Part 2: Slavery

187 10 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤

ROYAL CONSORT
Korean inspired novel

©️ marriam mayshanu.... ✍️

Page 2


❤️  Part 2 : slavery (bauta)

Shekarar 1432 AD.

Wata 'yar matashiyar yarinya ce da duka shekarunta ba zasu wuce goma sha uku ba,daga ganin kayan da yake jikinta dai baiwa ce,sai dai inda take ta kai kawo ne ban ga wata mace a wajen ba domin duka tarin maza ne,duk kowanne a cikin uniform din aiki,bayi maza,da kuma ma'aikatan da suke aikinsu a cikin wajen.
Aikinta takeyi cikin walwala da girmamawa,kuma suma da dukkan alamu kamar sunfi son tayi musu hidima a maimakon sauran bayi maza da ake dasu a wajen.
Ma'aikatar jin dadi da walwala kenan dake cikin masarautar qasar JOSHUN.
A wannan ma'aikatar akwai masu aikin kid'a,waqa,da kuma 'yan rawa mata da maza,wanda aikinsu shine nishad'antar da gidan sarauta a yayin da ake wani shagali a cikin masarautar. Ma'aikatar ta kasance ne a wani 'bangare a cikin masarautar,kamar yanda mukai bayani a baya,masarautar tana da girman gaske da duk wata ma'aikata tana cikinta ne.
Shukra ta kasance ita kad'ai ce baiwa mace a kaf fadin ma'aikatar,kuma ta kasance tana aikin share share,goge goge,wanki,taimaka wa ma'aikatan da kayan sawa,ko takalmi ko hula ko kuma daukan kayan aiki daga wani wajen zuwa wani.
Abinda yafi bawa kowa mamaki game da ita shine,ba'a san daga inda ta bullo ba,kawai wayar gari sukayi suka ganta a cikin ma'aikatar tun tana yarinyar da bata fi shekara 7 ba,amma tana qarqashin kulawar shugaban ma'aikatar.
A zaune take tana kallon wata farar takadda da dukkan alamu tunanin ta yayi matuqar nisa,leqawa nayi domin naga menene a cikin takaddar,wani zane ne mai matuqar qayatarwa,na malam bud'a (butterfly) anyi masa kalar ja mai dan turuwa(maroon) ta samanshi anyi abin maqalawa kamar abin maqala mukulli (key holder) ta qasanshi kuma igiya ce mai beza bazar bazar haka,abin sha'awa kamar ka dauka don kallon farko sai ka zata ba zane bane akan takadda tsabar yadda yayi kamar abin gaske ne a zaune a kan takaddar.
Wani matashin saurayi ne ya taho da gudu ya na qwala mata kira
"Shukrah shukrah " yana fad'a yana nufowa inda take a zaune,saboda yadda tai nisa cikin tunanin ta ne yasa bata san yana yi bama har sai da ya qaraso inda take ya tafa hannayensa a kusa da fuskarta sannan ta dan zabura ta kalle shi,cikin girmamawar da zata bawa wanda yafi ta a shekaru da kuma matsayi a ma'aikatar ta kalleshi tace
" yaushe kazo nan banji zuwanka ba?"
Gyada kai yayi sannan ya zauna a qasa yana fuskantar ta yace
"Shukra,duk cikin ma'aikatan nan kinfi kusa dani akan kowa,na dauke ki tamkar qanwata ta jini,amma ke naga alamar kwata kwata baki d'aukeni hakan ba" zare ido tayi ta bud'e baki cike da sakarci tare da cewa
"Ba haka bane maigida (boss kenan,domin shi ma'aikaci ne,ita kuma baiwa a ma'aikatar),babu abinda yake damuna,lapia qalau nake" ta qarasa cike da inda inda.
Kallon tuhuma ya bita dashi tare dasa hannu ya karbi takaddar hannun ta,ya dade yana nazarin abinda yake zane a kan takaddar kafin daga bisani ya dago kai ya kalleta,itama shi take kallo,yace
"Duk yadda akai akwai wani abu na rayuwarki da yake da alaqa da wannan abin saqala muqullin(key holder),amma tunda baki son ki fada ni ba zan yi miki dole ba,abinda nake so dake kawai shine ki rage zama ke kadai kina tunani don hakan zai iya zama illa ga nutsuwarki da ma rayuwarki gaba daya,ki manta abinda ya faru dake a baya domin ko baki fada ba,rayuwarki ta baya ce take saki a cikin wannan yanayin,ki fuskanci ta gaba"
ya qarasa tare da dora fuskar tausayi yana kallonta,murmusa wa tayi sannan tace
"Nagode maigida sameer,zan kiyaye hakan kuma yanzunnan zan fada maka abinda wannan zanen yake nufi a cikin rayuwa ta" ta qarasa tana wasa da 'yan yatsun hannunta tare da sunkuyar da kai qasa,shiru tayi na d'an daqiqai sannan ta fara da cewa
"Kwanaki kadan kafin nazo cikin masarautar nan,na rasa dukkan ahalina,dama ban tashi na samu mahaifiyata a raye ba,ina rayuwa ne tare da mahaifina sai kuma yayana,toh a wannan lokacin na rasa su gaba daya a lokaci daya,wanda alhakin mutuwarsu yana kan wasu mutane da ban san suwaye su ba,domin an d'ora musu sharrin laifin da basu jiba basu gani ba,hakan yasa Mai martaba sarki ya yanke musu hukuncin kisa" ta kai daidai nan yayinda kuka mai qarfin gaske ya qwace mata,shima fuskarshi fal tausayin yarinyar kuma ya kasa ce mata komai,don bai san dame zai fara ba,share hawayeta tayi sannan ta cigaba
"Wannan zanen key holder din da kake gani,na wata court lady ne,wacce na tabbar tana da alaqa da sharrin da aka yi wa ahalina,na taba haduwa da ita sau daya inda a wannan lokacin ne naga wannan abin maqullin a wajenta,kuma daga lokacin ban qara ganinta ba,na shigo cikin masarutar nan ne domin ina da yaqinin wata rana zan hadu da ita domin ta amsa min tambayoyina" ta qarasa hawaye na ta gangarowa daga idonta,bata damu da sharesu ba,domin ita kad'ai tasan irin quncin da take shiga a duk lokacin da ta tuna irin kisan rashin adalcin da aka yiwa ahalinta.
Cike da tausayinta ya kalle ta tare da cewa "kiyi haquri,ahalinki suna can suna hutawa in shaa Allah,kuma nayi miki alqawarin zan taimaka miki da duk abinda zan iya domin ki wanke baqin fentin da aka shafa wa ahalinki"
Kallon shi tayi da idonta da yake zubar da qwalla tace "Nagode maigida sameer,ba zan manta da karamcin ka a gareni ba" murmushi yayi yace "ba komai,dama manager ne yake nemanki nazo kiranki,amma ki zauna zan fada mishi ban ganki ba,in yaso zuwa anjima kya je ki gan shi" ya qarasa yana miqewa daga inda ya zauna,binshi tayi da kallo har ya bar wajen ba tare da tace komai ba,domin a halin da take ciki bata tunanin zata iya zuwa wajen manager domin yin wani aiki.

