Page 7

65 4 0
                                    

Page 7
Shukra tana cikin tafiyarta tana ta kalle kalle don ta dan jima bata shigo cikin gari ba,nan take yarintar ta ta ringa zuwar mata a cikin tunanin ta,duk inda ta wuce sai ta tuna wani abu da ta taba yi a wajen,a cikin haka ne ya buge wani mutum bata sani ba,juyowa tayi da sauri jin ta buge abu ta ganshi fuskar nan a murtuke yana kallon qasa,idonta takai inda taga yana kallo nan taga wasu fararen duwatsu ne suka zubo daga cikin wata jaka da take hannun sa,da sauri ta tsugunna ta fara kwashewa tana cewa
"Kayi kin afuwa,kayi haquri ban ganka bane"
Tana bashi tana kwashe mai duwatsun sa,daga bayansa wani mutum ya taho da alama tare suke dashi
"Mutumina me ya hada ka da yarinya?"
Dago kai shukra tayi domin taga mai magana,lokaci daya ta qura masa ido tana son ta tuna a ina ta taba ganin fuskarsa,yayinda shi kuma tuni ya gane ta,basarwa tayi ta cigaba da taince fafaren duwatsun tana mayarwa cikin jakar har sai da ta tsince su tsaf suna tsaye,mutumin da yazo daga baya ne yake ta rarraba ido yana Allah Allah su bar wajen don da dukkan alamu shujra bata gane shi ba,hannayenta ta dago zata karkade sai taga burbushin farin abin da ta kwashe,nan take mamaki ya kamata da sumulmulallun duwatsu zasu yi burbushi haka,hannunta takai zuwa baki ta dandana abinda yake hannunta
"Gishiri " ta furta da qarfi tare da tofar da yawu,a birkice suke kallonta,wanda ta zubar wa da kaya ne ya zaro wuqa a qugunshi,ganin haka shukra ta juya da gudu suma suka bita a baya,gudu takeyi sosai ba tare da ta san laifin da tai musu suke binta ba,lungu lungu take shiga har tazo wani waje kamar akurki ta shige ta buya,tana shiga su kuma suna qarasowa wajen suka tsaya suka rasa inda tayi cikin haki wanda ya gane fuskar shukra yacewa dayan
"Wannan yarinyar fa idan bamu samota ba tona mana asiri zatayi,na gane ta servant girl a bureu of music,kuma ranar da mukai akin nan tana cikin maqerar don a hannunta ma na karbi aikin nayi" ya qarasa cike da firgici da kuma takaici,dayan ne yace
"Kai kabi nan hanyar,nima zanbi nan,sai mun nemo ta mu gama da ita"
Haka suka rabu kowa yabi hanyarsa daban suna neman shukra,sai da ta tabbatar sun yi nisa da wajen sannan ta fito tana karkade kayanta,wani mutum ta hango yana tahowa ta dan tsorata har ta kasa motsi,zuwanshi kusa da ita ta gane ba su bane,a daidai lokacin kuma suka dawo ashe wayo sukai mata,ganin wannan mutumin da yazo wucewa ta kusa da ita sai suka zata ko tare suke da shukra,takobi suka ciro masu tsayi sosai suka nuna su da ita,take wanda yake tare da shukrah ya rikice har ya fita shiga tashin hankali,kallonta yayi yace
"Menene haka? Suwaye su? Me mukai muku? Ni ban san wannan yarinyar ba fa"
Duk a tare ya jero wadannan tambayoyin cikin tsananin firgici,shukra ce ta duqusa qasa cikin hikima kamar ta sadida,da sauri ta damqi qasa a hannayenta tare da watsa musu a ido,hannun mutumin nan ta kamo da gudu suka bace a wajen kafin su gama share qasar idonsu sun bace musu.
Gudu sukeyi sosai yayinda ya fara haki amma shukra janshi take,tsayawa yayi tare da tsayar da ita itama yace
"Nifa na gaji,daga ganinki fitinanniyar yarinya ce,me ya hada ki da wadannan mutanen?"
Kallonshi take cike da mamaki tare da cewa
"Karka qara ce min fitinanniya,dan gudun da mukayi shine ka gaji? Ka tashi mu qara gaba kafin su qara biyomu ko na tafi na barka a nan"
Bata fuska yayi
"Toh ni ai tunda nake a rayuwata ban taba gudu irin wannan ba shiyasa"
Shukra mantawa tayi da halin da suke ciki ta sheqe da dariya tare da nuna shi da hannu
"Na san dai daga ganin kayan daje jikinka kai dan gata ne,amma dan wannan gudun kace baka taba yi ba? Raina min hankali kawai kake so kayi"
Bai bata amsa ba suka hango mutanen da suke biyosu amma wannan karon suna da yawa don sunkai kusan su shida,da sauri ta jawo hannunsa suka maqale a jikin katanga yadda ba za'a gane da mutum a wajen ba saboda duhun dare,har suka zo suka gifta su tare da shigewa gidan da su shukra suka buya a jikin katangar shi,da yake guntayen katanga ne ana iya hango farfajiyar gidan,shukra ce ta dan dago kanta kadan tare da leqawa cikin gidan,ganinsu tayi sun je wajen wasu buhunhuna masu yawa sun fara jidarsu suna zagayawa cikin gidan inda bata iya hangowa,suna tafiya suna maganganunsu,wanda yace ya ganeta ne yake cewa dayan
"Muyi maza mu zubar da wadannan sauran abubuwan tunda sun gama amfani,dama ni kudin da na samu sun ishe ni na gina sabuwar rayuwa ba tare da na koma aiki a maqera ba,ai godiya mai yawa ga queen dowager"
Dayan ne ya bashi amsa da cewa
"Gaskiyar ka fa,gara muyi sauri mu zubar dasu a daren nan kafin yarinyar nan ta koma masarauta ta tona mana asiri,don matuqar aka gano mu muka lalata salon kidan masarauta to zamu biya da rayuwarmu ne"
Mamaki ne da firgici kwance a kan fuskar shukra,ta juyo ta kalli wanda suke tare
"Mallam ka taimaka min da wani aiki mana,mutanen nan ina ganin basu da gaskiya,naji suna maganar lalata salon kida kuma dama ina son bincike akan hakan,ko zaka taimaka min ka haura nan mu shiga gidan nan"
Cikin wani irin yanayi da ba zata iya fassara shi kai tsaye ba yace
"Haura katanga? Ba zan iya ba gaskiya,ni ban taba haura katanga ba a rayuwata"
Dariya ta sheqe da ita tana nuna shi irin ya sharo mata qarya dinnan
"Kai..... kai baka taba haura katanga ba..." ta cigaba da dariyarta "Amma dai wasa kake ko? Ko kuma kawai kace ba zaka taimaka min ba" idonsa a kanta ya qara jaddada mata
"Da gaske ni ban taba haura katanga ba,katangar gidan mu tsayi ne da ita da mutum ba zai iya haurawa ba kuma a cikin gidanmu nayi makaranta da komai shiyasa ban iya ba"
Shiru tayi kamar mai nazari a yayin da take qara jiyo maganar mutanen sama sama a cikin gidan,kallonshi ta qara yi tare da cewa
"To ni ka juya na taka bayanka sai na hau,ka jira ni a nan na dawo kada ka tafi ko ina"
Da qarfi yace mata
"Ke kin isa ki taka bayana ki hau katanga? Kinsan wanene ni?"
Haba kai kuwa,kana ganin masu laifi kuma kaga babu mai taimaka mana a nan,ka juya mana in hau in shiga na gani"
Ta fada masa tare da marairaice fuska,qara bude idonsa yayi a kanta sannan yace
"Ni bari inje in samo mutanen da zasu taimaka mana mu fita daga yankin nan,don gaskiya ni ban saba haka ba"
Kallon shi take cike da takaici a ranta tace
"Mutum sarqeqen na qato amma sai lalaci fal cikinsa,bai iya tabuka komai...."
Katse mata tunani yayi da cewa
"Ki tsaya inje in nemo mana jami'an tsaro yanzu zan dawo" bai jira amsarta ba ya fara takawa a hankali ya bar wajen,leqawa take tayi a hankali tana hangosu har lokacin suna ta kwashe buhunhunan daga inda suke,ya kai minti kusan bakwai sai gashi ya dawo, cikin sanda ya qaraso inda take a hankali shima ya fara leqa su tare da ce mata
"Ki zo mu tafi nasa a kirawo 'yan sanda su zasu zo su tafi dasu"
Harara ta daka masa tare da cewa
"Ni ba zan bar nan wajen ba har sai naga abinda suke yi,wata tana can cikin qunci anyi mata sharrin ta zama annoba kuma naga abinda zai wanke ta kace na jira jami'an tsaro? Tunda kace ba zaka durqusa min in hau ba zanje in shiga ta qofa kawai" ta qarasa tana mai miqewa sosai ta fara tafiya,da sauri yace
"Ahhahh ki dawo zan durqusa ki hau tunda ni ban iya hawa ba"
Durqusawa yayi daidai katangar ta sa qafarta a gadon bayansa tana qoqarin haura katangar
"Ka dago sama,sama"
Ta fada,yayinda fuskarsa tuni ta nuna alamu na jigata,gumi kawai yake yi,da quar ya samu ya qoqarta ya dan dago ta haura katangar ta barshi nan a tsaye.

