Page 50

165 7 0
                                    

Page 50

JOSHUN CAPITAL

da sauri assistant director na tribunal yake tafiya da wata takadda a hannunsa,office din jameel ya shiga cikin hanzari ya miqa masa takaddar,mamaki ne kwance akan fuskar jameel bayan ya gama karanta takaddar,dago kai yayi ya kalli AD
"Ka tabbatar da abinda takaddar nan take fada?" Rusunar da kai yayi
"Na tabbata yallabai" da hanzari ya fito daga office din ya nufi cikin palace,har chamber din queen jaleela,iso akai masa sannan ya shiga ya sameta,hankali a tashe ya fara yi mata bayani
"Your majesty! Tun bayan korar IG daga aiki,yana can yana zagaye sassan qasarnan ne domin neman wata yarinya,kuma ina da yaqinin cewar shukra ce yake nema" hankalin ta ya tashi sosai,wani zazzafan numfashi ta sauke bata ce komai ba
"Your majesty! Na tabbata mai martaba yana da dalilin da yasa yake nemanta,wataqila domin ya samu cikakken bayani ne game da sauke queen haneefa" rarraba ido kawai takeyi,ta kasa cewa komai gashi jaleel baya gari,kauda kai tayi
"Tashi kaje kawai! Zan nemeka idan nayi tunanin abinda ya kamata muyi" gwiwarsa a sanyaye ya tashi ya fita,qoqarin boye tashin hankalin ta takeyi kamar yadda ta saba,yunqurawa tayi ta tashi ta fito waje,maids dinta ne suka bi bayanta har grand palace,chief eunuch ne ya gaishe ta,cikin bada umarni tace
"Ayi min iso wajen mai martaba" rusunar da kanshi yayi
"Your majesty! Mai martaba yana tsaka da ganawa da wasu baqi da yayi,zan aiko quaters dinki idan ya....."
"Shikenan! Zan shiga ciki in jira shi" ta fada masa cikin izza,matsawa yayi daga hanya kanshi a qasa ta wuce ta shiga ciki,kalle kallen wajen take yi ba tare da ta zauna ba,idonta ne ta sauka akan kwalin an ajiye shi akan kujerar mai martaba,da yake duk inda kujerar sa take ta fita daban,saboda adon dragon da yake jiki,an nade kwalin da qyalle mai shegen kyau,hannu ta saka ta dauki kwalin tare da zuwa ta zauna,a tsanake ta kwance daurin da akayiwa qyallen sannan ta bude kwalin,da mamaki take kallon dan qaramin takalmin,kuma nan da nan ta fahimci zaiyi daidai da qafar shukra,daga kanta tayi sama domin mayar da hawayen da yake qoqarin zubo mata
"Ashe tana ranka duk tsawon lokacin nan your majesty?" Da sauri ta rufe kwalin tare da daure qyallen ta mayar inda ta dauka sannan ta fito,chief eunuch ne ya matso
"Your majesty.." dakatar dashi tayi
"Dama nazo gaishe da mai martaba ne,zan wuce kuma kada ka sanar da shi zuwana!" Rusunawa yayi kawai baice komai ba har ta wuce a fusace.

A tsakar gidan queen haneefah,madam nadeeyah ce da afrah,sai queen da maids dinta sai minister of state affairs a tsaye,dama su nadeeyah sun fito zasu tafi ne yayinda minister kuma yanzu ya shigo,sallama sukai musu sannan suka kamo hanyar dawowa cikin palace,kayane a jikinsu irin na mutanen gari ba uniform din aiki ba domin kada a gane su.

A Office of investigation,sameerah da ruqayya ne tsaye a gaban chief madam sumayya,ruqayya ce take bata labarin
"My lady! Da idonmu muka gansu a cikin gidan queen haneefah tare da wasu hakiman arewa" jinjina kai sumayya tayi cike da makirci tace musu
"Ina son ku qara samin ido a kansu,da kuma gidan queen haneefah a boye" rusunar da kansu sukai
"Yes Madam Chief" sannan suka fita daga office din nata,tashi tayi itama ta fito kai tsaye queens palace ta nufa,bayani tayiwa queen jaleela,sun tattauna akan abinda ya kamata suyiwa queen haneefa saboda ko da an samu hujjar abinda sukayi a baya zai zama bashi da amfani.

