Page 48

98 7 0
                                    

Page 48

Duk inda ake cinikin bayi da safarar su zuwa wasu qasashen sai da suka je amma babu ita,matan da suka samu a wajen suka saki,IG yayi umarnin a mayar da kowa gidansu lapia sannan kuma sauran 'yan sandan da yayi aiki dasu yayi musu gargadin kada kowa ya san cewar yazo domin yin wani aiki.

Bayan sun gama yawon ne suka dawo masaukin su,abdullahi yana cikin matsananciyar damuwa,IG ne mai kwantar masa da hankali,kafe idonshi yayi a waje daya yace wa IG
"Ina tunanin kafin mu gama zagaya inda zamu je nemanta,ita tana can a wani wajen tana zaman jiran mu" jinjina kai IG yayi
"Kada ka damu,tunda mun tura jami'an sirri ko ina a cikin qasar nan,na tabbata zamuji labarinta nan bada dadewa ba" abdullahi ne ya dawo da kallonshi kan IG
"Amma yallabai ina mamakin yadda akayi kake amfani da jami'an sirri da kuma 'yan sanda da sojoji" shiru IG yayi daga bisani kuma ya laluba gefen rigarsa ya ciro wata 'yar purse (jaka) zazzageta yayi sai wani abin katako ya fado,rubutun yaren su ne a jiki,ya miqawa abdullahi,karba yayi yana dubawa saboda bai san menene ba
"Wannan shine IMPERIAL DISPATCH SEAL wato wani hatimi ne da yake nuna umarnin mai martaba,shiyasa duk umarnin da zan bayar kuma nayi amfani da wanann hatimin,umarnina kamar na mai martaba ne"  da mamaki abdullahi ya kalli IG
"Amma ya akayi ka samu?" Kawar da kai IG yayi gefe
"Mai martaba ne ya bani shi kafin na taho nan" mamaki sosai abdullahi yakeyi don shi bai san mai martaba ya kori IG da wata manufa bane,bai san cewar akan umarnin mai martaba suka fito neman shukra ba.

Bayan wani lokaci,mai martaba zaune a inda ya zamar masa office,ya zauna ya dafe kanshi cikin dogon tunani,chief eunuch ne ya shigo ya rusunar da kan shi
"Your majesty! Qarfe uku da rabi yanzu na dare,ya kamata ka tafi bed chamber dinka ka kwanta"
Mai martaba dago kanshi yayi ya kalli chief eunuch sannan ya sunkuyar da kai
"Yanzu kwanaki dari da ashirin (120) kenan ko dari da ashirin da daya ne ma? Ban sa ta a idona ba,ban san inda take ba" yanda chief eunuch ya ji mai martaba ya riqe qirgen kwanakin ne ya bashi mamaki kuma ya tabbatar ba qaramar damuwa yayi da shukra ba.
Tunanin mai martaba ne ya koma inda yayi magana da IG bayan yasa an koreshi daga aiki
"Kaje ka nemo min shukra! Shiyasa na sa aka koreka daga aiki,ya kamata naji abinda zata fada min! Bayan na sameta a raye kuma cikin qoshin lapia,zan ji abinda zata fada min,daga nan kuma sai na san wane mataki ya kamata na dauka" sunkuyar da kai IG yayi,mai martaba ne ya dauko hatimin ya miqa masa,hannu yasa ya karba
"Wannan imperial dispatch seal ne,zaka iya amfani dashi wajen cika aikinka,amma bana son ya dauki lokaci domin za'a iya fuskantar dalilin korarka daga aiki kuma hakan sai bata komai! Shin zaka iya aikin da na sa ka?" Rusunawa yayi
"Yes your majesty! Zan bi umarnin duk abinda ka saka ni"

Bayan ya dawo daga tunanin ne ya kalli chief eunuch
"Muje ina son na sha iska" tashi yayi,C.E yabi bayanshi suka fito har garden din mai martaba,inda suke zama shida shukra yaje ya zauna cikin yanayi mara dadi yake kallon inda ta saba zama,hannu yasa ya shafa wajen zaman nata,tunanin yadda take sashi farin ciki da nishadi yakeyi a duk sanda ya nemi ganinta,abubuwan suka dinga dawo masa tamkar dai tana zaune a kusa dashi ne,runtse idonshi yayi can qasan maqogoronsa yace
"Na fara gajiya da jiran dawowarki,rayuwata ta cika da duhu da ɗaci saboda rashin ki! Ina kika shiga shukra? Ko dai ba zaki dawo bane? Ko dai ba zan qara ganinki bane?" Wasu ɓurɓushin furen fulawoyi ne suka fara zubowa,iska tana kadosu kanshi,daga kanshi yayi yana kallo,wani mai alamun shape din  zuciya ne ❤️ ya dauki hankalin shi,yana kallon shi har ya bacewa ganinsa,zuwa yayi ya sauka cikin wani ruwan kogi a can wani gari,hannu tasa ta dauko shi domin tana zaune a bakin ruwan taga saukar furen,daga kanta tayi ta kalli sararin samaniya,miqewa tayi tsaye tare da barin bakin ruwan ta hawo wata gada data kawo ta daidai inda dakunan tashar jirgin ruwan suke,irin furen ta gani a qasa sosai domin a yanzu lokacin kaɗewar su ne,a jikin wani katako ta tsaya ta kalli sama kamar mai tunani,can qasan maqogoronta tace
"Cheo-nah! Ta kafe idonta a sama tana kallon taurari.

