Page 30

91 8 0
                                    

Cikin farin cikin ganin shukrah sosai lady nadeeyah ta fara jero mata tambayoyi
"Shukrah meyasa kika sa kanki a cikin hatsari? Ya akayi suka barki kika taho?" Murmushi shukra kawai tayi tare da jan hannun lady nadeeyah tana cewa
"Ki taho muje mu zauna in fada miki komai,sannan kuma ki taimaka min mu samo mafita kafin wa'adina ya qare" bin shukra tayi har daki,saurin zama tayi domin ta matsu taji halin da ake ciki,ta kalli shukra da itama ta zauna,nan take shukra ta zayyane mata yadda sukayi da wakilin china,nadeeyah cikin damuwa tace
"Yanzu shukra maimakon ki zo wajenmu bayan kin je kinga gawar ba ita bace? Shine kika je kika kai kanki wajensu? Da yanzu bai yadda dake ba fa? Da tafiya fa zasuyi dake garinsu,ke dai bakya jin magana" cikin murmushi shukra ta bata amsa da
"Ai bana son in saku cikin matsala ne,kuma nayi sa'a ya yadda dani,duk da ina jin tsoro amma na nutsu sosai nayi masa bayani,gashi kuma yanzu ina zaune a gabanki" ta qarasa da sautin dariya,nadeeya ce tayi saurin cewa
"Gashi yanzu kwana uku yayi mana kadan amma zamu qoqarta sosai muga mun samu hujjar,sai dai kuma ta ina zamu fara?"
Shukra kanta a qasa tana wasa da 'yan yatsun hannayenta,tace
"Gaskiyane,lokaci yayi qaramci amma yanzu abinda yafi muhimmanci shine mu nemo inda Kun Yoon Dal yake,da mun ganshi shikenan komai ya qare" kaɗa kai nadeeyah tayi
"Gaskiyane,amma ta ina zamu fara nemanshi a cikin garin nan?" Shukra murmushi tayi tace
"Nayi magana da IG na police,kuma yace zai taimaka mana,domin shima ya yadda da bayanai na" jinjina kai nadeeya tayi tare da cewa
"Hakan ma yayi kyau,amma kafin nan akwai wani abu da nake tunani,me zai hana mu fara duba rubutun da yayi da sukace kafin ya mutu? Mu tantance ko rubutunshi ne ko ba nashi ba?" Kallonta shukra tayi cikin rashin fahimta tace
"Ban gane ba? Ta yaya kenan?" Murmushi nadeeyah tayi
"Kinsan Afrah,tana da qwarewa sosai wajen gane rubutun mutane,zamu kirawo ta cikin sirri domin ta taimaka mana,amma matsalar shine bamu san yadda za'ayi mu dauko wannan takaddar a record room din tribunal ba" jinjina kai shukra tayi tare da cewa
"In dai wannna ne akwai wanda ya taimaka min lokacin da naje ganin gawar,ina ganin idan mukaje da ke,zai taimaka mana mu shiga record room din" hakan kuwa sukayi,suka tashi suka tafi,cikin sauqi ya taimaka musu suka shiga ciki suka fara dubawa,suna cikin dube dubensu ne jameel ya shigo (baku manta ba shine director na tribunal ko? Babanshi kuma minister na tribunal) shukra ce tayi saurin durqusawa ta buya a qarqashin wani tebur da yake kusa da ita,hakan yasa bai ganta ba sai nadeeyah,kallonta yakeyi a tsanake sannan ya jefo mata tambaya
"Ba kece lady nadeeyah ta office if investigation ba?" Dan rusunar da kanta tayi"ehh yallabqi,nice" wata tambayar ya qara jefo mata
"Toh ne kikeyi a nan kuma?"
Cikin sanyin murya tace
"Nazo ne domin duba kayan yiwa yaranmu ladies investigators training" jinjina kai yayi,a lokacin ya saki fuskar shi tare da ce mata
"Me kike nema takamaimai,sai in taya ki dubawa" murmushi tayi masa tare da cewa
"Akwai rubutun da Kim Yoon Dal yayi lokacin da zai kashe kanshi,ina ganin zai taimaka musu sosai domin gane sigar rubutun wanda zai kashe kanshi domin qwarewa a bincike nan gaba,ko da buqatar hakan ta taso" jinjina kai yayi
"Ehh hakane,ina ganin suna ta nan ne" ya fada yana me nufar inda shukra take,zuciyar madeeyah da shukra kamar zasu fito saboda firgici,don wakilin china ya fada mata,ya kasance fitowarta cikin sirri ne,idan jameel ya ganta zai zame mata matsala,saura kadan ya zagayo inda take assistant dinshi ya shigo wajen tare da ce masa
"Yallabai,mahaifinka yana nemanka" jin haka yasa ya juyo tare da cewa nadeeyah yana nuna mata kan tebur din da shukra ta buya
"Ki duba yana ta can wajen ne,zanje mahaifina yana kirana" doguwar ajiyar zuciya ta sauke,tare da rusunar da kanta har ya fita sannan ta dago,shukra ma ta fito daga inda ta buya suka fara duba inda ya nuna musu,cikin sa'a shukra ta samu takaddar,dagota tayi ta nunawa nadeeyah
"My lady kin ganta nan" da murmushi nadeeyah ta miqo hannu ta karba,budewa sukayi suka tabbatar itace sannan suka bar wajen,kai tsaye record room din masarauta nadeeya ta tafi ta dauko littafin da mutum yake rubuta suna idan zai shga quaters din baqi sannan ta dawo gidan sameer ta samu shukra,sameer suka aika ya kirawo musu Afrah cikin sirri daga Office of investigation.

Duk abinda sukeyi shima IG ta nashi bangaren yana ta qoqarin ganin yadda zaiyi ya taimaka da abinda zai iya,yana zaune yana nazarin maganganun da sukayi da shukra,lieutenant ya shigo tare da rusunawa yace
"Yallabai mun shirya " da sauri IG ya miqe,ya dauki takobinsa a kan tebur tare da nufar hanyar fita daga office din,leiutenant ne yace masa
"Yallabai ya kamata kayi taka-tsa-tsan domin idan ya kasance yarinyar nan ba gaskiya ta fada ba,kaima zaka shiga matsala" juyowa yayi fuskar shi babu yabo ba fallasa ya kalli lieutenant yace
"Ni yadda da ita dari bisa dari,kuma zanyi iya qoqarina wajen ganin na nemo inda Kim yoon Dal ya buya,abinda kuma zai sani ahiga matsala abu daya ne,wato ya kasance Kim ya tsallake ya bar qasar JOSHUN" yana gama fadar hakan ya fita,leiutenant yabi bayanshi,inda 'yan sandan suka tsatstsaya suna jiranshi ya nufa,sun bi layi suna jiran umarnin sa,tsayawa yayi a saman step din bakin office tare da cewa
"Zamu raba kanmu zuwa duk inda muka san hanya ce mai sauqi ta fita daga garin nan zuwa china,domin a yanzu na san ko me yakeyi to yana neman hanyar fita daga garin nan ne,rabi zasu tafi gaɓar ruwan bodar gabas rabi kuma su tafi gaɓar ruwan arewa"
"Yea" dukkansu suka fada a tare tare da juyawa da sauri kowa ya nufi inda aka aika shi.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now