Page 58

114 5 0
                                    

Page 58

"Jaleel? Kace an kama shi?" Ministan tribunal yake tambayar jameel da yanzu ya kawo masa labari,jinjina kai jameel yayi
"Royal guards ne suka kama shi awanni biyu da suka wuce" runtse ido minista yayi tare da girgiza kai
"Amma menene laifin da ake tuhumarsa dashi?" Kauda kai jameel yayi gefe
"Akan maganar queen haneefa ne" minista daurewa kawai yakeyi
"Shikenan yanzu komai yazo qarshe! Idan har an gano cewar yana da hannu a cikin korar queen haneefah to lallai itama queen jaleela tana cikin matsala kuma muma ba zamu tsira ba,ina ganin qarshen mu ne yazo gaba dayanmu 'yan kudu"

Jaleela tana zaune sai tunane tunane takeyi,zuwa yanzu zuciyarta ta tabbatar mata cewar mai martaba ya hadu da shukra shiyasa yayi mata wulaqanci ranar nan da daddare bayan ya dawo,a hankali ta bude baki cikin sanyin murya tace
"Tabbas duk wannan abin aikin shukra ne! Ta bawa mai martaba hujjojin da tazo dasu,hakan yasa ya sakawa yayana tarkon da suka kama shi" chief maid sunkuyar da kai tayi
"Yanzu your majesty komai yazo qarshe kenan?" Kamar mai rada tace
"Ta yaya mai martaba zai yi min haka? Ku shirya yanzu akwai inda zamuje" ta qarasa maganar cikin murya mai amo.

Chief eunuch cikin farin ciki ya shigo wajen mai martaba,rusunar da kanshi yayi tare da sanar da mai martaba cewar shukra ta farfado,cikin murna kamar yaro ya tsinci alawa mai martaba ya tashi tsaye yace masa
"Da gaske? Ta tashi?" Qunshe murmushin sa chief eunuch yayi tare da gyada kai yace
"Tabbas ta tashi kuma har ta samu qwarin jikinta ma,ko a yi maka shirye shiryen zuwa ganinta?" Cikin farin ciki zai bashi amsa sai kuma yanayin fuskarshi ya canja
"A'ah ba sai na ganta ba kawai" cikin rashin fahimta chief eunuch yace
"Amma your majesty ya kamata ta kasance tare da kai" kai tsaye mai martaba ya gane abinda chief eunuch yake nufi,harararshi yayi
"Kaji ka kai kuma! Ka bari dai kawai yanzu rashin zuwana shine mafi alkhairi domin mun dauki layin hukunta masu laifi,hakan zai iya sawa a dinga bibiyar duk motsina har a gano inda take" jinjina kai chief eunuch yayi bai ce komai ba,mai martaba yace
"Tana cikin raina amma zanyi haquri da zuwa ganinta har zuwa wani lokaci"
Chief eunuch yana fita ya dawo,tare da rusunawa yace
"Cheo-na! Her majesty tana buqatar ganawa da kai" da mamaki yace
"Queen?"
"Yea cheo-na!"
"Je ka shigo da ita"
"Yea cheo-na" chief eunuch ya qara cewa sannan ya fita,yana fita ta shigo hakan yasa mai martaba tasowa daga kujerar sa ya dawo inda wasu kujerun suke da tebur wanda suke kusa da qofar shigowa,kallon kallo suka tsaya yi
"My queen! Ki zauna" ya fada mata fuskarsa ba yabo ba fallasa,zama tayi a hankali tace
"Cheo-na! Yau ka barni na ganka! Meyasa? Ko don kana da abinda zaka tambayeni ne?" Bai ce mata komai ba sai ido da ya zuba mata
"Ka taimaka ka sa a saki yayana your majesty! Bai taba qoqarin yiwa queen haneefa sharri ba,ba shi da laifi your majesty!" Ta fada cikin sanyin murya
"Ina da hujjojin da suke tabbatar laifinsa" ya fada mata kai tsaye
"Ehh nima na san kana dasu,na san sune hujjojin da shukra ta kawo maka" yayi mamakin jin haka a bakinta amma bai nuna mata mamakinsa ba
"Yanzu kenan komai zai faru ne yadda yarinyar nan ta tsara? Da kalamanta kawai zakai amfani? Ni kuma fa? Ita kadai ce zata iya fada maka gaskiya,yayinda kake tunanin cewar ni qarya zan yi maka? Har maganarta ta isa tasirin da zata jefa yayana cikin kurkuku ba tare da hujja ba? Amma ni magana ta tana buqatar bayyananniyar hujjar da zata tabbatar bashi da laifi?" Dauke idonsa yayi daga kallonta,domin ta fara cin nasarar abinda ya kawo ta,zuciyarsa tana matuqar sonta hakan yasa kalamanta suka fara huda zuciyarsa,ajiyar zuciya ta sauke
"Idan har akwai sa hannun yayana a cikin yiwa queen haneefah sharri,toh lallai zan sani,kuma idan har da gaske na sani din,baka ganin cikar adalci shine nima ka jefa ni cikin kurkukun?"
Jikinsa ya fara sanyi
"Yanzu idan na tambayeki ko kina da masaniyar abinda yayanki ya aikata,me zaki ce min?" Ya fada yana kallonta a cikin ido,idonshi ya qanqance sosai,yayinda ita nata idon ya cika da ruwa
"Yanzu amsata tana da muhimmanci haka a wajenka? Ko da gaskiya zan fada maka ko qarya zan fada,ai ka sawa ranka maganar shukra kawai zaka yadda da ita" bai ce mata komai ba,har yanzu idonshi yana cikin nata,sauke idonta tayi qasa
"Ni da yayana bamu da laifi your majesty! Ka yadda dani! Nice sarauniyar wannan qasar wacce ka zabeni da hannunka" dago idonta tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kanta
"Ni zan tafi your majesty!" Ta fada cikin matuqar sanyin jiki,cikin yanayin da za'a tausaya mata matuqa sannan ta miqe ta nufi hanyar fita
"Jaleelah" ya kira sunanta,tsayawa tayi cak amma bata juyo ba
"Har yanzu lokaci bai qure miki ba!" Da mamakin jin haka daga bakinshi ta juyo ta kalleshi,miqewa yayi tsaye shima
"Matuqar kika sanar dani gaskiyar a yanzu,na san ba zan iya boye laifin ki ba amma zuciyata zata yafe miki! Saboda haka na roqeki...."
"Banyi maka komai da zan nemi yafiyarka ba! Wannan shine kawai abinda zan iya cewa your majesty!" Ta katseshi cikin dakewa sannan ta sa kanta ta bar wajen.
Tana fitowa bakin qofar wajen ta fara jan qafarta da qyar saboda yadda gwiwarta ta sage da maganganun da suka yi,wasu hawaye masu zafi ne suka zubo mata,tsayawa tayi da tafiyar a zuciyarta take fadan
"Your majesty! Abinda baka sani ba shine,inda ace zan samu soyayyar ka ta dawo kamar yadda take da! To lallai zan iya amsa laifin da ba ni na aikata shi ba,amma a halin yanzu ba zan iya amsa wanda na aikata ba ma,saboda haka kada ka manta da cewar kaine silar zamana haka! Kaine silar canjawar halina! Kaine sila" kukan ta cigaba har da sheshsheqa yayinda shi kuma bayan fitarta zama yayi yana tunanin maganganun su,yana tuna iri kyawun halinta da kuma irin soyayyar da ya nuna mata.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now