Page 17

54 5 0
                                    

Page 17

Mai martaba da shukra suna tafe a cikin gari suna hirar su,ya kalli shukra yace
"Ke dai da alama ba kya jin magana,ba na ce miki ki daina yawo da daddare ba? Yanzu da ban zo ba fa? "
Rusunar da kanta tayi tare da cewa
"Nagode yallaɓai ka ceci rayuwata,amma yau na fito ne domin yin wani aiki mai muhimmanci"
Mayar da hankalinsa yayi gaba ɗaya kanta tare da cewa
"Wane irin muhimmin aiki ne wannan?"
Zaro ido tayi tana nuna shi
"na tuna,Ai har nemanka naje yi saboda aikin amma mai gadin yace min kace baka sanni ba"
Da sauri kamar an tsikare shi yace
"Ina kikaje nemana??"
Tace
"Office din 'yan sandan sirri mana? Ba nan ne wajen aikin ka ba? Amma suka ce min wai kace baka sanni ba"
Cikin rashin sanin abinda zai ce mata ya fara in-ina,can ya samo abinda zaice
"Ai ina jin wajen ɗayan shugaban suka je,kinsan mu biyu ne shuwagabannin wajen,kuma wancan office ɗinsa yafi kusa da qofar shigowa" murmushi shukra tayi cike da shashanci tace
"Auu hoo,shiyasa ashe suka ce yace bai sanni ba,ni kuwa har na zata ko ka manta da sunana ne" ta qarasa har yanzu da murmushi akan fuskar ta,shima murmushin ya mayar mata tare da cewa
"Yauwa baki faɗa min muhimmin aikin da kika ce kinje yi ba" ɗan ɓata fuska tayi
"Kasan office of investigation sunyi arresting ɗin lady jalila,kuma akan abinda bata aikata ba shine naje samo hujjar da zata nuna bata da laifi" ji yayi kamar an soke shi jin sunan lady jalila,cikin sanyi yace mata
"Toh yanzu me kika samo?"
Nan ta kwashe duk bayani duk faɗa masa,har da tafiyar IG wajen mai martaba,jin haka yasa guard dinsa guda ɗaya ya rakata har cikin bureu of music shi kuma ya juya ya tafi police bureu.

Da zuwansa shima IG ya dawo daga masarauta kuma an kawo pinellia da qwararren mai binciken gawa,mai martaba ne yayi umarnin a maimaita irin yadda shukra tayi,aka qara yi bai bada kala ba,sai yayi umarnin IG ya taba pinellia sai shima aka shafa mai vinegar,ana saka farin qyalle aka goge sai gashi kalar pink ta bayyana,murmushin nasara ne duk ya bayyana a fuskokinsu,mai martaba ya jinjina kai tare da kallon IG yace
"Kuma da gaske yarinyar nan ce ta bayyana wannan hujjar?"
Jinjina kai IG yayi cike da girmamawa yace
"Nima ina mamakin hakan your majesty,tabbas ita ta bayyana hakan"

Washegari da safe,a office of investigation,chief sumayya ce sai Sameerah da Aliya a bayanta,sun taho daga bangaren da ɗakunan baccinsu yake zuwa cikin office,wata tawagar investigators ne suka taho,wacce take gaba kayanta iri daya sak da na chief sumayya,ganin yadda chief sumayya da tawagar ta suka dakata suka tsaya cak a inda suke tare da rusunar da kansu a tare hakan yasa na gane mai tahowar wata babba ce a wajen,qarasowarta wajen chief sumayya tace
"Barka da shigowa Director"
Suma wanda suke bayanta haka suka furta a tare,hakan ya tabbatar min da cewar ita wannan matar tafi sumayya matsayi a wajen,wato itace director ɗin office of investigation gaba ɗaya,fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli sumayya tare da cewa
"Ina fatan lady jalila ta shirya domin tafiya ofishin tribunal" itama sumayyan murmushi tayi tare da rusunar da kanta tace
"Ta shirya ranki ya dade,guards din tribunal kawai muke jira wanda zasuyi mata rakiya zuwa can" jinjina kai director tayi cike da gamsuwa tace
"Office of investigation kunyi qoqari matuqa a qarqashin jagorancin ki kun kammala case mai wahalar ganewa,idan komai ya lafa zamuje tare domin ki gana da queen dowager"
Murna ne da tsantar farin ciki ya bayyana a kan fuskar sumayya,cike da zumuɗi tace
"Ranki ya dade da gaske zanje wajen queen dowager?" Murmushi director tayi mata na tabbatar wa da abinda ta fada sannan ta yi gaba ta tafi ta bar su sumayya a wajen.
Sameerah ce ta qaraso gaban sumayya tare da ce mata
"Congratulations my lady,ba qaramar karramawa bace zuwa ganin queen dowager"
Ta fada itama cikin tsantar farin ciki,sameerah ce ta qara qasa qasa da muryarta
"Dama aikinmu dole yasa queen dowager farin ciki tunda dama tana neman yadda zatayi da jalila kuma gashi ta samu,wataqila ke zaki zama next director a office dinnan"
Sumayya ce itama ta mayar mata cikin rada
"Ke ki daina gaggawa,mu fara zuwa ma mu gaisa da its kafin ki fara tunanin zama director " ta qarasa cike da murmushi da yake nuni da tsantsar farin cikin da take ciki.