UIJU

Ya shirya tsaf cikin kayan mutunci,da mamaki shukra tace masa
"Kana ganin kuwa zaka iya?" Harararta yayi
"To idan ban iya ba ya zamuyi? Ai dole wanan itace damar mu ta qarshe" kayan jikinshi ta kalla
"A ina ka samo wannan kayan?" Shima jikin nashi yake kallo
"Ina zan samo su kuwa? Na director ne!" Hannu tasa ta rufe bakinta tare da zare ido
"Me? Kayan director ka saka? Yanzu idan ya kamaka fa?" Kafadar sa ya daga
"Babu abinda ya dameni! Kafin ya kamani na gama abinda zanyi dasu" gyara zaman hularsa yayi tare da ce mata
"Mu tafi ko? Kada mu makara" gaba yayi,itama ta bi bayanshi da sauri,gabanshi ta sha ya tsaya yana kallonta
"To fada min ya kayi da tafintan? Ba dai kashe shi kayi ba ko?" Girgiza kai yayi
"A'ah zaiyi ta bacci dai har gobe da safe" ajiyar zuciya ta sauke amma duk a tsorace take da lamarin,don tafi kowa sanin waye jaleel,kuskure daya zasuyi su shiga hannu,sai da suka zo bakin qofar shiga gidan saukar baqin ya tsaya tare da dauko wani littafi daga cikin rigarsa
"Menene wanan kuma?" Shukra ta tambayeshi,yana bude littafin yake bata amsa
"Littafin koyon maganganun 'yan china ne" yamutsa fuska tayi tana nuna shi da hannunta
"Kana nufin baka ma iya chainancin ba?" Girgiza kai yayi
"Na iya mana! Ba dai sosai bane" boye littafin yayi daga inda ya ciroshi sannan ya shige gidan ita kuma ta tsaya anan tana jiran dawowarsa.
Basarwa yayi yana ta huhhura hanci har ya qaraso bakin qofar,masu gadin jaleel ne suka tambayeshi waye shi,cikin dakewa da qwarin gwiwa yace musu
"Nine tafintan da aka turo daga gidan hakimi!" Mutum daya ne ya shiga domin yi masa iso,sannan aka barshi ya shiga.
Bayan ya zauna ne suka fara magana,jaleel yace ka fada masa cewar "Nazo ne domin ya taimaka min a samu sahalewar sarkin china akan cikar matsayin yarima mai jiran gado"
naseer ya fadawa dan chinan da yaren da yake ji,sai yace ya bawa jaleel amsa da
"Kasancewar hakan ra'ayin sarkin china ne,hakan zaiyi wahala sosai" jaleel yace ya fadawa dan chinan cewa
"Kada ya damu,za'a biyashi ladan abinda zaiyi" haka dai suka cigaba da harqallar su naseer yana nade komai,ita kuwa shukra tana waje tana jiranshi taji wani a cikin masu gadin jaleel ya fito yana cewa wanda suke tsaye a waje
"Idan tafintan nan ya fito a rufe mana bakinsa!" Cikin neman qarin bayani yace
"A rufe bakinsa? Kana nufin..."
"Ehh yana fitowa ku kashe shi" shukra ta tsorata sosai da jin haka,hanyar da zata iya sanar dashi ta fara tunani,ta baya ta zagaya ta shiga cikin gidan,cikin sanda take tafiya ai kuwa taci karo da masu gadin jaleel,cikin tsawa suka fara tambayar ta
"Ke! Me kikeyi a nan wajen?" Dan kame kame ta fara
"Ni....ni baiwa ce a nan gidan,dama madam SULHEE ce tace in tsaya a kusa ko da akwai abinda zaku buqata" tsawa ya daka mata
"Ki bace mana daga nan! Babu abinda muke buqata,idan muna buqata zamu neme ki" wucewa sukai daga wajen,dafe qirjinta tayi ta sauke ajiyar zuciya,ai tana qara yin wata kwanar taci karo da madam SULHEE tare da wani,tsayawa sukai suka fara tambayarta daga ina? Shukra fa ido yayi wuri wuri,mutumin ne yace
"Ina ganin yarinyar nan bata da gaskiya!" Da sauri ya leqa ya kirawo masu gadin,kafin yadawo ta riqe hannun madam din
"Baki gane ni ba? Ni ce fa Shukra maleek! Mun hadu a can office din garin nan! Ni baiwar gidan directa byun ce"
Da mamaki madam din tace
"Shukriyya maleek?"
daidai inda masu gadin suka qaraso kenan,da mamaki suka kalli madam din
"Kina nufin wannan yarinyar ba mai aikin ku bace?" Mutumin da yaje ya kirawo su yace
"A'ah ba baiwar mu bace! Ku tafi da ita" ai kuwa suka kamata,tana ihun neman taimako,kamar wacce ta dawo daga tunani sulhee tace musu
"Ku dakata!" Tsayawa sukai suna jiran me zata ce,shukra ta kalla
"Da gaske kece shukriyya maleek? Qanwar abdulshakur? Shukriyya?" Tsananin mamaki ne ya rufe shukra,don ba kowa bane yake kiranta da shukriyya sai wanda ya santa tun yarintar ta,don tana sane ta canja sunan daga shukriyya Anas maleek zuwa shukra anas malak,cikin kaduwa take kallon madam din ta kasa cewa komai,hannunta sulhee ta riqo
"Ke qanwar royal musician abdulshakur ce! Shukriyya!" Janyo shukra tayi ta rungume ta tsam a jikinta,janyeta tayi suka tafi daki,ganin haka yasa masu gadin suma suka bar wajen,tunda ta nuna ta santa,zaunar da shukra tayi sannan itama ta zauna,kamar wacce zatai kuka tace
"Allah ya taimaka na ganeki da wuri! Da kin shiga matsala" rusunar da kai shukra tayi
"Nagode sosai kin ceceni! Amma kiyi haquri rashin ganeki da banyi ba" girgiza kai sulhee tayi
"A'ah ba laifin ki bane,rabona dake tun kina shekara goma sha daya

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now