Page 36

77 10 0
                                    

Page 36

Queen haneefah a royal pharmacy bata san me yake faruwa ba,gaba daya masu aikin da suke wajen ne suka zo suka jeru a gabanta,suka rusuna suka gaishe ta,cikin bada unarni take magana da babban royal doctor din da yake wajen
"Daga yanzu Duk tonics din da za'a kaiwa dowager queen sai na fara dubasu na bincika su sosai kafin akai mata" qara rusunawa yayi yace
"Yes your majesty"
Wata cikin maids dinta ce ta taho a guje tana kiran
"Your majesty! Ina da mummunan labari!" Chief maid ce ta tambayeta
"Me yake faruwa?" Cikin haki saboda gudun da tasha ta fara bayani
"Likitan da aka kama ya fadi cewar Her majesty ce ta bashi umarnin zuba baekchul tonic a cikin tonic din Her majesty" tashin hankali ne ya bayyana akan fuskokin su,chief maid ta ce
"Your majesty! Yanzu me ya kamata muyi?" Shiru queen haneefah tayi domin bata taba tsammanin haka ba.

Aliya ce ta miqe zumbur
"Ta yaya ma za'a ce haka ya zama gaskiya?" Rukayya tace
"Hakane mana,gashi munji da kunnen mu abinda likitan ya fada?" Aliya tayi saurin cewa
"A'ah her majesty ba zata taba aikata haka ba" ruqayya ta bata amsa
"Itama consort hui ba zata aikata haka ba,queen haneefah tayi haka ne domin tayi wa consort hui sharri"
Basma da sumayya ne suka shigo,basma tace wa su Aliya
"Ku rufe mana baki,ku daina gulma" sumayya cikin munafurci tace
"Ai ba gulma suke ba,gaskiyane queen haneefah ce ta aikata hakan,tunda likitan ya fadi hakan" basma tayi shiru tana hararar sumayya,Rukayya da taga an basu dana tace
"Yanzu za'a hukunta queen haneefah saboda tayi yunqurin hallaka queen dowager ko?" Sumayya cikin dakewa ta bata amsa
"Ai bama wannan kadai ba,hadda hukuncin qoqarin yiwa consort hui sharri ma" Basma ce ta katse zancen nasu
"Ku daina fadar haka tunda babu hujja" sumayya ta harare ta
"Ba aikin da Nadeeya,Afrah da shukra suke yi kenan ba,a bayan idon mu?" Shiru basma tayi dabakinta domin ta fahimci akwai wani abu a ran sumayya game da wannan batun.

Su nadeeyah da suke wani office daban dukkansu sunyi jugum,shujra tace
"Yanzu muna ji muna gani fa likitan qarya yake yi,don da idona na ganshi tare da nusaiba,bayan ta karbo takadda daga wajen jaleel" nadeeya cikin sanyin murya tace
"Ya za muyi? Bayan ya riga ya fadi hakan,kuma yanzu hukuncin komai ya ta'allaqa ne akan abinda ya fada" ajiyar zuciya shukra ta sauke
"Yanzu yaya zamuyi kenan?" Nadeeyah tace
"Ai yanzu idan har bamu tabbatar wa duniya cewar qarya yakeyi ba,ba queen haneefah ba,har mu ma mun shiga uku!" Shukra ce ta juya ta fita da gudu,har Afrah zata tsayar da ita nadeeyah ta hana ta
"Qyale ta,wannan duk makircin consort hui ne,amma zata fi kowa mamakin hakan,kuma hakan zaifi taba ta fiye da kowa"

Mai martaba yana zaune a grand palace maganganun da sukayi da queen haneefah ne suka dinga dawo masa
"Kin tabbatar consort hui itace tayi umarnin hada abindazai cutar da mahaifiya ta a cikin tonic dinta?" Mai martaba ya tambayi queen haneefah,bayan ta gama yi masa bayanin duk abinda ya faru,cikin sanyin da ya zana yanayinta tace
"Ina jin nadamar fada maka haka your majesty! Amma dukkan hujjoji sun nuna hakan"
"My queen,kin san hatsarin da yake tattare da kalaman ki kuwa?" Rusunawa tayi
"Your majesty! Nima ina jin takaicin da ya kasance sai na sanar da kai hakan,har yanzu ina jin kamar kada na amince da abinda binciken ya nuna,amma dole ne ka gano gaskiyar kuma ka bayyana ta ga kowa"
Bayan ya dawo daga tunanin jijjiga kansa kawai yake yi,domin a halin yanzu bai san me ya kamata yayi ba.

"Your majesty! Na san mai martaba ba zai taba yadda da qaryan likitan nan ba,domin ya san halinki sosai" chief maid take kwantarwa queen haneefah hankali,ba tare da ta dago ido ta kaeta ba ta bata amsa
"Ina ji a jikina cewa na riga da na fada tarkon consort hui"
"Your majesty me yasa kike irin wannan tunanin?" Chief maid ta tambayeta
"Saboda ina jin kamar na fada wani rami mai duhu sosai kuma da zurfi,wanda ba zan iya fitowa ba" ta qarasa cikin tsananin karaya,gaba daya ta qara zama abin tausayi.

Maids din consort jaleela ne suke ta fama da shukra,sai rirriqe ta suke,ita kuma tana neman bige su tana cewa
"Ku barni,ku qyaleni,lallai sai naga her highness" chief maid ce tace mata
"Wai ke wace irin yarinya ce? So kike ki tara mana hayaniya anan wajen? Nace miki ki tafi,kai kuzo ku fita da ita" ta qarasa tana kallon wasu ladies in waiting da suke tsaye a gefe,qarasowa sukai inda sauran suke fa da shukra suma suka sa hannu ana qoqarin janye ta daga wajen,ita kuma tana qi,tana ta cewa
"My lady! My lady! Ki taimaka ki barni na ga her highness" daga bayansu suka jiyo muryarta
"Ku qyaleta" hakan yasa suka saketa suka bar wajen,har gabanta consort jaleela tazo,shukra ta rusuna sannan ta dago ta kalli jaleela
"Your highness akwai abinda nake son sanar dake! Your highness! Na san wannan ba shine ainihin abinda kika shirya ba,na tabbata ba zaki aikata abu irin wannan ba,Don Allah ki tsayar da komai haka! Ki bar komai haka,ba halinki bane,wannan ba shine abinda ya kanata ki dinga yi ba!"
Idonta kar akan shukra,cikin yanayin da ta saba magana cikin izza da dakewa,da kuma boye abinda yake ranta tace mata
"Wannan abin? Shi menene abin da kike ta maimaitawa? Ban san akan me kike magana ba" zaro ido shukra tayi saboda mamakin abinda jaleela tace
"Your highness!" Jaleela ce ta katse ta
"Saboda mun kasance makusanta a baya,zanyi amfani da hakan nayi miki kashedi,kada ki yadda ki qara tsaya min a gabana,ki tsaya min akan hanya ta idan kina son ki tsira da rayuwar ki a cikin rigingimun da zasu faru nan gaba,ina shawartar ki da ki rufe bakin ki,kuma kada ki qara bari na ganki" jikin shukra ne gaba daya yayi sanyi jin kalaman da jaleela take fada mata,cikin sanyin murya da kuma hawayen da suka cika idonta ta bude baki tace
"Your highness!" Tayi maganar kamar cikin sigar tambayar,anya ita take fadar wannan maganganun? Juyawa jaleela tayi ta barta a tsaye a wajen,baki a sake.

ROYAL CONSORTDonde viven las historias. Descúbrelo ahora