Page 56

88 9 0
                                    

Page 56

Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa,kuma ya qara tabbatarwa shukra yake gani ba mafarki bane,ba gizo take masa ba,janye jikinsa yayi daga rungumar da yayi mata,ya kama hannayenta ya riqe su gamgam,hawaye ne yake fita daga idonshi,lokaci daya kuma yana murmushi,wannan shi ake cewa kukan farin ciki
"Ashe zan qara ganinki? Kinsan tsawon lokacin dana dauka ina jiranki? Zuciyata cike take da tsoro! Ina tunanin kamar ba zan qara ganinki a duniya ba,ina kika shiga? Meyasa baki iso gareni ba tun tuni?" Duk a jere yake jero mata tambayoyin,kallon mamaki kawai take binshi dashi don bata san ya damu da ita har haka ba,cikin kuka tace
"Ka gafarceni your majesty! Nayi qoqarin isa gareka amma na gagara yin hakan!" girgiza kai yayi
"A'ah kada ki nemi gafara ta,ni zan nemi gafarar ki! Saboda ni kike ta wannan wahalar a rayuwa,ni ne silar wahalar ki shukra" itama girgiza kanta tayi,tana kallon yadda yake zubar da hawaye,tace
"Cheo-na!" Qara janyota yayi ya rungumeta tsam tare da sakin murmushi wanda ya dade baiyi irinsa ba.

PALACE

"Kina nufin mai martaba baya cikin masarautar nan a wannan lokacin?" Queen jaleela ta tambaya cikin rashin nutsuwa,rusunar da kai chief maid tayi tace
"Ehh your majesty! Ya fita cikin shirin badda kama kusan awanni biyu da suka wuce,gashi har dare ya tsala" da hanzari ta koma wajen zamanta ta zauna,kana ganinta kasan tashin hankali ya samu wajen zama,tace
"Shin ina mai martaba zaije a irin wanann lokacin?" Tana magana ne tana jijjiga jikinta tsabar tashin hankali,chief maid bata kai ga bata amsa ba nusaiba ta shigo
"Your majesty! Police superintendent yana waje" da sauri jaleela tace
"Shigo dashi" komawa nusaiba tayi sannan jaleel ya shigo cikin tsananin tashin hankali,kafin ya zauna ta jefa masa tambaya
"Orabeuni! Ina shukra?" Baice mata komai ba sai zama da yayi yana huci,cikin daga murya tace
"Kun qara rasata kenan!" Dago kanshi yayi ya kalleta
"Your majesty! Kada ki damu....." katseshi tayi da wata gigitacciyar tsawa
"Orabeuni!!! Kada na damu? Bayan mai martaba baya cikin palace dinnan? Kuma babu wanda ya san inda yake,idan ya hadu da ita fa? Idan suka hadu fa?"
"A'ah your majesty! Ba zasu taba haduwa ba,ta yaya zai samo ta?" Huci kawai takeyi mai mugun zafi,don a halin yanzu babu wanda zai gane halin da zuciyarta take ciki.

Yana zaune a ofdice dinshi da yake gidan,banbancinsu da office dinshi na grand palace kawai kayan qawa da ado ne,amma kusan komai iri daya ne,gidan sarki kenan wanda yake wajen masarauta kuma a cikin gari,gida ne mai kyawun gaske,domin ya fita daban daga irin gine ginen su,chief eunuch ne ya shigo tare da rusunawa yace
"Your majesty!" Mai martaba Dago kansa yayi tare da miqawa chief eunuch takadda yace
"A kaiwa chief Suh wannan" karba yayi cike da girmamawa,har zai juya mai martaba ya qara ce masa
"Likitan yazo ne?" Juyowa chief eunuch yayi
"Bai qaraso ba,na aika a kirawo shi a sirri amma na san sun kusa qarasowa" jinjina kai mai martaba yayi
"A tabbatar ya duba ta sosai da sosai,ta rame sosai ta qara komawa 'yar shafal-shafal,ka fada masa na bashi amincewata,a duba min lafiyarta sosai"
Amsawa chief eunuch yayi yana qunshe murmushinsa,a karo na farko ya fara ganin halittar da mai martaba yake daga hankalinsa a kanta,shukra kenan,chief eunuch yana fita shima ya fito.

A bayan gidan ya sameta cikin garden tana zaune tana shafa algaitar ta,amma ta nutse a cikin tunani,tun daga nesa yake hango yadda take kallon algaitar a tsanake,ya dauki lokaci a tsaye a wajen kafin ta kula da zuwanshi,tasowa tayi tazo gabanshi ta tsaya tare da rusunar da kanta tace
"Cheo-na! Yaushe kazo nan?" Murmushi kawai yake mata,bakin yaqi rufuwa
"Kenan ba mafarki bane! Kece a tsaye a gabana" kallonshi take abin ya daina bata mamaki ya fara bata tsoro,hannunta ya riqe,wannan karon ta dan tsorata da irin riqon da yayi mata,fahimtar hakan yasa ya janyo hannunta suka dawo cikin Office din nasa suka zauna,bayan ta zauna ne take ce masa
"Har yanzu na kasa yadda duk wahalar da na sha akan na samu ganinka,sai gashi kidan algaita ne yayi sanadin haduwata da kai" dariya mai sauti sosai yayi sannan ya kalli gefen shi yace
"Wani lokaci can a baya,a daidai irin wanann lokacin...... FLASHBACK

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now