Page 46

118 7 0
                                    

Page 46

"Your majesty! Akwai labari mara dadi" dukkansu juyowa sukai suna kallon chief secretary da yake magana,murmushin da yake fuskar mai martaba ne ya gushe a take,tsayuwarsa ya gyara sosai
"Mummunan labari? Me yake faruwa?

Zanen fuskar shukra ne ake ta rabawa 'yan sandan da suke RIGHT police bureu na bangaren IG,sai da kowa ya samu nashi sannan IG yace musu
"Wannan shine hoton lady investigator shukra da ta bata! Ku tabbatar kun nemo ta,kuna ji na?" Ya fada cikin yanayin tsawa,daga ganin yanayin fuskarshi da maganarshi zai tabbatar maka yana cikin tashin hankalin batan nata
"Yes sir" dukkansu suka amsa,tare da rusunar da kansu sannan suka juya suka fita da hanzari,suna fita aasistant lieutenant yana shigowa,da hanzari ya qarasa gaban IG,shima yana ganin shi yace
"Ka dawo? Ya labarin minister?"
"Minister!" Assistant lieutenant ya fada cikin rawar murya,IG ne ya tambayeshi
"Yana da labarin shukra ko?"
Sunkuyar da kai yayi
"A'ah an kashe shi jiya da daddare" idanuwan IG ne suka fiffito waje,cike da mamaki yace
"Me kake nufi da an kashe shi?"
"Jiya da daddare wasu mutane da ba'a san ko suwaye ba suka gidansa,sun kashe kowa da kowa,amma LEFT police bureu (bangaren jaleel) sun tabbatar da cewa 'yan fashi ne,amma hakan ba mai yiwuwa bane,kisan gilla akayi masa" IG hankalinsa ya tashi sosai,kawar da kai yayi kamar mai tunani,sai kuma yace
"Amma ta yaya hakan zata faru?"
"Yallabai baka tunanin zai iya kasancewa itama lady shukra....." da hanzari IG ya juyo yana kallon lieutenant Nam da yayi maganar,taga taga IG yayi kamar zai fadi ta baya,da qyar dai ya iya dafa bango ya tsaya.

Abdullahi cikin galabaita yake tafka uban gudu kamar zai kife,sunan shukra kawai yake kira amma duk inda yabi shiru har ya bar cikin gari ya shigo daji amma babu ko alamun ta.

Tana ta faman qoqarin tafiya cikin ciyayin,zubar jinin yaci qarfinta sosai,tana tafiya tana qara bawa kanta qarfin gwiwa,ta dauki hanyar da zata kaita inda mai martaba yake ne tana cewa
"Ya zama dole naje ga mai martaba,dole ne na bashi wannan hujjojin" tana ta qoqarin tafiya tana faduwa kuma ta tashi ta qara tafiya,faduwa tayi a qasa warwas a wannan karon kuma nan da nan idonta ya fara ganin dishi-dishi,daga nan kuma bata qara sanin inda kanta yake ba.

Da hanzari ya shigo inda gidan sarki na garin hubbaren yake,inda ya tarar da ministan tribunal suna jiran shi,shi ya fara jefawa tambaya
"Gobara a royal treasury? Ta yaya haka ta faru?"
Rusunar da kai minister yayi
"Ina ganin wasu ne suka shirya tawaye saboda ganin baka nan"
Bude baki mai martaba yayi cike da mamaki yace
"Tawaye? Ta yaya kenan?" Wajen yake qarewa kallo sannan ya juya ga jameel
"Tribunal director! Na baka alhakin bincika abinda ya faru sannan ka kawo min report" rusunawa yayi
"Yes your majesty!"
Juyawa ya qara yi ga royal secretary
"Ayi mana shirye shiryen komawa gida!"
"Yea cheo-na!" Chief secretary ya fada tare da barin wajen.

Tana zaune hajiya jameela ta shigo,zama tayi tare da qarewa jaleela kallo,cikin sigar rarrashi tace mata
"Your highness! Naji labarin jiya bakiyi bacci ba,kalli yadda kika koma,kije ki kwanta...."
"Yanzu ba lokacin bacci bane maama" ta fada a cikin yanayin damuwa,amma kuma babu karaya a tattare da ita
chief maid ce ta shigo,ta rusunar da kanta
"Your highness! Mun samu labarin mai martaba yana kan hanyarsa ta dawowa" cikin razana ta dago kai ta kalleta
"Yana hanya?" Da tsoro da firgici kwance akan fuskar ta
"Jaleel yace babu damuwa,komai zai tafi daidai" haj jameela ta fada
"Yanzu mama! Abu mafi muhimmanci shine shukra,ba zamu iya sakin jiki ba har sai munga gawarta" hajiya jameela bata ce komai ba,don itama ta san shukra babbar damuwa ce a halin yanzu,jaleela ce ta cigaba da magana
"Na kasa ganewa! Da tana raye nasan dole zata nemi ganin likita,amma an neme ta an rasa a cikin garin nan,to ina zata je?" Sunkuyar da kai haj jameela tayi,kamar wacce ta tuna wani abu jaleela tace
"To ko dai tana..." hajiya jameela ta dago kanta
"Menene your highness? Me kike tunani?"
"Ko dai ta tafi wajen mai martaba ne?" Jaleela ta fada a cikin zuciyarta,bata bari maganar ta fito fili ba.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now