Page 29

84 5 0
                                    

Page 29

Abdullahi a bakin ruwa,shi da wani mai tuqin jirgin ruwa,tsabar kudi ya dauko ya bashi tare da cewa
"Jaleel ya fada maka zuwana ko? Zamu qaraso wajen qarfe tara" tare da juyowa hanyar gida,shukra tana dakin shi a zaune,tasa kayan da ya gama hadawa a gaba tana kallo,tana tunanin zuwansu nadeeyah zuwa wajen IG,a daidai lokacin da suke magana itama taje wajenshi,tana zuwa bakin qofa taji nadeyya tana cewa
"Yanzu kenan sai dai mu miqa musu shukra su tafi da ita? " IG ya bata amsa da
"Rudanin da mai martaba yake ciki kenan,amma abin ya girmama sosai" da jin haka sai ta kasa qarasawa ciki kawai ta koma,tana ta tunanin ta dai har ta tsayar da matsayar ta,tashi tayi ta lalubi brush din rubutu da takadda,tayi rubutu ta fito da takaddar a hannunta,sameer ta gani a tsaye a tsakar gida ta bashi tare cewa
"Ka bawa yayana idan ya dawo" ba tare da ta tsaya jin abinda zaice mata ba tayi tafiyarta.
Tsayawa sameer yayi yana ta kai-kawo a tsakar gidan har Abdullahi ya dawo,cikin alhini ya miqa masa takaddar tare da cewa
"Me yasa baka dawo da wuri ba? Abu ya baci sosai,shukra ta bayar da wannan a baka" cikin hanzari ya karbi takaddar ya bude,ganin abinda ta rubuta a takaddar yasa qwalla ta zubo a idonshi wani na bin wani duk bai san da suna zuba ba.

Zuwan chief eunuch office of investigation yasa aka lura da cewar shukra bata nan tun da rana,neman duniya akai mata amma ba'a ganta ba,hakan yasa lady sumayya ta tara 'yan matan a wajen assembly tare da cewa
"Zaku fita zuwa cikin gari lungu da saqo ku nemo shukra,zai iya kasancewa guduwa tayi,royal guards ma zasu taya ku nemanta" kowa ranshi babu dadi,domin in har ta tabbata guduwar tayi to lallai bala'in sai yafi wanda ake ciki,nadeeya ce ta bullo ta bayan sumayya tare da cewa
"Babu buqatar a tafi nemanta,domin na san inda take" kallone gaba daya ya dawo kan nadeeya,kuma bata tsaya yi musu bayani ba ta wuce ta shiga office,ganin haka lady sumayya ta sallami 'yan matan tabi nadeeya office domin jin inda shukra take.

Mai martaba cikin tashin hankali ya miqe tsaye tare da dakawa chief eunuch tsawar da bai san yayi ta ba
"Kace me? Shukra bata nan? Tana wajen Wakilin sarkin china? Waye yayi hakan ba tare da izini na ba?" Sunkuyar da kai chief eunuch yayi
"Labari yazo akan cewar ita takai kanta,ta aikowa daya daga cikin madam investigators takadda da take tabbatar da ita ta miqa kanta da kanta"

Cikin mamaki wakilin sarkin china yake kallon sojan da yake gabanshi
"Kace tazo nan wajen da kanta?" Rusunawa sojan yayi
"Ehh tazo tana waje,idan ka bada izini za'a shigo da ita" izini wakili ya bayar aka je aka taho da shukra har gabanshi,da zuwanta ta tsaya daidai tana fuskantar shi ta rusuna ba tare da tace komai ba,kallon wulaqanci yake binta dashi,daga bisani yace
"Wannan ce yarinyar kenan" qara rusunawa tayi
"Ehh hakane,ni ce lady investigator din da kake nema" jinjina kai yayi domin mamakin qarfin hali irin na yarinyar nan,yace
"Kin san me zuwanki nan yake nufi ko? Zamu tafi dake domin sarkin china ya sa a bincike ki" dagowa tayi ta kalleshi da dan alamun tsoro a kan fuskarta,alamu yayiwa sojojin da hannu,suka taho suka rirriqe ta domin suje su kulleta kafin lokacin tafiyar su china,shi kuma ya juya domin barin wajen,jin muryarta da yayi da abinda take fada yasa shi tsayawa cak ba tare da ya juyo ba,tana ta kici kicin qwace kanta daga wajen sojojin da suke riqeta take cewa
"Ka bani lokaci kadan nayi magana da kai" daya a cikin sojojin ne yace
"Ke baki da hankali ne? Ku wuce ku tafi da ita" jan ta suka fara yi daidai lokacin da wakilin china ya juyo yana kallonsu,da hannu yayi musu alama suka saketa,ta qaraso gabanshi da sauri ta durqusa
"Kamar yadda kake tunanin shiri ne,tabbas kuwa shirin ne domin komai da yake faruwa shirya shi aka yi" kallon tsanaki yake mata daga bisani yace
"Kin san me kike fada kuwa? Kina nufin kin amsa cewar shirya komai kuka yi?" Shiru tayi tana zazzare ido,umarni ya bayar su kaita inda zata zauna,zai zo ya ganta yanzu.

Nadeeya tana zaune a office ita da Afrah ta rasa me yake mata dadi,basma ta shigo da gudu harda hawaye a idonta tare da Aliya a bayanta,zama tayi tana kallon nadeeya
"Yanzu nadeeya meyasa baki tsayar da shukra ba,me yasa kika barta ta tafi?"
Afrah itama abinda ta fada kenan
"Gaskiyane my lady,ita shukra ai aikinta kawai take yi,bai kamata ace an yadda sun tafi da ita ba" Aliya itama da tayi tubus cikin sanyin murya tace
"Gaskiyane,duk da bana jin ina son shukra a raina,amma hakan bai kyautu ba,ba'a yi mata adalci ba,indai aka bari suka tafi da ita"

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now