Page 24

54 4 0
                                    

Page 24

Mai martaba cikin fara'a yake tambayar chief eunuch
"Kace an qara bata damar yin jarrabawar?" Shima chief eunuch da murmushin ganin yadda mai martaba yake fara'a yace
"Ehh your majesty,zasuyi jarrabawar ne nan da kwana uku"
"Kwana uku? Kamar kwanakin sunyi kadan,ko yaya zatayi da karatu ita kadai?" Shi dai ya rasa meyasa yake tsananin farin ciki ko da tuna shukra yayi,shiyasa da ruwa yake dukanta yaji a jikinshi,har shima ya shiga ruwan ya dakeshi ba tare da ya san dalilin da yasa yake tsaye a cikin ruwan ba,sai daga baya da ya samu labarin yadda shukra ta kwana a bakin office of investigation,har yaje wajen queen haneefah domin ta shiga maganar,da murmushi akan fuskar sa yace
"Ina tunanin ranar da zata san ni sarki ne,kai bana son ma ta sani don nafi jin dadin zama da ita yadda ta dauke ni a haka" shi dai chief eunuch tun yanzu ya fuskanci mai martaba yana qaunar shukra ne ba tare da shi kansa ya fahimci hakan ba.

Cikin kwanakin shukra ta dage karanta littafin DOCTRINE OF THE MEAN sosai,ba dare ba rana,ana i'gobe zasuyi jarrabawar da daddare tana zaune tana ta karatu a fili,mai martaba ne yazo wajen ya dade a tsaye yana kallonta bata sani ba,daga bisani ya matso kusa da inda take,jin motsi ya sa ta dago kanta,ganin wanda yake tsaye tasa murmushi
"Yallabai kaine a nan?"
Murmushin shima yayi mata
"Ehh nine,na jiyo mutum yana karatu tsakar dare ne,ashe kece" bata fuska tayi zuwa kalar tausayi tare da cewa
"Jarrabawa zanyi gobe,kuma ina tsoro sosai ban sani ba ko zan iya ci" shima bata fuska yayi yadda tayi
"Kina tsoron ko zaki ci? Anya kuwa shukran ce? Har kika karaya haka? Ai kuwa akwai abinda nake son na fada miki saqon mai martaba ne,amma ki taso daga nan,domin akwai sanyi sosai" da sauri ta kalleshi
"Saqon mai martaba kuma? Me yace ka fada min?"
"Ki taho mu bar nan tukunna sai na fada miki" haka ta bishi a baya suna tafiya har cikin wani library mai shegen kyau,tsarin komai a ciki ma abin kallo ne,baki bude shukra ta kalleshi
"Yallabai nan din ina ne ka kawo mu?"
Murmushi yayi
"Nan royal library ne" hannu tasa tare da rufe bakinta cike da tsoro tace
"Amma yallabai,nan fa wajen karatun sarki ne da ahalinsa kadai,idan wani ya ganmu fah?" Dariya sosai ta bashi yanayin yadda tayi maganar,sai da yayi dariyarsa mai isar sa
"Kada ki damu,yau ai night duty nake anan shiyasa babu mai zuwa" da sauri ta tare shi
"Amma ya za'ayi dan sandan sirri yayi night duty a cikin palace?" Diriricewa yayi ya rasa me zai ce mata,da qyar ya lalubo abin fada
"Ai da yake ni shugaba ne shiyasa kullun ni nake night duty a nan" jinjina kai shukra tayi
"Au hooo amma ban taba tunanin ana haka ba" gudun kada ta qara jefo masa wata tambayar yasa yayi saurin cewa
"Maza ki zauna kiyi karatunki a nan cikin nutsuwa kuma kinga nan babu sanyi" gyada kai kawai tayi tare da zama a kujerar da ya nuna mata,shima zama yayi a wata kujerar tare da ce mata
"Kika ce kina tsoron ko zaki iya cin jarrabawar? Gashi kuma mai martaba ya fada min yana da tabbaci da qwarin gwiwar zaki ci" zare ido tayi tana kallonshi
"Mai martaban ne yace haka?"
Jinjina kai yayi
"Qwarai kuwa,da kanshi ya fada min haka,kinga kuwa idan yaji kin karaya tun yanzu ai ba zai ji dadi ba,kuma zaki bashi kunya" jinjina kai tayi tare da cewa
"Kuma haka ne fa,da gaskiyar ka yallabai,zan dage sosai naci jarrabawar nan ko don kada na bawa mai martaba kunya" murmushin jin dadin maganar ta yayi tare da cewa
"Yauwa haka nake son ji" janyo littafin nata yayi
"Kinga haddace duka littafin DOCTRINE OF THE MEAN ba zai yiwu a cikin kwanakin nan da kika yi ba,bari in duba miki wasu wuraren da zaki haddace da daddaren nan,ki dai tabbatar kin iya sosai don wata qila su iya zama tambayoyin jarrabawar " jinjina kai tayi tare da cewa
"Amma ni fa nayi karatu sosai,kawai dai bani da wanda zan karantawa yaji ko nayi daidai shiyasa nake jin kamar karatun bai zauna ba,amma kawo na gani" haka ya ajiye littafin yadda itama zata dinga ganin inda yake nuna mata,ya nuna mata wurare kusan guda shida a take ta haddace su yace ta karanto masa yaji,haka ta karanto masa har asuba suna wajen suna karatu cikin nishadi da farin ciki,daidai kiran sallar asuba ya tashi suka fito,ta wuce office of investigation shi kuma ya wuce grand palace.

Bayan gari ya waye,kowa ya hallara a wajen jarrabawa,gaba daya ladies investigators din suna wajen,yadda akayi waccan haka aka tsara wannan,su biyu ne akan benchin shukra da ruqayya,takaddun da aka rubuta abinda zasu karanta aka ajiye musu a gabansu,nadeeya ce tayi saurin cewa
"Rukayya ta fara" hakan yasa ruqayya ta miqa hannu ta dauki takaddar ta bude,a hankali ta fara karantowa,abinda yake cikin takaddar take ta maimaitawa kusan sau hudu,sai da nadeeya tace
"Ki cigaba ki karanto har qarshe sannan kuma kiyi bayanin ma'anar sa" gyada kai ruqayya tayi cikin sanyin jiki ta fara cigaban kamar bata da tabbacin ko daidai take yi ko ba daidai ba,haka dai ta kai har qarshe ta gama,nadeeya tace
"Ruqayya - pass" ta kalli shukra
"Saura ke" hannu shukra ta miqa ta dauki takaddar,tana budewa mamaki ya cika ta,murmushi ne a kwance a kan fuskarta tare da sa tafin hannunta ta rufe bakin ta cikin tsananin farin ciki,a ranta tace
"Wannan yana cikin wanda yallabai yasa na haddace jiya" bata gama maganar a ranta ba taji muryar nadeeya
"Zaki iya karantawa?" Nadeeeya ta tambayeta cikin tausasawa,da sauri shukra ta daga kanta sama,tare da sauke ajiyar zuciya,a nutse ta fara karantowa cikin qwarin gwiwa da murmushin farin ciki har qarshe ta dire tare da bayani,mamaki ne fal akan fuskar chief sumayya da kuma baqin cikin ba haka taso ba,yayinda nadeeya da basma suma mamakin suke amma cike da farin ciki,nadeeya tace
"Shukra - pass" jin haka yasa shukra jin dadi matuqa,a nan take maganar yallabai dinta ta fado mata,a hankali tace
"Yanzu na san yallabai zaiyi alfahari dani domin ban bawa mai martaba kunya ba"

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now