Page 42

62 5 0
                                    

Page 42


Da hanzarin su suka taho har da sumayya,don tana son tazo taga yadda aikinta ya fara samun nasara,nadeeyah cikin kulawa ta matsa kusa da shukra tana dudduba ciwon da aka ji mata,sumayya kuwa ta qame daga gefe tana qare mata kallo,basma itama jajantawa shukra takeyi cikin tausayawa,summaya ta tabe baki
"Ai ita ta jawo wa kanta,saboda tsabagen karambani irin nata" kowa ya dawo da kallonshi kanta,basarwa tayi ta cigaba da maganar ta
"Ai da kin tsaya iya matsayinki da basu yi miki hakan ba,don mu dai a tarihi babu lady inves din da suka taba yiwa haka" shukra da tunda sumayya ta fara magana take kallonta cikin zafin murya tace mata
"Yanzu kina nufin nayi shiru na qyale su bayan na ga kuskure a tattare da su? A koda yaushe kuna horar damu domin mu zama masu gaskiya da riqon amana,amma ta yaya zaki ce haka?" Hararar ta sumayya tayi
"Ai sai kiyi tayi,ai dama ba hana ki zan yi ba,kina sane da cewar kamar yadda muke jagorantar inner court haka suma eunuch su suke jagorantar palace dinnan,wace riba zaki ci idan kika bata musu rai? Kiyi ta yi,ruwanki!" Tana gama fada mata haka ta fita daga office din,tunda ta gama abinda ya kawo ta.

Waahegari da safe bayan ta sha magunguna taji sauqin jikin nata sosai,cikin shirin uniform dinta tazo police bureu,IG ya fito shi da 'yan bayansa suna tsaye ya hango ta,kiran sunanta yayi
"Shukra!" Juyowa tayi,da hanzari ta qaraso gabansu ta gaishe su,cikin kulawa ya tambayeta
"Lapia na ganki anan da sassafen nan?" Girgiza kai tayi
"Ba komai,kada ka damu,kawai dai nazo neman shawarar ka ne akan wani abu" kallon tsanaki yake mata,jin yarinyar yakeyi kamar 'yar cikinsa,yace
"To taho muje office" bin bayanshi tayi har cikin office dinsa,ya nuna mata wajen zama ta zauna sannan ta fara yi masa bayani
"Dama aikin duba da muka saba yi ne aka kaini royal treasury" hankalinsa sosai ya mayar kanta,cikin mamaki yace
"Royal treasury kuma? Wajenda eunuchs ne suke jagoranta? Ya za'a yi kina palace maid su barki kiyi aikinki?" Jinjina kai tayi
"Hakane,na samu wannan matsalar sosai,amma abinda yafi damuna shine a lokacin da ina duba littafin records dinsu,sai na ci karo da wani abin mamaki"
"Abin mamaki kuma?"
Jinjina kai tayi domin tabbatar wa
"Ehh domin na gano cewar a cikin kudade da aka fitar dasu a sace,a cikinsu ne akayi amfani aka biya doctor NUH na case din tonic din queen dowager"
"Me?!" Ya fada cikin mamaki da firgici
"Kin tabbatar?"
"Ehh kuma ina ji a jikina kamar mafi yawan mason kudin ya tafi ne ga consort hui,ina tunanin sunyi amfani da kudin ne domin biyan wadanda suka taimaka musu wajen hada tuggun" wani huci IG ya fitar mai zafi,shukra ta cigaba da magana
"Ina ganin idan har muka bayyana wannan gaskiyar,zamu iya wanke queen haneefah daga qazafin da akayi mata" ajiyar zuciya ya sauke,ya kalleta
"Bayan ke,waye ya san wannan maganar?" Girgiza kai tayi
"Ban fadawa kowa ba"
"Da kyau,domin idan wanda bai kamata suji ba,suka ji wanann zancen lallai zaki fada cikin gagarumin hatsari,saboda haka kada ki fadawa kowa maganar nan har sai munga abinda hali yayi" ajiyar zuciya ta sauke
"Toh amma fa idan har zamu tono gaskiya ya zama dole mu binciki royal treasury,amma sai dai ni bani da qarfi akansu! Menene shawarar ka?" Shiru yayi tare da fadawa gajeren tunani,kafin yace
"Nima kaina royal treasury yafi qarfina! Amma taso ki biyo ni" tashi yayi itama tabi bayansa suka fita.

Jaleel ne shi da shugaban royal treasury suna ta hira suna nishadi,ga tebur a gabansu da kofin shayi,Eunuch dinnne yace
"Nagode yallabai da ka samu lokacina yau!"dariya jaleel yayi mai sauti
"Ai ka cancanci komai a wajena,don yanzu ma maganar da nake maka her highness itama tana son ganinka" washe baki yayi,jaleel ya cigaba da magana
"Ai na bata labarin irin taimakon da kai tayi min tsawon shekarun nan" dariya eunuch yayi
"Ai ba komai,saboda ita ne ai,shiyasa nayi duk abinda nake ganin yana cikin ikona,bai fi qarfina ba domin nasarar ta!" Hirar su suka cigaba dayi suna ta dariya,duniya tayi musu dadi.

