Page 55

84 7 0
                                    

Page 55

Washegari da safe,a qauyen da su shukra suka fara zama kafin su samu shiga cikin birni,IG da abdullahi ne a gidan da suka sauka suna cin abinci,yayinda leiutenant NAM,da assistant lieutenant suke cikin qauyen suna zagayawa da zanen fuskar shukra,cikin sa'a qawar sulhee da tayiwa su shukra masauki ta ga hoton da ake yawo dashi ta kuma tabbatar musu cewar sun zo,amma a halin yanzu bata san inda suke ba sai dai ta san cewar sun shiga cikin birni ne bayan sun bar wajenta.

PALACE

Dan directan bureu of music,shashashan nan ne a tsaye yana leqen bayin masu diban ruwa don yace shidai ya samu wajen zama don yaga kyakyawa a cikinsu (shukra) tana shanya ne yana tsaye yana hangenta,da mamaki ya mirtsike idonsa
"Kai! Menene haka? Ai kamar wanann yarinyar ko? Amma ya akayi haka?" Ita dai bata san me yake ba aikinta kawai take yi,bayan ta gama shanyar ne ta juyo fuskarta sosai,tare da bin wata 'yar hanya ta bar wajen,a nan ya tabbatar da cewar itan ce kuwa,hakan yasa ya tafi da gudu domin kaiwa babansa rahoto,tahowa bakin rijiya tayi inda masu wanki sukeyi,wani kaya ta taka da qafarta tana qoqarin jefa guga cikin rijiya baiwar da take wankin tace mata
"Ki daina taka wannan kayan! Na queen's palace ne" da sauri shukra ta tsugunna tace
"Au! Yi haquri ban sani ba" durqusawar da tayi ta fara karkade inda ta taka da takalminta,wani farin qyalle ta gani yayi yellow alamar an qulle abu a ciki,da mamaki tace
"Wannan ai bawon mung beans ne" (wani irin wake ne) tana cikin dubawa taga wasu ladies in waiting da gudu sun wuce,mai yin wankin ce tace
"Lallai yau ladies investigators sun fito kenan" da sauri shukra ta kalleta
"Ladies investigators kika ce?"
"Ehh haka nace,da yake a cikin masarauta suna yin binciken quaters din ladies in waiting lokaci zuwa lokaci,amma yanzu zasuyi binciken ne saboda gubar da aka sawa her majesty" ai da sauri shukra ta tashi da gudu ta bar wajen,tsayawa tayi tana kallon yadda ladies in waiting din suke ta guje guje don boye abinda suka san za'a iya kamasu da shi,hannunta ta daga ta fara lissafi da 'yan yatsun ta,cikin farin ciki tace
"Yauwa! Madam nadeeyah zata yi inspecting laundry quaters ne,tunda anyi inspection guda biyu kenan bayan tafiyata" kai-kawo take tayi a wajen,ta san cewar dukka ladies din zasu zo,ya zatayi kenan? Ta yaya zatayi magana da nadeeyah ko afrah ba tare da kowa ya sani ba? Wasu kaya ta hango da suka bushe,daukan kayan tayi ta ninke sannan ta tafi quaters din ladies in waiting din dasu a hannunta,wani daki ta shiga ta ajiye kayan a cikin wani akwati,sannan ta tashi ta nemi waje cikin wata pause qarama ta saka wata takadda data shigo da ita sannan tayi saurin fita daga dakin,tana fitowa suna shigowa quaters din,sumayya ta gani a gaba tana ta wani cika tana batsewa hakan yasa ta buya da sauri,a can baya ta tsaya har suka gama suka tafi amma ta tabbatar Afrah bata ga takaddar data ajiye ba don sumayya ta hanata shiga dakin da tayi ajiyar wai sai dai ruqayya da sameerah su shiga su duba tunda Afrah tana cikin wanda suka taya queen haneefah aiki saboda haka zasu iya boye wani abin ita da nadeeyah.

Bayan sun koma office suna zazzaune Afrah ta shigo,tacewa nadeeyah tana son ganinta,akwai abinda take son ta fada mata,bayan sun fita ne take ce mata
"My lady! Ina tunanin shukra tana cikin masarautar nan!" Da mamaki sosai nadeeyah tace
"Shukra kuma? Da gaske? Ta yaya kika san haka?" Pause din ta dauko ta nuna mata tare da cewa
"A cikin dakin ladies in waiting din na gani" bude pause din tayi ta dauko takaddar doguwa da ita sosai amma babu fadi da wasu kalmomi marasa ma'ana a ciki,ta nunawa nadeeyah tace
"Kin tuna wanann? Irin takaddar da shukra ta samo a quaters din wakilin china lokacin da muke case din Yoon Dal?" Jinjina kai nadeeyah tayi da sauri,brush din rubutu afrah ta dauka tare da nannade takaddar a jiki,nan take ma'anar rubutun ta fito ta rubuta
"Laundry quaters servant water" tayi rubutun ne yadda su kadai zasu iya fahimta,ko da ta fada hannun wanda basu ba,to baza'a fahimci me hakan yake nufi ba,nadeeyah ce tayi saurin cewa
"Servant water zai iya daukar ma'anar water maid"
"Yes my lady! Wannan takaddar daga wajen Shukra take,na tabbatar wannan rubutun ta ne" Afrah ta bata amsa.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now