Page 51

81 5 0
                                    

Page 51

IG da abdullahi a gajiye suna ta tafiya akan doki,sun qaraso cikin wani qauye inda IG ya kalli abdullahi da ya gaji yayi liqis yace masa
"Bari mu duba wajen ajiye dawakan mai martaba a qauyen nan,mu huta a can sai mu dauki wasu dawakan mu ajiye wannan,don wannan ba zasu iya haura nan ba saboda gajiya" jinjina kai kawai abdullahi yayi domin baya ma son magana,a hankali dawakan suke tafiya har suka qarasa wajen,seal din da mai martaba ya bawa IG ya dauko,tare da nunawa eunuchs din da suke kula da dawakan wajen,yace
"Muna kan umarnin mai martaba! Muna buqatar canjin dawakai" sunkuyar da kai eunuch din yayi cikin sanyin murya yace
"Yallabai babu dawakai a nan!" Da mamaki IG yake kallon shi,cikin qaraji ya daga muryarsa ya dakawa eunuch din tsawa
"Kamar ya babu dawakai a nan?Ai hakan ba mai yiwuwa bane,nan wajen ajiyar dawakan mai martaba ne"
"Kayi haquri yallabai" eunuch din ya fada cikin yanayin rashin gaskiya,da wata tsawar IG ya ce masa
"Wannan ne kadai uzurin ka? Toh idan baka bamu dawakai ba lallai kana qoqarin bijirewa umarnin mai martaba ne! Maza ka fada min inda dawakan suka tafi" sunkuyar da kai yayi ya fara gumi,hannayensa ya fara murzawa,bai ankara ba yaji takobin IG a wuyansa,a tsorace ya dago idonsa ya kalleshi
"Zaka fada ko sai na gama da kai?" Hannu ya hada waje daya
"Ka taimaka kada ka kasheni yallabai"
"Fadi toh! Fada min ina dawakan suke?"
"Yallabai jaleel......shine suka tafi da dawakan shi da mutanen sa" da mamaki IG yayi saurin dauke takobinsa daga wuyan eunuch din,a hankali ya furta
"Jaleel?" Shima abdullahi da yake tsaye abinda ya furta kenan cike da tsananin kaduwa,IG da qyar iya bude bakinsa ya tambayi eunuch din
"Jaleel garin UIJU ya yafi daga nan?" Rusunawa yayi
"Yes my lord!" Hakan ya qara firgitasu matuqa,basu san dalilin da yasa jaleel yaje garin cikin sirri ba,ko dai yana da labarin shukra tana can ne? Gashi babu dawakai da zasu iya hawa su qarasa cikin hanzari,kuma idan a qafa zasu tafi to sai sun kwana biyu a hanya,dukkansu cikin tunanin mafita suke,domin sun tabbata shukra zata nemi taimakonsu idan har sukai karo da jaleel,ya kamata su riga shi isa gareta amma ta yaya?

Kai-kawo yake tayi yana maimaita sunan
"Naseer TAEK?" Hakan yake ta maimaitawa,kanshi ya daga sama tare da tsayawa waje daya,ya furta
"Tabbas! Shi ne! Shine wanda ya shigar da qara wajen mai martaba a lokacin queen jaleela tana qwarqwara" da hanzari ya bar wajen,aikawa yayi a kirawo masa eunuch din da ya kawo wasiqar naseer dazu,zuwanshi wajen ya rusuna ya gaishe da jaleel,cikin hanzari yace masa
"Ina wasiqar da naseer TAEK ya bayar akai masa cikin birni? Je ka kawo min ita"  rusunar da kai yayi
"Yes my lord" sannan ya juya ta tafi,jim kadan ya dawo da wasiqar a hannunsa ya miqawa jaleel,bude wasiqar jaleel yayi kafin ya fara karantawa eunuch din yace
"Amma yallabai! Hakimi ne kadai yake iya karanta wasiqun,shi kadai doka ta bawa dama" harara ya wurga masa
"Fita ka bani waje!" Rusunar da kai ya qara yi
"Amma yallabai...." Katse shi jaleel yayi
"Umarni na kake qoqarin takewa? Ka fita nace!" Ya qarasa cikin tsawa sosai,sum sum eunuch din ya fita daga office din,shi kuma ya mayar da kanshi domin karanta wasiqar 🥺🥺
Yanayin fuskarshi ne ya canja lokaci guda zuwa mamaki,firgici da kuma tashin hankali,cikin kidimewa ya furta
"Shukra?" Dudduba takaddar ya cigaba dayi
"Shukra Malak! Ta yaya hakan zata kasance? Dama tana raye duk tsawon lokacin nan? Tana nan garin? Wai ita wace iriyar mayya ce?" Ya qarasa maganar cikin bacin rai.