A qofar wani gida suka tsaya,IG bai ce mata komai ba,ganin sunyi 'yan mintuna suna tsaye yasa tace masa
"Muna jiran wani ne?" Jinjina kai yayi
"Ehh akwai wani abokina tun muna makaranta,shine minister na 'yan sanda,ina ganin zai taimaka mana" basu gama magana ba ya fito,da murna ya tari IG da cewa
"Chief SUH" murmushi yayi masa,suka gaisa sannan ya nuna masa shukra
"Wannan itace lady investigator Shukra Anas Malak,mun zo ne saboda ka bamu shawara akan wani al'amari,shin ko zaka iya sauraron bayanin ta?" Jinjina kai yayi
"Ba damuwa,mu shiga daga ciki ko?" Binshi sukayi ciki domin yi masa bayanin abinda ya kawo su.

Washegari da safe a office of investigation 'yan matan ne a tsaitsaye kowa yana hada takaddu,Aliya tace
"Ni na gaji wallahi,na qagu mu gama wannan aikin saboda goge-goge kullun" sameerah ce cikin tsiwa tace
"Ai hakan ne ya dace dake! Ba ke me tsinin bakin cewa kina son akaiki wajen kyawawan samari ba?" Ta qarasa maganar tana hararar Aliya,Shukra da ta gama abinda take yi ta daga kai tace musu
"Ni na tafi! Sai..." bata qarasa maganar ba basma da shigowarta kenan ta tsayar da ita
"Ke! Ba dai royal treasury zaki ba ko?" Tsayawa shukra tayi da murmushin ta,tace
"Can zan tafi my lady!" Kwabe fuska basma tayi
"Amma dai baki da hankali ko? Idan suka qara dukan ki fa?" Dariya ta bawa shukra yadda tayi maganar,
"Ai aikina ne,ba yadda za'a yi naqi zuwa,kuma ai ba zan qara barinsu su dake ni ba,sai na rama kawai" ta qarasa maganar tana dariya,basma ce ta kwabe ta
"Ke wai waye yake miki wasa a nan?" Wata dariyar shukra ta saka
"Toh shikenan tunda ni ba zan iya ramawa ba,sai in tafi da Aliya ta rama min,ai ita tana da qarfi" tayi ficewarta ta barsu a tsaye kowa yana mamakin qarfin halinta.
Basma ce tacewa sauran 'yan matan
"Ku taho muje,dole mu tsayar da ita!" Fitowarsu kenan gaba dayansu sai ga nadeeyah da Afrah suma,yadda suka ga su basma cikin hanzari yasa nadeeyah cewa
"Sai ina?" Basma ta bata amsa da
"Shukra ce ta kama hanya ta tafi royal treasury,kuma nasan in dai bamu dakatar da ita ba to Allahi ne kadai ya san yau me zata janyo mana" zaro ido nadeeyah da Afrah sukayi cikin mamakin jin shukra ta koma inda aka lakada mata duka.

A tsaye a bakin qofar royal treasury shukra ce suke ta tababa ita da eunuch din da ya shigo da ita ranar farko,roqonsa take cikin girma da arziqi ya matsa mata ta shiga,da mamaki yace mata
"Lallai yarinyar nan! Ke wace irin mara hankali ce? Bayan abinda mukai miki ashe zaki iya qara waiwayar nan wajen" rusunar da kanta tayi kamar tijarar da yake mata bata dameta ba tace
"Na roqeka ka bani hanya na wuce,domin ni aikina kawai nazo yi"
"Ke! Dalla gafara can! Ina ganin yau ma sai mun qara yi miki yaren da kika fi ganewa...." Maganar ce ta tsaya a maqogoronsa yayin da yaga ayarin 'yan office of investigation,nadeeyah da basma a gaba sai 'yan matan a baya,cikin rawar murya yace
"Mad....am nadee....ya me ya kawo ku nan?" Cikin dakewa fuskarta babu alamun wasa tace
"Munzo ne domin mu bincike ku! Kuma akan wane dalili ne zaka hana lady investigator shiga?" Ji yayi kamar an zuba masa ruwan sanyi a jikinsa,don bai taba tunanin akwai ranar zata zo da za'a yi musu irin haka ba,shugaban eunuchs din ne ya qaraso wajen cikin tsare gida yacewa nadeeyah
"Ku dakata tukunna! Ta yaya zaku shigo kuce zaku bincike mu saboda kun raina mu? Lallai yanzu zanyi maganin ku!" Da hannu yayi alama,nan da nan kuwa royal guards suka matso,yace
"Ku fitar min dasu" jan su Aliya aka fara yi suna qwace hannayensu za'a fitar dasu daga wajen
"Ku dakata!" Suka ji murya daga sama,juyawa kowa yayi suka ga chief eunuch ne,chief steward (shugaban eunuchs din royal treasury) ya fara tsilli tsilli da ido,kowa da kowa a wajen rusunar da kanshi yayi har da tawagar 'yan matan,gyaran murya chief eunuch yayi tare da fara magana yana kallon chief steward
"Akan wane dalili ne zaku dinga hatsaniya haka? Har sawa akai royal guards su fita da investigators? Toh ku taho mai martaba yana neman shuwagabbanin ofishoshin biyu,royal secretary da office of investigation yanzu yanzu" ba chief steward ne kadai ya firgita da maganar ba,hatta dukkan stewards (eunuchs) da suke wajen duk sai da suka tsorata jin maganar taje wajen mai martaba.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now