Page 39

72 5 0
                                    

Page 39

A matuqar gigice likitocin suke suma,dubata suka fara yi,queen haneefah tana gefe tana ta rushin kuka,ajiyar zuciya likitan ya sauke tare da juyawa saitin da queen haneefah take
"Your majesty,bata cika ba! Tana numfashi" da sauri ta qaraso gaban queen dowager ta tsugunna tana share hawayenta
"Omma-maama!" Ta fada tana shafa gaban gashin queen dowager,daidai lokacin mai martaba ya shigo,bai kalli inda take ba,ita kuma ganin shi yasa ta matsa ta bashi waje,ganin bai kula da shirgin ta a wajen ba kawai ta fita,idan ya tafi ta dawo.

IG ne ya fara qoqarin bincike ko za'a samu wani dan uwan sakataren banki,don zai iya kasancewa wani dan uwa ko wani aboki ya bawa ajiyar chek din da suke nema,amma abin yaci tura,duk inda ya tambaya sai ace masa bashi da wani dan uwa a raye,kuma shi kadai yake rayuwar sa,saboda haka ba'a sanshi da wani aboki ba,cikin sanyin gwiwa suka dawo office bayan sun gama zagaye sun gaji,shukra suka samu tana jiran dawowar su,IG ne ya zauna yayi mata bayanin yadda ake ciki,assistant lieutenant da suka shigo tare da IG ne ya kalli shukra
"Yanzu shikenan idan bamu samu chek dinnan ba,babu abinda zamu iya yi,tunda gashi nan ministoci sun fara ingiza mai martaba akan a cire queen daga sarautar ta" cikin firgici shukra ta kalle shi
"Me ?? A cire ta kuma?" Jinjina kai IG yayi
"Tabbas idan har daya daga cikin ma'aikatan ta da suke hannun tribunal suka bude baki suka fadi zancen qarya saboda tsananin azaba,toh tabbas babu abinda zamu iya yi akai,tunda dama binciken ba'a hannun mu yake ba,muna yi ne ba tare da sahalewar hukuma ba,don karan kanmu mukeyi" girgiza kai shukra tayi tace
"A'ah akwai wata hanyar,akwai wanda zai iya dakatar da tribunal din,zan sameshi domin mu samu qarin lokaci" bata jira me zasu ce ba ta fice da gudu.

