Page 47

97 5 0
                                    

Page 47

"Na sanki tsawon lokaci mai yawa! Nafi kowa sanin wacece ke! Kuma kema kinfi kowa sanin wanene ni! Hakan ya kamata na yadda dashi" bata ce komai ba,kuma bata nuna wata alamun tsoro ko firgici ba,cigaba yayi da magana
"Haka nan kuma ban yadda cewar shukra haka kawai zata tsara yi miki sharri ba tare da wata qwaqwqwarar hujja ba" yanzu ne hankalinta ya dan fara tashi
"Kenan ni zan iya yin hakan? Me zuciyarka take fada maka game dani?"
"Jaleelaah!" Ya kira sunan ta cikin wani irin yanayi,ta kuma manta yaushe rabon da taji hakan a bakinshi
"Fada min your majesty! Ka tambayeni abinda kake son sani! So kake ka tambayeni ko na aikata ko? Ko ba haka ba?" Shiru yayi mata yana karantar yanayin ta
"A'ah your majesty! A'ah! Ban taba yi maka qarya ba,wannan shine gaskiyar" kallonta kawai yake yi
"Nan ba da dadewa ba,za'a nada min sarautar sarauniyar joshun,amma idan har baka yadda dani ba,kana kokonto a kaina,ya kamata ka tsayar da komai haka,idan baka yadda dani ba ai hakan ba laifinka bane,laifi na ne,Ko kadan ba zanga laifin ka ba!" Ta fada da bacin rai a cikin idonta,ita a lallai ya bata mata rai tunda bai yadda da ita ba,sai da ya gama karantar yanayinta sannan ya tashi ya fita ba tare da ya ce wani abu ba,hannunta ta saka ta damqe skirt dinta hawaye ya zubo akan kumatun ta.

Haj jameela ta kasa tsaye ta kasa zaune!
"Ji nake kamar zanyi hauka! Yanzu idan komai ya lalace fah?" jaleel da yake zaune a qasa yace
"A'ah hakan ba zai faru ba! Her highness ta jajirce tayi aiki tuquru akan haka,an haife tane domin ta zama sarauniya,kuma lokacin  yazo" dafe kanta tayi domin ciwo yake mata sosai har yanzu ji take ba zata iya zama ba don tsabar tashin hankalin da take ciki.

Washegari da safe,chief eunuch ne cikin hanzari ya fito ya aika wani eunuch ya kira chief secretary da sauri,chief secretary yazo ya shiga wajen mai martaba babu wanda ya san me suka tattauna,fitowa yayi kai tsaye RPB ya nufa wajen IG,sai da ya gama fada masa saqon mai martaba IG yace
"Na fahimta! My lord!" Ajiyar zuciya ya sauke
"Kayi haquri da irin saqon dana kawo maka chief Suh" jinjina kai kawai IG yayi.

Da sauri assistant director na tribunal ya shigo gidansu jameel,jameel yana zaune shi da mahaifin shi ya shigo da labari,cike da mamaki jameel ya kalle shi
"Da gaske kake? Mai martaba ya sauke chief SUH daga matsayin shi?"
"Ehh hakane yallabai,yanzun ma daga RPB nake domin tabbatar da hakan" jameel ya kalli minister
"Baaba!" Ya fada cikin murna,minister ya bugi tebur din da yake gabansa
"Mai martaba ya zabi yabi bayanmu mu da consort hui"
"Komai ya tafi yadda muka tsara! Congratulations your excellency!" AD tribunal ya fadawa minister,sannan ya juyi ya kalli jameel
"Congratulations sir"
Murna suke gaba dayansu cikin farin ciki da nishadi.

IG ne a office yana ta tattare litattafansa,lieutenant ne yace masa
"Yallabai! Yanzu tafiya zaka yi?" Jinjina kai IG yayi,assistant lieutenant yace
"Yallabai bai kamata mai martaba ya koreka ba! Gaskiya hakan rashin adalci ne!" Baice musu komai ba,yana ta harhada kayansa
"Zan bika mu tafi!" Lieutenant ya fada
"Nima zan bika mu tafi" AL shima ya fada,girgiza kai IG yayi
"A'ah ba zaku bini ba! Domin zan dawo" kallon rashin fahimta sukai masa
"Ehh zan tafi ne yanzu domin na samu damar dawowa! Ba zan dawo ni kadai ba,zan nemo shukra duk inda take domin mu dawo da cikakkiyar hujjar da zata kifar dasu! Ku kuma zaku yi haquri har lokacin da zan dawo,duk da nasan hakan zai muku wahala,domin yanzu sune zasu yi abinda suka ga dama a garin nan saboda suna ganin yanzu duk wata matsalar su ta qare! Amma ba zamu barsu su juya RIGHT POLICE BUREU yadda suke so ba!" Ya qarasa da murmushi a kan fuskarsa,kamar ma dai korar tashi daga aiki bata dame shi ba.

Jaleel ne a qofar gida,wata baiwar haj jameela ta rako shi waje inda aka ajiye wata kujera da manyan masu kudin garin suke hawa,kujerar tana da mariqi guda hudu wanda qartan maza suke dauka sukai mutun inda zaije,baiwar ce tayi masa "a dawo lapia" sannan ta shige gida,juyowa yayi ya kalli masu daukan kujerar yace
"Palace zaku kaini! Zanje naga her highness"
"Zaka fara ganina tukunna kafin kaje chan!" Juyawa bayanshi yayi domin ganin mai maganar,tahowa yayi har gabanshi ya tsaya
"Kai kuma me kake nema? Na san dai ba kashe ni kazo yi ba,tunda ba daddare kazo ba" jinjina kai abdullahi yayi idonshi a bushe babu digon tausayi yace
"Ehh ba kashe ka nazo yi ba,don ba zan bari ka mutu da wuri kuma cikin sauqi haka ba!" 'Yar gajeriyar dariya jaleel yayi
"Hahhaahaha me hakan yake nufi?"
"Shukra bata mutu ba!" Abdullahi ya fada,Zaro ido jaleel yayi cikin tsoro,ganin haka abdullahi yace masa
"Ai kaima baka samu gawarta ba! Ka jira ranar da zan dawo tare da qanwata,kafin nan kayi yadda kake so,amma ka sani duk ranar da muka dawo tare to kashinku ya bushe" huci jaleel yakeyi domin ya shaqa sosai,kuma gashi babu abinda zai iya yiwa abdullahi,a nan abdullahi ya tafi ya barshi a tsaye yana hucin baqin ciki.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now