Page 34

88 8 0
                                    

Page 34

Washegari da safe shukra da Afrah suka shiga kasuwa bangaren masu siyar da magani,a tsanake suke gabatar da kansu tare da duba registar kowane shago,da kuma itatuwan da ake aikawa cikin royal pharmacy,yayinda suke riqe da takaddar da take dauke da rubutun dukka tonics din da ake bawa queen dowager,duk iya kacin bincikensu basu samu wani abin zargi ko kuma wani abu mara kyau acikin magungunan ba,hakan yasa suka dawo domin bawa lafy nadeeyah rahoto,sun tabbatar mata basu samu komai ba,komai lapia yake,cike da mamaki tace
"Amma meyasa rashin lafiyar ta take qara ta'azzara lokaci daya?" Cikin hanzari shukra tace
"My lady ina ganin kamar an yi wannan ne domin a qalawa consort hui sharri" jinjina kai Afrah da nadeeyah sukayi,nadeeyah tace
"Lallai maganar ki abar dubawa ce" kafin wani ya qara magana suka hango basma ta taho da gudu a sukwane tana qwallawa nadeeyah kira,cikin razana suke kallon yadda ta nufo su,tana huci ta tsaya tare da ce musu
"Kun ji labari? Jikin queen dowager ya rikice sosai,ance ta shiga coma bata san inda kanta yake ba" cikin tashin hankali dukkansu suke kallonta tare da neman qarin bayani.

Queen haneefah cikin tashin hankali take tafiya kamar zata fadi,ta taho daga quaters dinta zataje wajen queen dowager,tunda labarin rikicewar jikinta ya riske ta,gabadaya ta rasa nutsuwarta,taje ta ganta a kwance yayinda royal doctors suke iyakacin qoqarin su amma babu alamar zata farfado,cikin tsananin tashin hankali ta aika a kirawo mata nadeeyah,da zuwanta ta fara tambayarta menene sakamakon bincikensu,cikin ladabi nadeeyah tace mataa
"Your majesty duk binciken da mukai bai nuna akwai wata matsala da tonic din da dowager queen take sha ba" queen haneefah cikin tsanin tashin hankalin da take ciki tace mata
"Amma kina ganin abinda ya faru yau ko? Ance har ta danji sauqin jikin,har ta tashi fa ta shirya zataje ganin mai martaba a grand palace kawai ta yanke jiki ta fadi,ba zai yiwu ace hakan bashi da wani dalilin faruwa ba,dole akwai wani abu" jinjina kai nadeeyah tayi tare da cewa
"Zamu qara bincikawa your majesty,Allah ya bata lapia"

