Page 12

59 7 0
                                    

Page 12

Washegari da safe lady jalila ta tashi da wani irin yanayi da kowa ya kasa ganewa,aikawa tayi a kira mata shukra,a kan hanyar su ta shigowa cikin quaters din suka ci karo da chief maid da tray a hannunta,abinda shukra ta kawo ne akan tray din,a dayan bangaren kuma wuqaqe ne,har sunyi gaba shukra ta juyo tacewa chief maid din

"My lady wannan ba leonuri herba (motherwart in english,ban san sunanshi da hausa ba) bane da na kawo jiya?" A razane chief maid ta jefo mata tambaya

"Ya akayi kika san haka? Kin bude abinda aka baki kenan kafin ki kawo?"

Girgiza kai shukra tayi tare da cewa

"A ah ban bude ba,qamshin ta na gane,kuma na san qarfe yana rage qarfinta (anti metal properties) gara kisa wuqar kaba amma kada kisa qarfe"

Jinjina kai chief maid din jalila tayi tare da qara jeho wa shukra tambaya

"Amma ya akayi kika san duk ilimin wannan abubuwan?"

Rusunar da kanta tayi tare da bata amsa

"Saboda ma'aikatan bureu of music suna dan yin rashin lapia da ba'a rasa ba,shiyasa nake karanta littafan magunguna domin samar musu magani"

Ba tare da ta qara ce mata komai tayi gaba,ganin haka yasa itama shukra tayi hanyar shiga wajen lady jalilah.

Bayan shukra ta tafi Haj jameela ta shigo ta tarar da jalila a inda shukra ta barta,zama tayi a inda shukra ta tashi,kafin jalila tace wani abu haj jameela ta fara magana

"My lady wace iriyar magana nake ji daga wajen chief maid dinki?" Jalila ta bude baki zata yi magana kenan chief maid ta shigo da faranti sai wani qaramin bowl 🥣 da magani a ciki yana ta tururi,ta ajiye kan qaramin tebur din da ya raba jalila da haj jameela,haj jameela ce ta qara cewa

"Maza ki shanye,domin babu wani maganin da zai yi sauri boosting din fertility dinki (haɓaka damar daukan ciki) kamar wannan"

Jalila ta kalli chief maid dinta tare da cewa

"Shekarar ki nawa kina tare da ni?"

Cikin ladabi tace

"Na kusa shekara shida"

Harara jalila ta watsa mata tare da cewa

"Shekara shida kuma har yanzu baki sanni ba ko? Dauke wannan abin kuma ki batar da duk wata shaidar shigowar sa a cikin masarautar nan"

Da mamaki haj jameela take kallon jalila

"Jalilah cewa fa kikayi a zubar,kin san tsadar maganin kuwa? Da kuma hatsarin da aka shiga kafin a shigo miki da shi?"

"Hatsarin da aka sa yarinyar nan a ciki kadai ya isa mama,me yasa kikai haka? Sai da kira yarinyar na bata haquri akan aikin da kuka sata don da an sanar dani tun farko da baku fara wannan aikin ba ma,bata dade da tafiya ba "

A dai dai lokacin wata a cikin maids dinta ta shigo a rikice tare da cewa

"My lady! an samu gagarumar matsala"

Gaban jalila ne yayi mummunar faduwa,Cikin razana ta kalli yarinyar tare da cewa

"Fada min yanzun nan,me yake faruwa"

❤️❤️❤️❤️❤️

A grand palace,mai martaba cikin razana ya kalli chief eunuch tare da cewa

"Kace an sa guba a tonic (hadin magani) din queen haneefah?"

Gyada kai chief eunuch yayi tare da cewa

"Hakane mai martaba,an gane hakan ne ta hanyar cokalin qarfen da aka saka da ya canja kala,Abin farin cikin ma shine bata kai ga shan tonic din ba" (a wancan zamanin suna gane akwai guba a cikin abinci ne ta hanyar amfani da qarfe,idan har akwai gubar qarfen zai canja kala kamar an zuba masa hypo,idan kuma babu toh ba zai yi komai ba)

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now