Tana shiga cikin office dinta taci karo da nadeeyah da basma wanda a qa'ida su suke biye mata a matsayi,tashi sukayi cikin girmamawa da rusunawa suka gaishe ta sannan suka koma suka zauna,cike da ladabi nadeeya tace
"Ranki ya dade akwai abin dubawa da muka ga ya dace a qara bincikawa a al'amarin nan"
a take farin cikin da ke fuskarta ya gushe,ta kallesu a tsanake tare da cewa
"Kamar ya a sake bincike? Ban gane ba"
Har basma zatayi magana,nadeeya ta katse ta da cewar
"Ranki ya dade bayan an sallami yarinyar nan shukra,ta sameni take fada min lallai fa lady jalila bata da laifi,hakan yasa na nemi taimakon basma muka tafi kasuwa inda ake dealar itatuwan,mun duba littafin da suke record kuma mun tabbatar sama da shekara uku ba'a siyar wa wannan mai maganin itacen pinellia ba,shiyasa muke tunanin idan aka sake bincike za'a iya gane inda matsalar take"
Chief sumayya tayi kasake tana jinta,sai da ta gama tsaf sannan tace
"Toh kuma sai akace don bai siya pinellia ba shikenan ba zaiyi amfani da ita ba,mu mun gama bincike kuma babu abinda zai sa mu sake wani bincike a halin yanzu,bayan ana ganin mun qara ɗaga darajar office of investigation har ana tunanin queen dowager zatayi mana tukwuici shine zaku kawo mana wani zancen banza?"
Basma cikin murya mai sanyi tace
"Ranki ya dade idan mukai haka za'a hukunta wanda ba shi yayi laifi ba,alhalin mai laifin yana nan yana yawo a cikin masarautar nan"
Wata gigitacciyar tsawa chief sumayya ta buga mata
"Ai sai kuma ku yi!!! Na fada muku ku ajiye wannan shirmen zancen da kuka samo domin bincike ya qare"
Kafin su nadeeya su farfado daga tsawar da aka daka musu,sameerah ta shigo da gudu har tana tuntube,da dukkan alamu cikin tashin hankali take
"My lady ki fito kiga me yake faruwa a waje"
Zumbur chief sumayya ta miqe da sauri tayi waje,haka nan nadeeya da basma suka bita domin ganin me yake faruwa,chief sumayya ce cike da mamaki tace
"Kamar royal guard nake gani,ina tribunal guard din kuma?"
Afrah da take tsaye ce tayi saurin qarasowa wajen chief sumayya
"My lady sun ce sunzo ne qarqashin umarnin mai martaba domin tsaron lafiyar lady jalilah"
Cike da rudani ta kalli afrah kafin tace wani abu sai ga royal chief secretary ya taho da sauran sakatarorin cikin masarautar suna dauke da tray wanda takadda ce a kai,shigowar su yasa dole director ta office din ta fito daga office,suna qarasowa dukka ladies investigators din suka rusuna don girmama su,domin da an ga chief secretary toh anga umarnin mai martaba,hannu ya miqa aka miqo masa takaddar da suka zo da ita,kai tsaye ya miqawa director din,a hankali ta bude takaddar ta fara karantawa,tashin hankali da firgici ne qarara ya bayyana akan fuskarta har takai qarshen takaddar,juyawa tayi tare da miqawa chief sumayya,tashin hankalin da sumayya ta shiga yafi wanda director ta shiga sai aka shiga kallon kallo a tsakaninsu,sauran ladies investigators da suke tsaye basu san me yake faruwa ba duk sun shiga rudanin shin me yake shirin faruwa a safiyar yau?

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now