Qauyen UIJU, wanda yake cikin garin PYONGAN

Gidan wani babban dan kasuwa ne shaharrare sosai a cikin qasar,yana tsaye ya goya hannayensa a bayansa yana ta kai-kawo a farfajiyar gidan,wani yaronsa ne da yake masa aiki ya bullo ta dayan bangaren gidan,da hanzari ya juya inda yaron yake tahowa
"Ka ganta kuwa?" Cikin kidimewa yaron yace
"Na duba ko'ina ban ganta ba" cikin tashin hankali da bacin rai yacewa yaron
"Me kake nufi? guduwa tayi ne?"
Girgiza kai yayi
"Bana tunanin haka! Tunda har yanzu bata gama warkewa ba"
"Kasa mutanen mu su tafi nemanta,yanzu!!" Ya qarasa maganar cikin qaraji
"Yes my lord" yaron yace sannan ya bar wajen da sauri.
Cikin nutsuwa take takunta har ta shigo farfajiyar gidan,a kan hanya suka ci karo da shi zai fita da sauri,ganinta ya sashi dakatawa
"Shukra! Ina kika tafi ne?" Murmushi tayi masa
"Na danje na zagaya ne na miqe qafafuwa na,wani abin ya faru ne?" Sunkuyar da kai yayi
"Kowa hankalin shi a tashe saboda muna tunanin ko guduwa kikai" dariya mai sauti tayi
"Guduwa kuma? Meyasa zan gudu?" Kafin yace mata wani abu mai gidan ya qaraso inda suke,da hanzari ya qaraso ganin shukra yana kiran sunanta,jin haka yasa ta juya ta dan rusuna tare da cewa
"Director!" Cikin damuwa yace mata
"Ina kika shiga ne? Na shiga damuwa sosai" dariya tayi cikin jin dadin kulawar da suke bata tace
"Kayi haquri director! Na saka nemana" girgiza kai yayi
"Ba komai! Wuce muje ki sha maganin ki" bata fuska tayi
"Ni na warke fa! Kaga kafadar tawa,har hannuna ma ina iya dagawa yanzu" girgiza kai yayi
"Ke dai ba zaki daina gudun magani ba,ai likitan yace har yanzu jikinki babu qwari sosai,kina buqatar ki cigaba da shan magani" haka ta bishi a baya amma fuskar babu walwala.
Dakinta suka shiga inda aka ajiye mata maganin tun dazu bayan an dafa shi an tace,daukowa yayi ya miqa mata bayan sun zauna,karba tayi da hannu biyu tare da kaiwa bakinta ta shanye sannan ta ajiye kofin,goge bakin tayi
"Ban san ta yadda zan saka maka ba da irin karamcin da kayi min! Ka ceci rayuwata kuma kana bani kulawa sosai" dariya yayi mai sauti
"Shukra kenan! Ai kawai nayi abinda ya kamata nayi ne,saboda ba zan iya barinki a wajen ki mutu ba! Kinga a haka ma sai da kikai wata biyu baki san inda kanki yake ba don har likitocin sai da suka ce da qyar in zaki rayu" rusunawa tayi
"Gani nan kuma a raye saboda taimakonka,nagode sosai" girgiza kai yayi
"Ba godiya nake so ba,ki dage da shan magani saboda ki warke sosai kinji?" Jinjina kai tayi tace
"Yes sir"
Dan sunkuyar da kanta tayi sannan ta dago ta kalleshi
"Yallabai babu wani labari daga cikin gari har yanzu?" Yanayin shi ne ya canja lokaci guda,cikin rawar murya yace
"Labari?" Kada kai tayi
"Ehh,wasiqar da na aikawa yayana nake nufi,ya kamata ace naji daga gareshi zuwa yanzu"  dan kauda kansa yayi gefe
"Ehh..... ai kinsan saboda masu fatauci muka bawa wasiqar,kuma suna tsaye-tsaye a wajaje da dama kafin su qarasa cikin birni! Na tabbata zakiji daga gareshi kwanan nan,kafin nan dai ya kamata ki daure da shan magani don ki samu lapia sosai"
"Yes director" ta fada cikin jin dadin yadda yake kulawa da ita.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now