Wani matashi ne yake shiga babbar headquater 'yan sanda ta garin da wani abu a hannunsa,katako ne abin da rubutu a jiki sai qasan akayi igiya mai beza bazar bazar haka,yana shiga da gudu fili ne fetal sai gine ginen katako irin na wancan zamanin,wajen zagaye yake da sandunan aci bal bal wanda sune suke bawa wajen haske,kai tsaye wajen wasu 'yan sanda da ya gani a tsaye ya nufa yana haki
"Barkanku ranku ya dade,ina da saqo zuwa ga babban sufeto(inspector general )"
Cikin sa'a yana cikin mutanen da suke tsaye,a nutse ya kalli mutumin tare da cewa
"Lafiya? Daga ina?"
Abinda yake hannunsa ya miqa masa da sauri,ido ya zaro tace da cewa
"Imperial dispatch seal" ya kai kallonshi ga matashin tare da cewa
"Waye ya baka wannan?"
"Wani mutum ne ya bani yace in kawo nan" ya bashi amsa kai tsaye,IG ne ya qara cewa
"Ina ne inda yace maka?"
"Bayan hauren maqera" ya qara bashi amsa
IG ne ya kalli wani dan guntun a kusa dashi yace
"Gather all force,mai martaba yana cikin hadari"
"Yes sir" ya fada tare da barin wajen don tqjo da sauran 'yan sandan da suke available.

Har yanzu bamu shiga cikin labarin ba gadan gadan,ku kasance tare dani domin jin yadda zamu warware komai.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now