A cikin masarauta kuwa Hakimai ne jere a cikin fada,sun kai su 40,a gefe da gefen karagar mulki suke zaune a qasa kan carpet,goma a gaba,goma a baya,haka dayan bangaren ma goma gaba,goma baya.
A tsarin grand palace,hakimai sun rabu bangare hudu ne,akwai hakiman bangaren kudancin qasar,akwai na yammaci,akwai na gabashi sannan akwai na arewacin qasar.
Kasancewar babu gwamnati yasa masarauta ce take kula da komai na garin,saboda haka wadannan hakimai sune kamar ministers,akwai na bangaren ilimi,shari'a,tsaro,da sauran su.
Akwai zazzafar muqabala tsakanin hakimai na wadannan yankin basa shiri da wadancan yankin,kuma ko wanne yanki yana son wani nashi ya samu babban matsayi a kusa da sarki saboda su samu fad'a aji a masarautar.
A duk lokacin da sarki yake da wani hukunci da ya shafi masarauta,to suna da damar karba ko kuma yin tsokaci game da wannan hukunci kamar dai yadda akeyi a majalisa,dukkan hukunci yana zama cikakke ne tare da amincewarsu.
Kamar ko wane lokaci yau ma zaman fada akeyi,yayin da hakiman da suke a arewacin garin suke da jaa game da dawo da wata court lady da ta taba yin wani laifi aka koreta daga masarautar,yayinda ta kasance d'aya ce daga cikin ahalin hakiman kudu,su kuma hakiman kudu suna goyon bayan dawo da ita da za'a yi cikin masarautar domin su a ganin su wata dama ce a garesu.
Zazzafar tattaunawa ce a tsakaninsu yayinda mai martaba yana zaune akan karagar sa yana kallon kowa,ya riga da yasan menene a cikin rayukansu da dalilin da ya sa suke ta wannan cece- ku cen. Gyaran murya yayi da yasa kowa a wajen yin tsit,ya nisa tare da cewa
"Haqiqa mun fuskanci inda kowa a cikin ku ya dosa game da dawo da JALILA cikin masarautar nan,sai dai abinda zan fad'a muku guda d'aya ne,babu wani abu komai girman sa da zai hana dawowar jalilah cikin rayuwata"
Ya fad'a cike da iko da izzah ta cikakken basarake.
A lokacin na qare masa kallo sosai,matashi ne da ba zai wuce shekara arba'in da biyar ba,domin a cikin hakimansa akwai wad'and'a sun haife shi ma,sarki YA'AQUB NAUFAL kenan.
Yana da hasken fata sosai,idanunsa basu da girma can,sai dogon hanci siriri da ya ratsa fuskarsa,d'an sird'id'in saje ne a gefen fuskar sa sai dai bai barsu sun zubo har zuwa gemunshi ba,an katsesu ne daidai tsayin kunnensa,sai gemun da yake rage shi ba tare da yana barinshi yayi tsayi ba,a kallon farko zaka iya masa kallon sha-sha-sha ba don wannan alkyabbar mai zanen dragon 🐉 da yake sanye da ita ba,domin gaba d'aya bashi da suffar cikakkun maza,hakan ya samo asali ne daga sangarta shi da aka yi,ba shi da mu'amala da mutane,domin an raine shi tun yana yaro a matsayin yarima mai jiran gado,saboda haka karatunsa,da dukkan al'amuran rayuwarsa yana yinsu ne a cikin masarauta.

Tsit fadar tayi da jin furucin mai martaba,hakiman kudu har cikin zuciyar su sun ji dadin yadda sarki ya tsawatar kuka yayi amfani da qarfin ikon sa domin murtauke bakin hakiman arewa,wanda gaba dayansu sun cika da takaici akan dawowar jalila,domin kowa shaida ne akan irin son da mai martaba yake mata,kuma suna da yaqinin yana shirin dawo da ita ne domin ya aureta ta zama consort dinsa.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now