Masifa yakeyi kamar zai ari baki,cikin uniform din shi a office yakewa wani dan sanda masifa
"Kace bakuga gawar sakataren ba? Toh lallai ku nemo min shi! Ko a raye ko a mace,ku kawo min shi,shashashai kawai" shi dai haquri kawai yake bashi,wani dan sandan ne ya shigo tare da rusunawa yace
"Yallabai wata yarinya tazo nemanka,tace ace maka Shukra Anas ce" zaro ido yayi cike da mamaki yace
"Kace Shukra anas??" Gyada kai dan aiken yayi,juyar da kai jaleel yayi
"Da kanta ta kawo kanta nan? Ko me take nema kuma?" Qara juyowa yayi ya kalli dan aiken
"Ce mata ta shigo"
"Yea" ya fada tare da fita daga office din,yana fita shukra ta shigo,a nutse ta rusunar da kai ta gaishe shi sannan ta dago kanta ta kalleshi ido cikin ido,a zuciyar shi ya jinjina qarfin hali irin na yarinyar nan,shima kallonta yake yi,cikin qarfin gwiwa ta ja kujera ta zauna ba tare da ya mata izini ba,ganin haka shima ya zauna a tashi kujerar,shi ne ya gaji da rainin hankalinta yace mata
"Naji dadin zuwanki nan wajen! Dama na san ke hatsabibiyar yarinya ce mara tsoro,shiyasa na cewa her highness ta kawar dake! Yanzu me kika zo ki fada min?" Har yanzu idonta kar a cikin nashi,babu alamun tsoro a cikinsu,dan karkatar da kai tayi
"Jiya da daddare!" Ta fada,yana ta jiran me zata ce,sai da ta qara jan fasali sannan ta cigaba da magana
"Na san cewar kaine kasa a kashe ni!" Daga kanshi yayi sama yana kallon ceiling tare da yin murmushi
"Au! Kice zuwa kikayi kiyi min barazana,kai!!! Amma fa na cika da tsoro a cikin raina" ya qarashe da dariyar wulaqanci,bata ce masa komai ba ya cigaba da magana
"Toh ace ma dai ni dinne na sa a kashe ki! Shin kina da hujja akan hakan? Ko dai zaki je ki fadawa mai martaba ne? Duk da kina da alfarma a wajenshi amma duk da haka ba zai amince dake akan abinda baki da hujja ba,Ni nan babban yaya ne ga ROYAL NOBLE CONSORT idan har kikayi irin wannan qorafin a kaina,toh za'a yi miki hukuncin qage da sharri ga her highness consort jaleela" ya qarasa maganarshi yana mata hararar gefen ido,ajiyar zuciya ta sauke tunda taga alamun ya gama soki burutsun nasa
"Hakan ma ba zai faru ba! Domin kamar yadda kace bani da hujja,hakane bani da ita,amma fa ka sani cewar dayan laifin da ka aikata jiya da daddare, shi kam ina da cikakkiyar hujjar sa" kallon rashin fahimta ya bita dashi,ganin haka ta fara yi masa bayani
"Sakataren da ka sa ya rubuta maka chek din kudi,mutumin da kayi yunqurin kashewa jiya,kana nemanshi ko ba haka ba? Toh yana wajena!" Wani irin zabura yayi daga inda yake zaune,cikin tsoron da ya fara kama shi yace mata
"Me kika ce?"
"Nace maka yana wajena!" Qara zaburowa yayi,yanzu kam ya firgita sosai
"Ke kin isa ki ce zaki tsorata ni da qarairayin ki?" Gyara zama tayi tunda taga tarkon ta ya fara kama shi
"Ai na san kana nan kana ta neman gawar sa! Amma sai dai kash!! Ba zaka ganta ba domin yana raye" ji yayi kamar kujerar ba zata iya daukar shi ba,rirriqe hannayen kujerar yayi da qarfi,duk shukra tana kula da duk motsin sa,cikin ko in kula ta cigaba da magana
"Ba qarya nake maka ba! Yaji mummunan rauni,amma yaji dama dama bayan likita yayi masa magani,kuma yana jin sauqi,wannan shine dama abinda ya kawo ni wajenka,abinda nazo in fada maka kenan"
Idon shi cike fal da tsoro,sai huci yake yace mata
"Ke qaramar mahaukaciya...ni zaki rainawa hankali? Zan iya kashe ki a nan wajen!"
"Baka isa ka kashe ni ba! Domin duk mutane na sun san nazo wajenka,kuma wajen office dinnan naka a cike yake da jama'a"
Cikin tsawa da bacin rai yace mata
"Ke qaramar mara kunya! Me kika zo ki fada min? Ne ya kawo ki wajena?" Ya qarasa cikin qaraji,ita kuwa ko kadan bata razana ba,a nutse take sauke kalamanta
"Zan dawo maka da shi wajenka! Ni kuma ka tsayar min da tribunal akan binciken da suke yi" nutsuwar sa ce ta dan dawo masa,domin ya dan fara kokonto akan maganarta
"Kina tunanin zan yadda dake ne? Idan har da gaske yana hannun ki ai baki da matsala,zai iya yi miki aikin bayyana gaskiya,me yasa sai da kika zo wajena?" Ajiyar zuciya ta sauke
"Dole ce tasa nazo wajenka,domin ni babu abinda nake so sai gaskiya ta bayyana cewar queen haneefah bata da laifi,amma kafin ya warke sosai wataqila an riga an fitar da takaddar cire ta daga sarautar ta,kuma da zarar takaddar ta fita shikenan babu dawowa baya" jinjina kai yayi
"Sai na ganshi tukunna,domin....."
"A'ah!" Shukra ta dakatar dashi
"Ni lady investigator ce,rashin wayona ba zai kaini in nuna maka inda yake ba,kuma ni bance lallai sai ka yadda ba,in kaga dama ka yadda idan baka ga dama ba kada ka yadda! wannan duk ya rage naka!" Tana gama fada masa haka ta tashi tayi tafiyar ta,tana fita bakin office din ta tsaya tare da dafe qirjinta tana maida numfashi,domin kuwa tsoro ne fal cikinta kawai dai daurewa tayi,tana kuma fatan ya yadda da abinda ta fada masa.
Shi kuwa tana fita jikinsa ya fara rawa kamar mazari tsabar bacin rai da tsoron abinda yarinyar nan zata iya aikatawa,ta shi yayi ya sa ihu kamar mahaukaci ya fara watsi da kayan da suke kan tebur din shi yana ta ihu
"Ta yaya ma zata ce min yana wajenta? Ta yaya akayi ta sameshi?" Tunanin shi ne ya koma kan lokacin da 'yan daban daya tura su kashe masa shi suka dawo suke fada masa sunji mai mummunan rauni,zuwa yanda shukra itama tace masa an jimai mummunan rauni amma da sauqi tunda likita ya duba shi,tunanin hakan ya tabbatar mai da cewar yarinyar nan gaskiya take fada,hakan ya qara tunzura shi sosai.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now