Page 49

112 7 4
                                    

Page 49

Tana durqushe tana cire ganyen lettuce (salad) 🥬 daga cikin qasa,a hannun ta wata qaramar fatanya ce tana ta cirewa,tun maids din suna hanata har sun haqura saboda tana jin dadin yin nomar,chief maid din tana gefe itama tana wanke wani ganye dayar maid din ta shigo da saurinta tana cewa
"Your majesty!" Queen haneefah da sauri ta juyo don ganin dalilin wannan kiran,yarinyar cikin murna tace
"Kinga na kawo littafin nan da yake tashe a cikin gari" queen haneefah mayar da kanta tayi ta cigaba da abinda take yi,yarinyar cikin sanyin jiki tace
"Na kawo ne ko zaki karanta kema" cikin sanyin murya tace
"A'ah ba zan karanta ba" chief maid da take zaune tace
"Ai kuwa da kin karanta your majesty! Wata qila zakiji sauqin bacin ranki! Domin fitar littafin nan yana nuni da cewar mutanen gari duk basu goyi bayan rashin adalcin da aka yi miki ba,kuma na tabbatar wanann haqurin da kikayi wata rana mai martaba zai gano gaskiya" cikin sanyin murya tace
"Ta yaya littafi guda daya zai dawo da abinda ya riga ya faru? Ni damuwata shine mai martaba zai iya shiga damuwa saboda littafin nan" shiru dukkansu sukai,domin sunsan tunda tace ba zata karanta ba,to ba zata karanta ba din.

PALACE

"Ki daina damuwa your majesty! Domin muna ta aikin batar da littafin nan a hannun mutane" girgiza kai tayi
"Duk da haka mutane suna surutun cewar bai kamata na zama sarauniya ba,ya kamata mu nemi wata hanyar da zata tabbatar cewar babu wani abinda zai sameni" jaleela ta fada cikin damuwa,jaleel kuwa babu damuwa ko kadan a tattare da shi,cigaba tayi da magana
"An nada prince a matsayin yarima mai jiran gado ne akan umarnin mai martaba,amma inda ace zamu samu rubutacciyar takaddar sahalewar sarkin china akan hakan,na san babu wani abu da za'a iya yi min domin zan kasance uwar yarima mai jiran gado kuma babu wanda ya isa ya taba ni"
"Gaskiyane your majesty! Ki bar komai a hannuna domin ni na gama shirin wannan ma tun tuni" ajiyar zuciya ta sauke domin hankalinta kwata kwata ba'a kwance yake ba.

UIJU

Shigowarta cikin dakin ajiyar su kenan tana qoqarin saqale wani kwando a jikin qusa taji ta taka abu,firgigit ya cire tabarmar kabar da ya rufe jikinshi da ita domin yaji zafin taka shi da tayi,ita kuwa firgita tayi ganin mutum a cikin store room din,da hannu ta fara nuna shi cikin mamaki tace
"Kai...!" Shima nuna ta yakeyi
"Me kake yi a cikin store room dinmu?" Tashi yayi ya zauna,shima yace mata
"Kema me kikeyi a nan gidan? 'Yar aiki ce ke a nan?" Gyada kai tayi,qasa qasa yace mata
"Mai gidan nan ne ya sani kwana anan saboda ya bani wake ban siyar ba,kuma ba zai barni na zauna ba sai dai in dinga siyar mai da wake saboda banida kudi" bakinta ta rufe cike da mamaki tace
"Kaine ma'aikacin gwamnatin da akace zaizo ya zauna a gidan nan? Ai har na gyara maka dakin da zaka zauna" bayanta yabi ta kaishi har dakin,da abin shimfida da na lulluba,haquri ta bashi akan abinda tayi masa a kasuwa tunda ita bata san da gaske yake ba,sai da ta gama sannan ya jefa mata tambaya
"Amma kina 'yar aiki ya akai kika iya karatu? Ko dai da gaske ke palace maid ce?" Zaro ido tayi,cikin rawar murya tace masa
"A'aahhh kawai dai ina jin ana yi ne" Kallon tuhuma yake mata
"Ji kikai anayi? Ai wanann littafin da kika gani a hannuna ko 'ya'yan masu kudi ma da ake kaisu makaranta basa iya karanta shi sosai,ki dai fada min gaskiya" miqewa tayi ta tattare bokitin ruwan da tsumma da ta shigo dashi tace
"Idan babu abinda za'a yi maka zan tafi" bata ma jira amsar shi ba ta fice daga dakin,tana fita ta dafe qirjinta
"Wai! Allah ya taimakeni! Idan aka gane cewar ni palace maid ce ai Zan shiga mummunan hatsari!" Yaron director ne ya qaraso wajen da take tsaye
"Shukra! Director yana nemanki" da hanzari ta tafi zuwa inda yake zama,yana hangota yace
"Yauwa zo ki zauna" takaddu ya miqa mata
"Ki fitar min da takaddun nan,ki lissafa komai yadda ya kamata sai kisa a cikin envelope ki jera su dai yadda kikeyi,domin kwanan nan ina da muhimmin aikin da zanyi shiyasa ba zan samu lokacin zama ba"
"An gama yallabai" tace masa cikin girmamawa,tashi yayi ya fita ya barta ta fara aikin da ya saka ta,envelope dinne bai fito dasu ba,hakan yasa ta fara bin durowar da suke dakin daya bayan daya tana dubawa,a nan ne taci karo da wasiqu sunkai guda goma duk wanda take bayarwa akai wa yayanta,ba wanda aka kai,cikin kaduwa ta dauko su ta fito waje,yaron directer ta samu
"Yallabai! Yallabai!!" Ta qwala masa kira,yana qarasowa inda take ta nuna masa takaddun hannunta
"Wanann takaddun! Wasiqun da nake baka ne a kaiwa yayana,me sukeyi a dakin director?" Wuri wuri yayi da ido,dama shi yana jin tausayin yarinyar
"Kiyi haquri shukra! Ba'a son raina nayi miki haka ba,director ne ya saka ni" bayanin komai yayi mata,bayan ta koma daki,a tsorace take sosai saboda abinda yaron director ya fada mata game da rashin aika wasiqar ta
"Director ya hana tura wasiqun ne saboda yana son ki zauna a nan har abada saboda qwaqwalwar ki domin ki cigaba da kula masa da kasuwancin sa" sunkuyar da kai tayi
"Shukra! Director abin tsoro ne,yawan kudin da lokacin da ya bata akan ki,na tabbata ba zai taba barinki ki tafi ba"
Matse takaddun tayi a hannunta kasancewar dare ne yasa bata qara fitowa ba sai saqe saqe da take a acikin zuciyar ta.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now