Page 18

63 4 0
                                    

Page 18

A ɓangaren queen dowager bata san me yake faruwa a office of investigation ba,jikinta yayi qwari sosai tayi shigarta kamar yadda ta saba cikin alkyabbarta ta alfarma,tana zaune inda ta saba zama a sit room dinta,ɗan ɗaga murya tayi

"Waye a nan kusa?" Ta fada tana mai kallon qofa,chief maid dinta ce ta shigo da sauri tare da rusunar da kanta tace

"Your majesty! ,kamar kina kirana ko?" Jinjina kai tayi

"Ehh ni na kiraki,kuyi shiri yanzu zamu fita" cewar queen dowager,qara rusunawa chief maid din tayi

"Ranki ya dade,ina zamu je a wannan lokacin?" Dago kanta tayi ta kalleta tare da bata amsa

"Ba yau da safennan za'a miqa lady jalila zuwa tribunal ba? Ya kamata naje rakiya saboda darajar qawancen da ke tsakanin mu" ta qarasa cikin shu'umin murmushi,amsawa chief maid din tayi tare da fita domin shirin fitar su.



Lady jalila tana zaune tayi nisa cikin tunani taji shigowar mutum,ɗagowar da zatayi taga chief maid dinta ce,da sauri chief maid din ta qaraso gaban lady jalila,cikin fuskar alhini tace

"Maa- maa" (My lady da suke kiran Matan sarki kenan banda queen da suke kiranta CHUNCUN MAAMA,My lady da suke kiran SAURAN PALACE LADIES din kuma maa-maa-neem! Da yarensu)

Murmushi jalila ta yi mata tare da cewa

"Me ya kawo ki nan a wannan lokacin,na zata kuma kuna karɓar hukunci saboda laifin uwar dakin ku" rusunar da kanta tayi,qwalla ta tsatstsafo a idonta,daga bisani tace

"Mun sha wahala my lady,amma wannan ba komai bane domin muna can amma zuciyar mu a cikin tunanin ki take,da fatan kina lapia"

Jinjina kai kawai jalila tayi alamar "Eh " cike da tausayin ma'aikatan nata,

"Maa-maah! yanzu zaki fita daga wajen nan domin an samu hujjar cewa baki da laifi" zumbur lady jalila ta miqe daga inda take zaune,idonta suka fiffito take kallon chief maid dinta cike da mamakin furucin da yake fitowa a bakinta daidai lokacin da ta riga ta yanke tsammanin fita daga wannan matsalar,cike da rikici tace

"Me kike nufi da hakan? Hujjar cewa bani da laifi? Ta yaya kenan?"

Rusunar da kanta tayi

"Yarinyar nan shukra itace ta samo hujjar,kuma mai martaba ma da kanshi ya tabbatar da hakan,saboda haka yanzu chief secretary ya shigo cikin nan wajen tare da royal order domin a wanke ki daga laifi" wani farin ciki ne mara misaltuwa ya bayyana a kan fuskar jalila,da sauri tayi hanyar fita waje chief maid dinta ma tabi bayanta,tana fitowa ta tarar da duk ma'aikatan office of investigation sunyi layi kamar 'yan assembly suna jiran fitowar ta,director da chief sumayya da green din uniform dinsu a gaba,nadeeya da basma da ash din uniform dinsu a baya,sai sauran ladies masu pink din uniform kusan su 30 suma a baya duk sunyi layi layi kamar assembly dayan bangaren kuma maids din lady jalila da suka zo yi mata rakiya,a daya bangaren kuma royal guards ne da suka zo tsaron lafiyar jalila,sai kuma su chief secretary da sauran sakatarorin masarautar suma a gefe guda.

Tana fitowa ta tsaya kan step din office da ta fito,dukkan mutanen wajen suna can qasa da ita,director ce ta fara magana

"Maa-maah! Ki yafe mana,haqiqa munyi babban kuskure,ki yafe mana" ta fada tare da rusunar da kanta har wuyanta qasa sosai alamun neman afuwa,chief sumayya ce da idon ta yai qifi qifi itama ta rusuna tare da cewa

"Maa-maah! Haqiqa mun aikata mafi munin kuskure,ki yafe mana " ta qarasa tare da qara rusunar da kanta qasa sosai,sauran ladies dinne gaba daya suka rusunar da kansu tare da fadin

"Maa-maah! Ki gafarce mu"

Cikeda nutsuwa jalila ta sauko daga inda take tsaye sai da tazo daidai inda sumayya take

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now