Sameer ne a tsaye a tsakar gidansa yana ta kai kawo yana jiran dawowar abdullahi,tun da ya hango shi daga nesa ya tafi da gudu
"Yauwah,yayan mu,shukra ce take nemanka a office of investigation,kuma neman na gaggawa ne" cikin mamaki ya kalleshi yace masa
"Amma ni ba za'a barni na shiga palace ba ai"
"A'ah za'a barka ka shiga tunda muna tare" sameer ya bashi amsa,hakan yasa suka dauki hanya suka tafi har cikin office of investigation,sameer ne yaje ya nemo shukra,godiya tayi masa sosai da ya kawo mata abdullahi,tare suka tafi da abdullahi zuwa wajen su nadeeyah da afrah,ta nuna musu abdullahi tare da cewa
"Wannan yayana ne,yana aiki a police bureu a matsayin mai binciken gawa" Afrah ce ta qura masa ido,tana murmushi,shujra da ta lura da ita ta tambayeta
"Ya dai? Kin san shi ne?" Kada kai Afrah tayi
"Ehh mun taba haduwa dashi,amma ban san yayanki bane" sai a lokacin abdullahi yayi magana
"Ehh mun taba haduwa,lokacin da muka zo nan tare da IG yin wani training" murmushi shukra tayi tare da cewa
"Na sa yazo ne domin yana da experience sosai akan abinda ya shafi guba (poison) ko zai taimaka mana da binciken da mukeyi"
Cikin hanzari Afrah taje ta kawo dukka itatuwan da ake amfani dasu wajen yin tonic din queen dowager,a tsanake ya gama dubasu tsaf kuma ya tabbatar musu babu wata matsala dangane da itatuwan,sun baro wajen shukra ta taho domin ta raka shi yake tambayar ta me yake faruwa,rage murya tayi sosai tare da fada masa binciken sirrin da suke yi,da mamaki sosai a kan fuskar sa ya ce mata
"Kina nufin ana tunanin akwai wata matsala da tonic din queen dowager?" Jinjina masa kai tayi cikin sanyin jiki,sai da ya shiga dogon tunani kafin daga bisani yace mata
"Sai dai kinsan wannan itatuwan da kuka nuna min ana amfani dasu ne wajen hada mata tonic din da take sha,kuma kinsan wadannan itatuwan basa haduwa da wolfsbane,rhino horn,da black cohosh,to indai tana shan wani abin da yake dauke da su lallai zai iya zamar mata guba" jinjina kai shukra tayi tare da tambayar shi
"Toh Amma yaya,tonics din da ake hafawa da wolfsbane...." Bata qarasa ba ya tari numfashinta
"Ai suna da yawa,kamar Gungang,baekchul,da kuma....." katse shi tayi
"Baekchul kace?" Shukra ta katse shi cikin hanzari,gyada mata kai yayi
"Me ya razana ki haka?" Daidaita nutsuwar ta tayi tare da ce masa "ba komai" A take tunaninta ya koma kan takaddar data gani a dakin nusaiba,maid din lady jaleela ranar da suka je bincike a.chamber dinsu,bayan sun rabu da abdullahi ta kasa fadawa kowa domin tana tunanin maganar da nadeeyah ta fada mata
Nadeeyah-
"Idan har hakan ya kasance gaskiya,toh zai iya kasancewa aikin consort hui ne"
Shukra - "a'ah my lady,consort hui ba zata aikata rashin imani irin wannan ba,kuma zamuyi aiki tare domin wanketa daga wannan zargin"
Bayan ta dawo daga tunanin ta rasa inda zata sa kanta,daga ina zata fara? Domin gaba daya kanta ya kulle,me yake shirin faruwa da ita haka? Tashi tayi tazo daidai qofar quaters din consort jaleela ta buya a bayan wasu shukoki,bata dade a wajen ba kuwa nusaiba ta fito,amma ba uniform ne a jikinta ba,ta dora alkyabba a kanta,yadda ba za'a gane fuskarta sosai ba,a hankali shukra ta fara bin bayanta har suka fita daga masrautar,nusaiba da take jin kamar ana binta ta tsaya tare da juyowa,amma bata ga kowa ba,cigaba tayi da tafiya,itama shukra ta cigaba da binta a boye,gani tayi ta tsaya a wajen wani mutum da ya juya bayansa tare da ce masa
"Yallabai na qaraso" juyowar da zaiyi shukra taga jaleel ne,murmushi yayi mata tare da miqa mata wata takadda
"Ki kaiwa royal doctor wannan takaddar" hannu tasa ta karba tare da boyeta a jikinta,jinjina mata kai yayi yace
"Lallai aikinki yana kyau,zan aika sakamakon aikinki zuwa wajen iyayenki" rusunar da kanta tayi cikin farin ciki tace
"Nagode yallabai" duk abinda sukeyi akan idon shukra,daga nan nusaiba ta juyo ta dawo cikin masarauta,kai tsaye royal pharmacy ta nufa,ta samu royal doctor da yake duba queen dowager a cikin hikima ba tare da kowa ya lura ba ta miqa masa takaddar,karba yayi ita kuma ta dauko hanya zata koma quatera dinsu,duk abinda ya faru akan idon shukra,da sauri ta fito ta qarasa ta janyo hannun nusaiba,a razane nusaiba ta juyo,ganin shukra yasa gabanta mummunar faduwa,cikin inda inda ta fara
"Ke shukra,ne ya kawo ki nan?" Cikin dakewa shukra ta jefa mata tambaya
"Ke zan tambaya,takaddar me jaleel ya baki ki kawo wa royal doctor? Baekchul tonic dinne da kuke rubutawa domin a dinga bawa queen dowager?" Tsurewa nusaiba tayi amma da yake ta raina shukra sai tace mata
"Me kike magana akai? Ni ban fahimci me kike fada ba" idon shukra karr a kanta ta qara jefa mata wata tambayar
"Waye yake baki umarnin abinda kike aikatawa? Yallabai jaleel ne? Ko kuma...." Katse ta nusaiba tayi
"Ke shujra kin isa ki sani a gaba kina min irin wannan tambayoyin? Har kin isa ki tsaya a gabana wai ke lady investigator,bayan munsan lokacin da kike a baiwar ki? Dalla sake ni" ta qarasa tare da fincike hannunta daga na shukra.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now