Page 38

69 5 0
                                    

Page 38

Har duhu ya fara shiga shukra da yayanta suna tsaye a wani waje sun labe suna jiran masu aikin bankin su tashi daga aiki,suna ta kallon qofar fitowa har sakataren bankin ya fito,shukra ce tayi saurin cewa
"Yaya kaga sakataren!" Jinjina kai yayi
"Ehh shine yake rubuta da dukkan kudaden da ake fitarwa,shi zamu bi bayanshi yanzu amma sai mun kula sosai don na tabbata wanda suka bada chek din qaryan suma suna bibiyar shi"
"Toh yaya muje" ta fada tana qoqarin tattare skirt dinta don fara tafiya,dakatar da ita yayi
"A'ah bazaki je ba! Ni zanje,saboda haka ki zauna a nan ki jira ni domin koda zasu nemi cutar dani,zan iya ji dasu" ba yadda batayi dashi ba amma ya hanata zuwa,hakan ya tafi ya barta a tsaye a inda suka labe,a hankali yake bin bayan sakataren da yake tare da wasu mutane biyu,ji sukayi kamar ana binsu,amma suka juyo suka ga ba kowa,haka suka cigaba da tafiya sai da suka zo daidai wani lungu suka qara juyowa,abdullahi ya qara buya,kafin abdullahi ya fito daga inda ya buya babu su babu alamun su,haka ya qarasa wajen da gudu yana ta waige waige don ya rasa inda suka bi,kamar daga sama suka fara dirgowa daga inda suka buya suka fara kawo masa farmaki,fada ne sosai ya kaure tsakaninsu,da yake shima gwanin fada ne kuma basu taba tsammanin hakan ba,haka yayi musu duka gaba dayansu,amma fa babu sakataren,takun sahun mutane masu yawa ya fara ji,kafin ya ankara 'yan sandan sun zagaye wajen,suna tare da sakataren sun daure shi da igiya,IG ne a gaba,kallon abdullahi yayi cikin rashin fahimtar dalilin da ya kawo shi wajen ya tambaye shi
"Me ya kawo ka nan wajen? Me kake yi?" Leiutenant NAM ne yace
"Yallabai,ina ganin mu tafi office tunda abokin aikin mu ne" hakan akayi,suka dunguma suka tafi dashi office,sai da suka qarasa IG yayi umarnin ayi masa tambayoyi,cikin damuwa ya fada musu cewar shukra qanwarsa ce,kuma tare suke da ita,su bar shi yaje ya duba ko tana lapia,don ya barta a cikin kasuwa,amma suka qi barin shi,har sai da IG ya tura gidan sameer kuma aka tabbatar masa da cewar dan uwan shukra ne sannan ya ce a kawo masa abdullahi,IG yana zaune Abdullahi ya shigo,rusunawa yayi ya gaishe shi,IG ya kalle shi
"Amma Me kuka je yi kai da shukra wajen?" Qara rusunawa yayi
"Munje domin binciken chek din kudi da aka bawa doctor Nuh ne" dago kai IG yayi ya kalle shi
"Ku ma? Muma abinda ya kaimu kenan,amma sai da na fadawa shukra ta cire hannunta a cikin binciken nan ko? Saboda kada hakan ya jawo mata wata matsala amma bata ji ba"
Daidaitawa sukayi da IG ya kuma tabbbatar wa abdullahi cewar ya aika a taho da shukra a inda yace ya barta,fitowa yayi daga office din IG hankalinshi ya kasa kwanciya domin dare yayi sosai,hankali tashe yake ta kallon hanyar shigowa wajen,assistant lieutenant da yaga alamun tashin hankali a fuskar shi yace masa
"Ka kwantar da hankalinka,ai an tafi a taho da ita,yanzu zaka gan su sun dawo" abdullahi bai kula shi ba,domin yadda yake ji a ranshi baya tunanin zai iya wata doguwar magana.

Shukra tana tsaye a inda ya barta,ta fara jin takun tahowar mutane,saitin inda take jin takun ta juya,mutane biyu ta gani suna doso inda take da yake dare ne,bude baki tayi ta fara cewa
"Yaya! Yayana! Kaine?" Kafin ta ankara sun rufe mata baki,dayan ya sa igiya ya daure mata qafa da hannaye,suka rufe idonta da wani qyalle suka sabata a kafada suka bar wajen da ita,sai da sukai tafiya mai nisa kamar ma zasu bar garin sannan suka tsaya,cikin wata bukka suka sata suka daure ta tare da daure mata bakinta yadda ba zata iya ihu ba.

Jaleel yana zaune babban yaron shi ya shigo
"Ranka ya dade mun dauko yarinyar,mun ajiyeta a wata bukka can kusa da kogi" jinjina kai jaleel yayi
"Toh ina son idan dare ya qara yi,mutane sun qara raguwa a wajen,ku kashe ta kuma kada ku bar wata alama da zata bayyana muna da alaqa da hakan"
"Yes sir" ya rusuna tare da tashi ya fita.

Queen haneefah tana zaune a gaban queen dowager,a halin yanzu tana iya bude idonta amma ba magana,queen haneefah kuka kawai takeyi,tunda aka tafi da ma'aikatan ta hawaye ya kasa tsayawa a idonta don har yanzu basu dawo ba,ita dai dowager ba umm ba umm umm,sai ido kawai,kafin kace me wannan,numfashinta ya fara daukewa,cikin tashin hankali queen haneefah ta fara qwalawa likitan da nurse din da suke kula da ita kira.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now