau" chief maid da ranta yafi na jaleela baci tace
"Me kika ce uour highness?" Jaleela ta juyo ta kalleta
"Uniform din investigators nake nufi,yayi kyau a jikinta sosai,baki gani ba?" Shiru chief maid tayi tana mamakin qarfin hali irin na jaleela,ko kadan bata son aga karayar ta,ta juya kenan zata bar wajen hankalin mai martaba ya kawo kanta amma shukra bata ganta ba,sallamar shukra yayi tare da sauri yabi bayan jaleela,hannunta ya riqo suka shiga sit room din dake wajen suka zauna,ko kadan bata nuna masa ranta ya baci ba,shima kuma bai yi tunanin ranta ya baci ba tunda dai shi ba son shukra yake ba bare yace ranta zai baci,tea din da suka taho dashi chief maid ta ajiye a tebur din dake tsakaninsu sannan ta fita ta bar dakin,lady jaleela cikin nutsuwa take zuba shayin yayinda mai martaba ya saki baki yana ta bata labarin shukra
"Kin ga yarinyar nan,duk da ta sani cikin tashin hankali kuma sai da nayi mata fada saboda abinda tayi amma duk da haka ina alfahari da ita" ya fada ba tare da ya kalli shayin da ta zuba ba,murmushi tayi mai qayatar wa tare da ce masa
"Lallai shukra ai yarinya ce mai hazaqa,kuma wacce ya kamata ayi alfahari da ita" washe baki yayi cikin farin cikin jin ta yabi shukra,ganin har yanzu bai lura da shayin da ta kawo ba ne,ya sa tace
"Your majesty ba zuba maka shayin" kallon dan qaramin kofin shayin yayi tare da kai hannu ya riqe amma bai kai bakinshi ba,ganin haka yasa tace
"Ko dai insa a dauke ne? Naga kamar hankalinka yana wani wajen daban" girgiza kai yayi tare da kai kofin shayin bakinshi ya shanye,dama irin qaramin kofin nanne mai kurba daya,ajiye kofin yayi
"A 'ah hankalina yana nan a wajenki my lady" girgiza kai tayi
"Your majesty,ai abinda yake cikin zuciya ba ta kalamai ake gane shi ba,ana gane shi ta yadda fuska da ayyukan mutun suka nuna,ko dai kana jin wani abu na musamman game da shukra ne?" Ta qarasa maganar da murmushi akan fuskarta,kamar bata fargabar amsar da zai iya bata,murmushi yayi mata mai dauke da mamaki,yace
"Wa? Shukra? A'ah babu wani abu na a daban kawai dai tana sani nishadi a duk lokacin da nake tare da ita,tana da abin dariya sosai,amma bayan haka babu komai" jinjina kai tayi
"Ka tabbata your majesty?" Nutsuwa yayi ya lura da yanayinta tare da ce mata
"Ehh na tabbata,kim ganki ! Kina kishi ne? Nayi mamakin ki amma" ya qarasa yana qyalqyale mata da dariya,itama dariyar ta taya shi
"Nima nayi mamakin kaina your majesty,ina tunanin kamar matan da suke kishi basu da hankali ne,amma kuma nima sai na samu kaina a haka" dariyar shi ya cigaba da yi mata,ta cigaba da magana cikin sauti mai sanyi
"Your majesty a rayuwar nan babu wani abu da mutum zai qayyade cewar ba mai iya faruwa bane,saboda haka kada ka miqa yaddarka sosai akan abinda kace kana ji a a kanta,domin zai iya kasancewa ba hakan bane,wani abu ne na daban" bai fahimci yadda tayi maganar a dunqule ba,hakan yasa suka canja hira,tare suka yini sai yamma lis sannan suka fito tare kowa yayi hanyar quaters dinshi.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now