Page 35

69 5 0
                                    

(A cikin masarautar JOSHUN ana adressing sarki da YOUR MAJESTY,hakan ma sarauniya,domin kanar yadda sarki yake shine uba ga dukkan 'yan qasar,itama sarauniya haka take,itace UWA ga dukkan mutanen qasar,shiyasa duk wata matar sarki ba za'a kirata da queen ba,queen guda daya tal akeyi a cikin masarauta,shiyasa itama ana kiranta da YOUR MAJESTY,ita kuwa queen dowager,ainihin kalamar DOWAGER yana nufin kamar sarauniyar da tayiwa sarki takaba,ko da kuwa bata da da,kuma wanda ya gaji sarautar da danta bane na cikinta,idan sarki ya mutu yana da consort,kuma consort dince kawai take da dan da zai gaji sarauta,to wannan consort din ba zata taba zana queen dowager ba,kuma itama queen dowager ana adressing dinta ne da YOUR MAJESTY,bayan mutum ukun nan,duk wani wanda zai biyo baya,ko dan sarki,ko consort din sarki sai da a kirasu da YOUR HIGHNESS,ina fatan kuna fahimta)



Page 35

Ya fito daga quaters din queen dowager,chief eunuch da sauran maids da suke jiran shi a waje suka bi bayanshi,yadda yake tafiya jikinshi a sanyaye,da qyar yake daga qafa,haka suma suke bin shi,suna fitowa daga quaters din nata ya juyo ya kalli chief eunuch
"Zaku iya tafiya daga nan,ina son aksancewa ni kadai" rusunawa chief eunuch yayi
"Mai martaba dare ya tsala,ya kamata kaje ka kwanta" girgiza kai mai martaba yayi
"Ko naje na kwanta yanzu,ba zan iya bacci ba,zan zagaya domin na sha iska" rusunawa yayi tare da cewa
"Yes your majesty" wuce mai martaba yayi,sauran maids din suka bi bayanshi suka bar mai martaba a wajen,zagaye ya fara yi har office of investigation,Jin shiru ya tabbatar masa da ba kowa a wajen,zagayowa yayi domin ya koma cikin garden din da yake shan iska, akan hanyar shi ya ganta a zaune akan wani dandamali,kanta a sunkuye,wajenta ya qarasa ya tsaya a kanta,bata ji alamun zuwan shi wajen ba sai muryar shi da taji
"Kina nan ashe? Zaman me kike yi a cikin daren nan?" Dago kanta tayi,ganin shine yasa ta tashi tsaye da sauri tare da zuwa gabanshi ta rusuna tace
"Cheo-na" (your majesty) sannan ta dago idonta ta kalleshi,a tsanake ya fara binta da kallo tun daga sama har qasa,yanayinta ya karanta,yace mata
"Me yake damunki?" Girgiza kai tayi
"Babu komai your majesty" tafiya ya farayi tabi bayanshi har sai da suka jera suka qarasa cikin garden din,da yake tsakar dare ne sosai,gari yayi shiru tsayawa yayi tare da kallonta yace mata
"Ina cikin damuwa saboda halin da mahaifiyata take ciki,amma kema kinyi min shiru kinqi cewa komai,kuma na fito ne domin ina son na kasance ni kadai" rusunawa tayi tare da cewa
"Ka gafarce ni uour majesty,ban san oana son kasancewa kai kadai ba,ni zan tafi" ta qarasa tare da juyawa,cikin hanzari yace mata
"Dakata! Babu inda zakije,ganinki yasa na ji dama-dama,kawai dai ban san meyasa yau bakya son yi min magana ba,duk kin zama wani ahiru shiru,amma dai duk da hakan ina jin hankalina yana kwanciya kasancewar ki akusa dani ko da ba zaki ce komai ba" shiru tayi masa bata ce masa komai din ba,tafiya ya fara yi har zuwa inda kujeru suke,suka zauna,cikin sanyin murya,muryarshi na rawa,idonshi ya cika da qwalla ya fara magana
"Ina jin kamar duk laifi na ne halin da mahaifiyata taje ciki! Ana washegari zata fadi ta shiga wannan halin muka samu sa-in-sa da ita,na fada mata maganganu marasa dadi,abin yana damuna,kada ya kasance sune maganganun na qarshe da taji daga gareni,kada ta tafi da baqin ciki na,na kasa jurewa,na kasa,laifi nane,ni na janyo mata halin da ta shiga" ya qarasa maganar cikin karaya sosai,haqiqa duk abinda yake ji aransa ba qarami bane,cikin sanyin murya tace masa
"Ka daina fadan haka,ba laifin ka bane,maganar da na fadawa mahaifina ta qarshe itace NA TSANE SHI saboda ya hana ni abinda nake buqata a wannan lokacin,cikin rashin sanin ashe kareni yakeyi daga fadawa halaka,maganganun da ya ji daga gareni na qarshe kenan ana i gobe zai rasu,amma duk da haka,yasa min kaya masu kyau a cikin jaka,ya raine ni cikin sangarcewa,duk abinda nake so shi ake yi min,ya nuna min tsananin qauna da kulawa,kuma na tabbata bai riqe maganar da na fada masa ba har ya tasu da wannan baqin cikin,domin iyayenmu a koda yaushe masu jin qai ne a garemu,na tabbata mahaifiyar ka ma zata aikata irin haka!" Ta qarasa hawaye yana zubowa a fuskarta,ba tare da ya kalle ta ba yace
"Hakane,na tabbata itama zatayi irin yadda mahifinki yayi domin ita uwa ce! Mahaifiya ta ce! Amma ina mamakin yadda jikinta ya ta'azzara cikin lokaci qanqani,duk da haka ina jin kamar nine silar kasancewarta hakan" da sauri tace masa
"Ka daina fadar haka,ba kaine sila ba,ba kai bane!" Ta qarasa cikin amon murya mai dan qarfi,tare da fashewa da kuka,sai da ta gama kukanta tsaf yayi mata sallama ya tafi ya barta a zaune a nan,tunda ya taci take tunanin kalamansa,gashi bata da damar da zata fada masa ainihin abinda ya faru domin bata da ishashshiyar hujja,gashi yasa abin abin a ranshi ya dameshi matuqa,me ya kamata tayi?"

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now