Page 13

61 6 0
                                    

Page 13

Tun yammacin da aka fara azabtar da shukra babu tausayi babu imani,daureta akayi akan kujera a bakin office din chief madam inspector,ba ruwa babu abinci tana zaune amma babu wata uquba bayan wannan,har yanzu amsarta daya ce cewar babu wanda ya sata shigo da magani cikin masarautar.



Sameer da manager hankalin su yayi qololuwar tashi kuma gashi babu abinda zasu iya yiwa shukra a wannan halin,tahowa sukayi qofar office of investigation,idan masu karatu basu manta ba,office of investigation yana cikin gidan mata ne inda ba'a shiga sai mai martaba kawai sai kuma wanda aka bawa izinin hakan,cike da tashin hankali manager ya kalli sameer yace

"Ya kamata mu bar wajen nan kafin wani ya ganmu"

Sameer ba tare da ya juyo ba ya mayar masa da amsa

"Yallabai shukra fa tana ciki,ko ma yanzu sun kashe ta oho"

Hannu manager ya saka ya doke bakin sameer tare da cewa

"Kul ka qara fadan haka,amma dai ina jin tausayin yarinyar nan don babu wanda zai damu don ta amsa laifin da ba nata ba"



A quaters din lady jalila itace zaune a inda ta saba zama sai mariqinta minister na tribunal yana fuskantar ta,cikin tsanaki tace

"Hakan nake nufi minister,zanje na miqa kaina a office of investigation "

Cikin razani bakinshi na rawa yace

"My lady idan kikayi haka zaki sa mai martaba cikin wani hali,za'a dinga cewa an kama matar da ya fiso da qoqarin kashe sarauniyar shi,kuma a wannan lokacin ko shi ba zai iya yi miki komai domin dokar qasa ba zata bashi wannan damar ba,ki duba dai My lady!"

A tsanake tace masa

"Kayi haquri amma abinda zanyi kenan,ba zan iya zuba ido ana azabtar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba,ni matar sarki ce basu isa suyi min yadda sukai mata ba,kuma tunda nasan ban sa an shigo da pinellia ba,na san gaskiya zatai halinta"

Haka minister ya cigaba da bata baki,ba tare da ta qara ce masa komai ba har suka gama magana ya tafi.

A quaters din queen dowager jikinta da sauqi,mugun nufi ya sata ta qarfafa jikinta ta shirya tsaf cikin kayanta na alfarma,da kuma alkyabbar ta mai dragon 🐉 a zaune take a sitting room dinta,a gabanta kuma minister of state affairs ne a durqushe,cike da ladabi yake ce mata

"Your majesty komai ya kammala"

Fuskarta cike da mugun nufi tace

"Ka tabbatar wannan karon ba'a samu matsala ba"

Qara rusunawa yayi yace

"Komai yana tafiya daidai yadda muka tsara your majesty ki kwantar da hankalinki"

Jinjina kai tayi ta maida idonta kallon waje daya,tana kimtsawa kanta abinda ita kadai ta san menene.



A office of investigation chief madam ce take cewa shukra

"Da alama bakya son rayuwar ki,ki fadi abinda ake buqata ki bar wajen nan kema ki huta amma kinqi ko?"

Shukra ta bude baki cikin yunwa da qishirwa tace

"Magana ta daya ce,banyi hakan akan unarnin kowa ba kuma babu pinellia a cikin abinda na shigo dashi" ta qarasa da qyar.

"Nice nan na saka ta shigo min da maganin"

Dukkansu suka kalli daga inda maganar ta fito,da mamakinsu lady jalila ce,chief madam da sauri ta qarasa inda take ta tsaya,dan rusunar da kanta tayi kamar an mata dole tare da cewa

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now