Fitowa yayi farfajiyar wajen fuskarshi duk ta jiqe da gumi ya juya bayansa,da sauri yaranshi suka qaraso wajen cikin girmamawa,ba tare da ya juyo ya kalle su ba yace
"Shukra! Wannan mayyar yarinyar! Tana nan a raye a cikin garin nan!" Da mamaki babban yaron nashi yace
"Me? Tana nan?" Juyowa yayi ya kalleshi
"Ehh tana nan,hakan ya nuna baku yi mata raunin da zai kashe ta ba" rusunar da kai yayi
"Kayi haquri my lord" mari ya kwada masa har sai da ya hantsila,tashi yayi ya qara tsayawa akan qafarsa tare da qara cewa
"Kayi haquri my lord" kawar da kanshi yayi
"Yanzu yanzu! Tana gidan directa BYUN muje mu dauko ta ku kashe min ita!"
"Yes sir" suka ce.

Da qullin kayanta a hannu ta shirya barin garin a cikin daren,ta fito daga daki kenan bata kaiga fita daga gidan ba taci karo da director,cikin bacin rai yace
"Dama kwana biyun nan bana ganewa lamarin ki! Ashe shirin guduwa kike yi?" Cikin tsananin tashin hankali tace masa
"Kayi haquri ka barni na tafi! Akwai abu mai muhimmanci da ya kamata nayi a cikin birni! Ka taimaka"
"Qarya kike yi! Na taimaki rayuwarki shine zaki ci amana ta?" Roqonshi ta fara yi
"Kayi haquri,kamar yadda na fada maka ni palace maid ce! Akwai abinda ya kamata naje na sanar dasu,ka taimaka ka barni....." katseta yayi cike da masifa
"Dalla rufe min baki da zancen masarautar qarya! Tunani kikeyi zan yadda da wanann qaryar taki ne?"
"Mutumin da kake taimakawa yana shirin yin babban laifin cin amanar qasa,idan ka cigaba da taimakon jaleel kaima zaka taya shi aikata laifin"
"Yi min shiru! Kin san me kike fada kuwa? Ke kin isa ki san waye jaleel?" Marairaicewa tayi
"Ka taimaka ni dai ka barni na tafi! Ya kamata mahukunta su san halin da ake ciki! Ka taimaka min"  kauda kanshi yayi alamar ba zai ma kula abinda take fada ba,ta bude baki zata cigaba da roqonsa kenan tajiyo muryar da ko a mafarki ba zata manta da ita ba
"Ke!!!! Shukra malak! Ashe kina nan a raye a cikin garin nan!" Zaro ido tayi tana kallon mai maganar har ya qaraso gabanta ya tsaya yana kallonta ido cikin ido,yayinda directa mutuwar tsaye yayi da yaji jaleel ya kira cikakken sunanta,kallon cikin idonta jaleel yakeyi da kyau,itama kuma ta qura masa ido
"Ya akayi? Ta yaya? Ta yaya kike raye? Ya akai kika zo garin nan?" Idonta har ya fara cika da qwalla ta qanqame qullin kayan da yake hannunta
"Ke wace iriyar mayya ce?  Kenan kina nan a boye duk tsawon lokacin nan! Ku kama min ita!" Ya qarasa maganar cikin tsawa da bacin rai,tahowa sukai zasu kamata director ya kareta ya tsaya a gabanta,tambayar jaleel yayi
"Me yake faruwa haka my lord?" Cikin qaraji jaleel ya daka masa tsawa
"Zaka matsa daga wajen ko sai na kashe ku tare? Nace ka matsa! Ku kuma ku kamo min ita" kamata sukai suka tafi da ita tana ta ihun kiran sunan director,jaleel ne ya tsaya ya yanka masa kashedi cikin tsananin bacin rai,fuskar nan tashi taji jajir
"Baka ga komai ba a cikin daren nan! Kada naji labari a wani waje! Kaji ko?" Jinjina kai yayi da sauri sauri,jaleel ya kama hanyarsa ya bar gidan yabi bayansu shukra.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now